New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE... 197-199

[7/12/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-197~199.*

Ta juya idonta ta ce" na manta ban miki godiya da karamcin da kika min, gaskiya kin can-canci in gode miki, kin had'a ni aure da gwarzon Mijiki Haiydar kuma kin iya had'i sosai, don ni kaina na san, nasamu mijin nuna wa sa'a gashi kyakyawa, jarumi a kowanne fage nagode". Hannu Aishat tasaka akan bakinta tare da yin kiss ta hura ma Falmi, ta saki wani murmushin mugunta, don yanda taga Falmi ta dawo, juyawa tayi ta nufi d'akinta tana rangwad'a. Falmi batan lokacin da ta d'aura hannu aka ta fara ihu tana cewa"lalle yau nasan na *TAFKA BABBAN KUSKURE* wato d'an hakin da na raina...... Na raina Indo sai ita ce zata gasa min aya a hannu". Falmi ta fara Safa-da-marwa a falon bakinta ta ciza tare da dunkule hannu, tana tunanin mafita yanzu wani mataki zata d'auka gashi taga Aishat da zafin ta take can komai ta tuna tasaki lallausa murmushi ta nufi dakinta wanka tashiga don tasamo ma kanta matakin da zata d'auka.
Aishat ko tana barin falo da gudu tayi d'akinta key(mabud'i) tasa ma d'akin ta rufe tare da jin gina a jikin k'ofar dakin tana maida numfashi. Wani sassanyan ajiyar zuciya ta saki a fili ta furta" lalle na iya cika baki duk wannan kurarin kamar zan iya dukan Falmi ai ko yau da ta shakeni sai dai wata Aishat bani ba". Jin kamar motsi yasa ta zabura jikinta sai b'ari yake ta ce"wayyo yau na janyo ma kaina tabbas yau inta rikeni nikam sunana gawa". Wani dabara ne ya fad'o mata doguwar kujeran hutuwa dake cikin d'akinta ta janyo zuwa bakin k'ofar ta tokare k'ofar dashi, wai ko da Falmi ta biyo ta bazata iya b'alle k'ofar ba. Sai zufa takeyi ga tsoro da take ji duk a razane take sai zare idanu takeyi tamkar wacce tayi ma sarki lafi.
Haiydar ko d'aki ya koma yana tunanin irin rayuwan da zaiyi da matansa biyu, gashi yanzu ba abunda yake da k'auna da muradi kamar Aishat amma sam bai ganin fuska ajiyar zuciya ya sauke a fili ya furta"Allah ka sanya Aishat sona". Mik'ewa yayi tare da d'aukar key(mabud'i) d'in motarsa ya fita waje don ya samu abunda zai ci.
Falmi ko tana fitowa cikin hanzari tasoma shiri make-up (kwaliya) tayi ta d'auko kaya tasaka tare da d'iban kud'i tana wani murmushin mugunta ta fita.  Wayarta ta d'auka ta kira wata magana sukeyi kasa-kasa wanda nikai na Rash duk son d'ibo rahoto na bansamu damar naji mai take ce wa ba, dole na hak'ura injira ta gama na bita naga mai take shiri aikatawa.
Haiydar yana fita gurin cin abinci yanufa ya sayo guda uku, gida ya dawo ko da yazo falo yaga ba kowa, d'akin Falmi ya nufa yaga batanan da alamar ta fita ledar da yaso nata ya ajiye mata. Ya nufi b'an garen Aishat ko da ya tura k'ofar yaji a kulle sai ya kwan-kwasa k'ofar.
Aishat da take ciki jin an kwan-kwasa k'ofa take cikinta ya bada sautin kululuuu! Wani fitsari ne ya taho mata bashiri ta sa hannu tana matse k'asan k'afarta duk a tunaninta Falmi ne, bata san lokacin da yanka bayi da mugun gudu ta kulle bayi sai ga fisari na gan-garowa ta k'asan k'afarta.

Niko Rash mai zanyi in banda dariya nace"haba Indo karki bada ni mana duk kurarinki nan ace kina wannan tsoro haka?".

Masu karatu kuyi hak'uri da d'an wannan yau banda charged ne sai gobe zakujini in sun bar wuta.
Luv u all my fanz����.

                  *®NWA*

  
                  *DEDICATED TO*
           *AISHAT MUHAMMAD*
      *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                   *RASH KARDAM��*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts