BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-136~140.
Cikin hanzari ya kaimata cafka, yayi sa'an riketa, Falmi tayi ta kwace takasa, kuka tasoma masa duk ya rikice, sakowa yayi ya mata nil down ya riko hannuta yace"haba Falmi na mai na miki kike hukuntani ta wannan hanyan?.
"Shin kaki tsoron kamun Allah Falmi?.
"Kisani ko dai-dai da seconds daya kika tutarni a wannan harka Allah zai saka min.
"Kulum cikin azarbtar dani kikeyi Falmi.
"Ko so kike in fara bin matan banza.
Wani kalon ko oho ta aika masa cikin muryan kuka tace"Aliyu in ka ga dama ka kama d'aki a bayan gari ba ruwana.
"Kasani da *KISHIYAR GIDA GWARA TA WAJE* na tsani in gani da wata matsayin matarka.
cikin kuka tace" ni daka auro min Indo gwara ka ringa bin mata a wa....
Bata k'arasa ba taji saukar lafiyayen mari a fuskanta, cikin huci yace"Falmi asai baki da hankali?.
"Asai bakisan mai kikeyi ba?.
"Tabbas na yarda bakisan ciwon kanki ba.
"Kinga ina lallab'aki ko don kibani hakkina.
"To wallahi ta karfi zan ringa karb'a yanzu, banza kawai.
Falmi ba k'aramin tsorata tayi da yanayin Haiydar ba, qofar d'akin yaje ya zate key d'in ta sanya a saman Waldrop d'insa, ya suma bin Falmi tana hawaye suka soma kokawa da kyar Haiydar ya samu ya wurgata kan gado, Falmi ta fara ihu, kamar k'araman yarinya, cikin b'acin rai yace"keee baki da hankali ko?
"Yau ko a gaban wakike sai na karb'i hakkina, Haiydar da iya karfin sa ya zage yake abunda yakeso. Niko Rash ina ganin haka na tattaro yan matan kafata na fito.
Su Indo sun gama shiryawa shiru ba labarin ango, har an kai wasu a mare cikin *LAREMA HOTEL* anan za'ayi dinner, ya rage daga cutie sai Hasna da pinky suma yanzu saurayin Pinky Nura yazo d'aukarta, sai Hasna da Cutie Sadiq zai tafi dasu. Ana haka saiga Haugal ta iso ita da Ghalinta,(masu karatu ina fatan baku manta da Haughal ba ko?. Nacikin litafin *BAZATA*). Ghali yaje gunsu Sadiq yace"wai ina Man d'in ya shiga ne?.
"Tun zamu taho nake ta kiran wayansa bai d'aga ba. Sadiq yace"wallahi muma hakane amma bari zamuje gidansa muduba shi, daga nan sai mu wuce.
Jiddah da sallama ta shiga gidan, da su Hasna ta gamu da su, cikin girmamawa Hasna tace"lah! Aunty Jiddah kin isone?
"Jiddah tace"eh yanzu muka zo.
"Hasna tace"ina Uncle Ghalin"yana waje yanzu zanje muwuce kenan.
Jiddah tazo kusa da Indo tace"amaryan mu kinsha kyau bari mu fara gaba sai kun iso.
Indo murmushi ta iya mata don tana gabda yin hawaye, sabida tasan daman Haiydar ya tsaneta wahala zatasha ba kad'anba. Haughal ta fita zuwa gun Ghali don su wuce gun dinner. Sadiq yace"Ghali bari muje gidansa kawai mu duba sai muga ko lafiya ne. Ghali yace"ok hakan za'ayi.
Sadiq ya kira Hasna yace"ku fito da amaryan kawai mu wuce.
Da kyar Indo ta fito don hawaye take amma sai kalura ka gane hakan, suka sakata a motar da za'a kaita Cutie a da Hasna motar Sadiq Hasna ce a gaba sai cutie a baya. Pinky kuma Ya Nuranta.
