[4:09PM, 7/22/2016] Rash Kardam:
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.*
*Pg-233~234.*
Zuwa yayi ya rungumeta ya ce"baby na kinyi kyau sosai", murmushi tayi ya lakaci hancinta ya ce"kullum kyau kike k'arayi ina rok'on Allah banu baby mai kama da ke". Da irin wannan kalaman ya lallab'a Aisha suka lula duniyar masoya. Washe gari Haiydar ya fita zuwa aiki Falmi ta tattari kawayen ta 'Yan bariki suka zo da niyar dukan Aisha kowacce da bulalarta a hannu ana haka sai ga Haiydar ya dawo ganin su yasa ya kira jami'an tsaro aka tattaresu ko wacce taji a jikinta suna kulle a gurin jami'an tsaro, cikin Falmi ya faro ciwo kafin me sai ga jini wanda hakan yasa aka kira Haiydar da gaggawa aka kaita asibiti suna zuwa ana dubata cikin inkon Allah suka zai da jinin suka shaida ma Haiydar cewa magani Hana Haihuwa ta sha wanda yayi wa haifarta illa, nan ran Haiydar ya k'ara b'aci sosai, sai da aka taimaka mata jini ya tsaya, tana farfad'owa ya ce"Fatima naga abu abunki yayi yawa don haka in kin samu sauki ki wuce gidan ku". Ya juya ya fita hawaye ke zuba afiskansa tabbas Haiydar na son Falmi amma ita tana bin zugar kawayen banza shi yasa da kishin hauka dake damunta.
Bayan kwana biyu Haiydar, da Sarkin Fulani dasu Lamid'o da Hajiya suka tafi Yola tabbas Aisha taga ga tanta da dangin ta ko ina sai murnan ta akeyi. Batun gona ko Sarkin Fulani ba k'aramin kud'i ya kashe a gun ba an k'awata gun sosai gwanin burgewa wanda aka sanya masa suna *AISHA VILLA GARDEN* sai da akayi bikin bud'e gurin Lamid'o ya damk'a amanar gurin wa Maharbin nan daga nan kuma aka d'ibi ma'aikata a kauye da birnin Yola, kafin suka dawo lokacin Aisha ta k'ara kyau tayi haske ga wani kwad'ayin da takeyi kulum sai tasha ice cream rigimar yau daban na gobe daban. Yau ma kamar kulum Haiydar ya dawo Aisha ta tasashi gaba da shagwab'a dole sai sunje shan ice cream ba yanda ya iya dole ya fita su tafi, bayan sun saya ice cream dai-dai zasu shiga mota Aisha ta hango wasu mutane take ta rud'e tafara kuka ta mak'ale Haiydar yayi ta tambayan ta duk ta rud'e sai da Haiydar ya sanya bakinsa cikin nata ya bata wani sassayan kisses kafin ta dawo hayyacinta rungeta yayi ya ce"mai ya faru wa ya tab'a ki mai ya tsorata ki". Cikin kuka ta ce"sune sune". Haiydar ya ce"waye su d'in?". Aisha ta ce"sune suka d'aukeni lokacin dana b'ata". Haiydar ya ce"what!!" Gwada min su nan ta nuna masa su suna shiga gun shan ice cream d'in Haiydar yasa ta a mota ya ce"ki zauna anan karki fito", rikesa tayi ta fara kuka dan Allah ka kyalesu kar su cutar da kai". Murmushi yayi ya ce"karki damu kimin addu'a Allah zai kareni". Kai ta gir-giza masa wayansa ya d'aga ya kira 'Yan sanda da suke kusa ya na zuwa ya bada umurni aka rufe gun aiko saiga police nan suka shiga aka kamasu duka, nan yasa aka tafi dasu ya ce"bari ya mayar da matar sa gida". Gidan Hajiya ya kaita ya koma gun aiki. Azaba akayi ta gana wa mutane nan da kyar suka fad'i wacce ta sa su ran Haiydar ya k'ara b'aci da kansa yaje har gidansu Falmi yasa aka kamota sai da ta daku a gunsa sosai kafin ya ce"ki sani na sakeki saki d'aya tunda har haukan ki ya kai kiyi tunanin kisa". Falmi taji wahala har tayi nadama abunda ta aika, ga wahala ga auren ta ya mutu,.***************
Bayan wata takwas Aisha na hango da zungureren ciki tana tafiya tana ciza baki ta dafe cikin ta Haiydar ne ya fito daga d'aki da sauri ya riketa ganin kamar nak'uda ne da gudu yayi d'aki ya d'auko akwatin kayan haihuwar ta ya fitar ya dawo ya sun kuceta sai asibiti cikin ikon Allah bata dad'e tana nak'uda ba ta haifo baby boy d'inta, nan fa Haiydar yayi ta kiran 'Yan uwa yana fad'a musu kasancewan lafiyarta lau ta haihu hutawa tayi aka sallame su kafin kace me gida ya cika da 'Yan uwa da abokan arziki.
Bayan kwana bakwai ranan suna yaro yaci sunan *_ABDUL SHAKUR_* Yaro kyakyawa gwanin burgewa bikin suna yayi kyau ida muka samu kyatuttuk'an zannuwa ne mai hoton yaro da Al-qur'ani mai girma abun sai wanda ya gani haka aka watse.
*®NWA*
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
0 comments:
Post a Comment