New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE... 177-179

[7/7/2016]Rash Kardam
����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-177~179.

Rayuwan Indo haka yaci gaba da tafiya, tana zuwa makaranta.
Sun had'a kai da su Sanah da Sadeey, da zamansu ta ga na da kyau, bata b'oye musu komai na rayuwanta ba, ta fad'amusu. Sanah tace" mukuma zamu bada tamu gudumawar gurin ganin kin gyaru.
Sadeey ita ta dage gun koya mata k'waliayar zamani, Sanah kuma gyaran jiki, hatta yanda Indo zatayi tafiya saida suka koya mata.
Bayan kwana biyu suka zo mata da form d'in makarantar kwaliya ta cika, da kanta ta biya kud'in kasancewar tana samu 'yan kud'i, a haka ta fara zuwa.
Hajiya ganin jarabawan Indo yayi kyau hakan yasaka ta bata motarta, ranar da Falmi tasamu labari kamar zatayi hauka a gidan, don saida Hajiya ta tsayar mata ita da Aliyu, don motar Falmi bai kai na Indo ba.
Sanah suna hira da Sadeey da Indo, Sadeey tace"Indo gaskiya ni bana son ana kiranki, da Indo nan sai kace yar kauye.
Sanah tace"kamar kina raina.
"Shawara daga yau duk wanda yace miki Indo, in ba wanda kike jin kunyarsa bane karki amsa.
Tun daga ranar sunan Indo ya b'ata yakoma Aisha, nima Rash nace" daga yau na daina cewa Indo sai Aishat.*********
2yrs later
Wata k'yak'yawan budurwa na hango, tana fitowa da ga cikin gida ta na k'ok'arin bud'e motar ta, mai k'irar RANGE ROVER, sanye take cikin wani doguwar riga ya d'an kamata daga sama, sai d'an k'aramin cikinta dake a shafe ya fito. Hakan shi zai baka daman gane irin halittan da ubangiji ya mata, harta shiga mota ko mai ta tuna cikin damuwa tace"oh shirt! Da sauri ta fito ta nufi hanyan cikin gidan, gudu-gudu sauri sauri, sam bata ankara da wanda ke fitowa ba, sai jin garam sunyi karo da mutum. Ko ta nuna alamar damuw ta d'ago kai tare da d'an zaro gilashin  dake idota, sai da ta d'an rausaya ido, ta wani kashe murya tace"oh  i'm sorry! you guy.
Bata jira amsan shi ba ta sakai ta wuce abunta, Haiydar da tsananin mamaki kasa motsi yayi, shafa ida ta buge sa yayi, haryanzu dadda d'an k'amshin ta yana tashi. Wani yawu ya had'iye da ya tuna yanda take sarrafa mazaunanta, da k'irjinta.
Tabbas Allah yayi halita a gun, cikin zuciayrsa ko cewa yake"wannan taci a kirata da zallaziya ko zank'aziya hmm wannan tamk'ar ita tayi kanta.
"Gaskiya ta had'u ba k'arya.
"Gashi ta had'a duk wani abunda nake so ajikin mace amma taya zan tink'areta?.
"Hmm ni shakkanta na ke ji ma yanzu.
Wata zuciya tace"to ko kana jin shakkanta sai ka tin k'areta, ai girmanka zai zube.
Yana tsaye tazo ta wuce sa, motarta tashiga sai da ta yi ribas, kafinta ta da kura ta bule Haiydar ta wuce da gudu.
Haiydar ko gizau baiyi ba ila bin motarta da kallo.
Zuciayrsa tana masa wani irin abubuwa nai wuyan fasaruwa, kasa motsi yayi don duk jikinsa ba k'wari.

Masu karatu wai shin wata yarinyace wanna, da har zata iya taka Haiydar, ta masa wannan wargin batare da ya d'au mataki ba?.
Don son jin wannan amsar ku biyo ni.

                *DEDICATED TO*
          *AISHA MUHAMMAD*
   *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                *RASH LUV��*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts