BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.*
*Pg-227~228.*
Na tattara dukkan shanuna da 'yar sanda na muka d'au hanya sai da mukanshiga cikin daji kawai mutanen nan suka b'ullo mana ba k'aramin razana mukayi ba amma duk da haka nayi iya k'ok'arina akan su amma Allah baiyi ina da nasara ba haka suka kwad'a min sanda a kafad'a ganin bazan iya kare kaina ba shine na wurgo ma Safinatu jakata da kud'i a ciki da awarwaron da Hajiya ta ban sannan da hoton mu da ku da nawa ni da ita wanda mukayi a auren mu". Ya nisa tare da gyara zama ya d'an kurb'i ruwan Faron da ke gefensa ya ce"kunji yanda muka rabu da Safinatu". Duk fiskan su d'auke da hawayen tausayi Sarkin Fulani ya share kwala ya ce"muna jinka yanda ku ka k'are da mutanen". Lamid'o ya ci gaba da ce wa"bayan tafiyar Safinatu tana kuka tana waige na haka mutanen nan suka kwada min sanda na suma a gun, sukuma suka kad'a shanuna suka tafi, ana haka sai ga wani Maharbi ya zo ganin halin da nake ciki ya d'aukeni yaje ya ta min magani, da ikon Allah ciwukan dana ji duk sun warke amma me sai na samu tab'in hankali haka Maharbin nan yayi ta jinyana tsawan shekara goma sha bakwai kafin da ikon Allah ya samomin magani shekara guda da rabi yayi yana min jinya da maganin cikin ikon Allah na samu lafiya, daga nan ya tambayeni labari na na basa labarina tun daga kawo ni da akayi Yola har zuwa lokacin. Maharbin nan shi ya tara 'Yan uwansa da mai gari aka karb'a min shanuna ko da suka dawo hannuna sai na saida guda uku a cikin garin yola na dawo kauyen fofure na sai babban fili a jeji wanda filin ba k'arami bane(kunsan filin kauye ba zada sosai). Nan na sake biyan kud'i aka kewaye min da wayoyi nazuba shanuna aciki sannan nasaka su kaji da raguna da akuyoyi da talotalo da agwagi ruwa, bayan dana gama aikin sai na damk'a wa Maharbin nan gonan a hannusa zai na kula dasu don ana saran koyayen zabbi da sayan madaran shanu a gun na masa sallama na sanar da shi zanzo Mahaifata na ga iyayena da Matata da na turota tare da cikin da ke jikinta nan na kamo hanya zuwa Gombe, to kunji labarina". Wannan karon harda Haiydar a 'Yan yin kwalla labarin gwanin ban tausayi. Sarkin Fulani cikin fushi ya ce"yanzu abinda Hajiya k'arama zata min kena batare da b'ata lokaci ba ya kira police ya ce su zo gidan sa yanzu-yanzu".
Hajiya k'arama da ta lab'e tana jin duk abunda ya faru cikin sauri ta koma d'akin ta tafara shirya kayanta a k'aramin jaka sai ta nufi d'akin Sarkin Fulani ta d'ibi kud'i da dollars cikin jaka, nan ta fara dariyan mugunta tasan wa'yan na kud'in sun isheta rayuwa a ko ina take ga kuma wanda ta tarasu a account d'inta K'ofar baya tabi tayanda sarki bazai ga fitarta ba cikin hanzari take tafiya dan kar a ganta.
A falo kuwa police sunzo d'akinta aka nufa kai tsaye amma me sai wayam suka gani ba kowa nan suka bazama aiko suna zuwa k'ofar baya suka ga ta k'ofar a bud'e cikin hanzari suka bazama bakin titi suka hango ta tana shirin shiga napep ganin haka wasu suka tsari mashin aka bita wasu a mota
[10:29PM, basuyi nisa ba aka kamata aka sa mata ankwaf aka nufi C.I.D da ita ana kamata aka sanar ma Sarkin Fulani nan ya ce"Lamid'o muje C I D tare suka fita a jikin mota ko da suka je nan ma aka basa duk abunda aka kama a hannuta, ransa ya k'ara b'aci sai da yabata kyawawan mari masu lafiya ya kuma ce" wallahi kin cucen na yarda da ke sakayyar da ki ka min ke nan ki sani ba amfanin zamana da ke na datse igiyar aurena uku da ke kanki". Nan ya ba da umurnin abata wahala sosai tukun a turata kutu.
Haiydar ko Hajiya na mik'ewa ya nufo gun Aishat Hasna na ganin haka ta ja 'yan matan k'afar ta ta bar falon, Aisha cikin hanzari itama ta mik'e har ta fita a falon taku k'alilan yayi ya fisgota sai a k'irjinshi ta fad'o nan wani kamshi mai tattare da sanyi ya daki hancinta Haiydar cikin kwayan idonta ya fara kallo ganin haka ta lumshe ido dul jikinta b'ari yakeyi, hancinsa ya d'aura akan nata ya fara gogawa tare da sanya bakinsa cikin nata nan yaji wani laushi a labb'an ta, tun da yake da Aishat sai yau yasamu wannan damar Aisha ko k'ok'arin ta gudu take amma me hannuta ya manna da garu tare da d'aura hannusa akan nata yasona kiss d'inta kamar wani mayunwaci, duk yanda taso ta kauce ba hali gashi jikin ta na b'ari sosai hawaye ke zuba harshensa yasaka yana lasar hawayen sai da ya lashe tass, Aisha gashi ba halin tayi magana ya had'a bakinsa danata dai da ya jagwa-gwata son ransa ya saketa da gudu tayi hanyan cikin d'akinsu sai hakki takeyi cikin sa'a ba Hasna a d'akin kan gado ta fad'a tana maida numfashi sama-sama tare da lumshe ido cikin zuciyarta ko cewa take" a sai haka kiss d'innan ke da...
*®NWA*
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
0 comments:
Post a Comment