DEDICATED TO
AISHA MUHAMMAD
(MAMAN ABDUL SHAKUR)
RASH KARDAM
[6/3/2016] Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-141~145.
Suka d'au hanyan gidan sa, Indo ko in banda hawayen takaici babu abunda takeyi, tana rokon Allah ya kawo mata d'auki a rayuwanta.
Haiydar ko bai kyale Falmi sai da ya tabbatar ya gamsu sosai, ya mike ya shiga wanka. Bayan ya fito yayi Sallah isha'i kenan ya d'auko wayarsa, mai zai gani 60miss call na Hajiya 20 na Sadiq 46, sai na Ghali da wasu abokansa, sam ya manta da zasuje dinner sai a lokacin ya tuna, cikin hanzari yasa d'anyar boyal d'insa mai ji da shek'i, ya kawo agogon hannu ya d'aura ya sanya takalminsa, ya d'auko hularsa itama fara yazo gaban miro ya na d'aurawa, Falmi dake kwace jiki ba k'arfi ta mike cikin zuciyarta ko cewa take"nayi ma kaina gashi ban hanasa zuwa dinner ba, gashi ya gurjeni son ransa amma dole na b'ata kwaliyan nan kuma bazaije ba.
Tana d'ingisawa tazo ta tare qofan fita Haiydar ya gama shiryawa yazo zai wuce tace"baka isa ba yau kaje dinner auren wata marar asali.
"Yar titi kuma tsintaciyar mage bazai yuwu ba.
Haiydar yace"kiyi hak'uri ana jira na kuma kinga mutane sunzo doni ne.
"Ni badan Yar aiki zanije ba.
"Sabida mutanen da suka taru domin ni zanje in fita kunya.
"Falmi kinsan ina matuk'ar qaunanki.
Falmi tace"k'arya ne *MAYAUDARI* maha inci kawai.
"Da kana sona bazaka yarda ka auri Indo Yar aiki na ba.
"Haydar yau ko ni ko kai don ba inda zakaje maci *AMANA* kawai.
"Ka kasa rike *AMANA TA* da iyayena suka baka.
Ganin zata b'ata mishi lokakaci ya d'auko key zai bud'e qofa tazo ta rike hannu qofar. Ganin bata da nutsuwa a tare da ita, kuma ya mata magana duk taki fahimta. Wata zuciya tace"bata k'yak'yawan mari zata fi fahimtan wannan yaren.
Sai da ya gyara hannusa ya bata lafiyayen mari, take Falmi takoma gefe don sai dataga wasu Stars suna mata shining. Haiydar ya bud'e qofa har yafito harabar gidan yana shirin sanya k'afarsa waje kenan, Sai ga su Sadiq nan suka fara tambayamsa lafiya?.
Sadiq ya fara masa surutu Haiydar yace"mutafi lokaci ya kure.
Yazo sai shiga mota kenan, Falmi ta fito da gudu ta rik'e murfin motan tana cewa"yau ba inda zakuje indai inanan.
"Alo tsiya alo danja ba mai fita da kai.
Cikin takaici ya tureta ya rufe motar.
Falmi batayi k'asa a gwiwa ba ta je ta tatare gaban motar tabaje tana cewa"yau sai dai in ta kaina zakubi ku fita ehe.
"Sai ku kasheni in huta.
Haiydar bai ma lura da Indo da take gefe tana hawaye ba. Takaici duk ya ishesa da kunya, gashi a gaban abokansa.
Sadiq ya mata Horn amma taki matsawa sai ihun da take kurma musu kamar masu satan mutane. Cikin zafin rai Haiydar ya bud'e qofar mota.
Ga d'an wannan ina samu lokaci zakujini da daddare in nasamu lokaci, in bansamu ba kuwa sai bayan *SALLAH* In Allah ya kaimu da rai da lafiya.
DEDICATED TO
AISHA MUHAMMAD
(MAMAN ABDUL SHAKUR).
RASH KARDAM
0 comments:
Post a Comment