New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE... 210-213

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-210~213.*

Fad'uwa Haiydar yayi a kan gwiwarsa kamar mai (nil down) yana k'araji yana ihu ga hijab d'in Aishat a hannusa ya na kuka wi-wi kamar yaro. Da gudu ya tashi yayi gabar yana kiran Aishat! Da gudu ya dawo yayi yamma yana kiran Aishat!! Ya sake dawowa yayi Arewa yana kiran Aishat!!! Yazo ya sake yin kudu yana kiran sunanta, ya dawo kaman zarare. Ya dad'e a haka ya kasa tab'uka komai sai kuka tamkar mace kamar ba jarumin d'an sanda ba mai hazak'a da kwazo wayarsa ne tayi k'ara yana kuka ya ciro daga aljihunsa ya ga sunan Hajiya kafin ya d'auka harta tsinke.
B'an garen Hajiya ko ta ce"yau lafiya banga Aliyu ya d'au wayata ba?".  Kamar ta ajiye wayan sai wani zuciya ya ce"kawai ki sake kira kiji lafiyarsa dana d'iyarki". Cikin hanzari ta danna kira. Haiydar jin waya na ringing ga jikinsa sai b'ari yakeyi (daman wannan yanayinsa ne in ransa ya b'aci jikinsa b'ari zainayi). Da kyar ya iya danna gun amsa kira yasa a kunnensa kuka yakeyi yana kiran Aishat! Ciki razana Hajiya ta ce"Aliyu lafiya mai yasamu Aishat?". Bai iya amsa mata tambaya ba sai ce mata" Hanyan gida b'ata Aishat". Sam kwakwalwarsa ta kasa tuno masa ma ya zai had'a kalman a dai-dai ya fad'a Hajiya cikin kid'ima tun da taji yananyi Haiydar tasan abun ba k'arami bane, ta d'auko hijab d'inta ko Abban su Haiydar dake hanyan dawowa yau bata sanar masa ba ta fito a gi-gice, bata tsaya kiran driver ba(mai tuk'a mota) kasancewar daman ta iya mota da sauri ta figi mota tun daga nesa take horn ma mai gadi, shi kansa mai gadi sai da ya rud'e da horn d'in da takeyi ai ya na wangale gate(gareji) da mugun gudu ta fita. Gudu take shararawa cikin min tunan da baifi hud'u ba ta soma hango Haiydar ga kuma motar Aishat! Gudu ta k'ara tana isowa ta gansa a durk'ushe a kan gwiwansa zuwa tayi da sauri ta rugumesa tana jijiga sa ta ce"Aliyu lafiya? Ina Aishat d'in?".  Jinsa a jikin Hajiya ya saki sassayan ajiyar zuciya sai a lokacin nutsuwa ta zomasa, cikin kuka ya sanar da Hajiya abinda ya tarar Hajiya ta ce"innalilahi wa inna ilaihi raji'u ai ba zama zakayi kana kuka ba, kaman ba jarumin police ba?" Abunda ya da ce zamuyi yanzu tashi kabi sawun motar sannan ka kira duk wata ma'aikatar police da ke kusa a sane dasu don a baza matakan tsaro. Haiydar ya shiga motarsa zuciyansa na suya gun aikinsu ya kira yasanar musu ya ce"susanar da sauran ma'aikatar hukumar 'Yan Sanda a bazama wasu su biyo sa, hayar da mota tayi yafara bi har ya fitar dashi bakim ti-ti, daga nan kuma hanya ta kasu kashi uku ya tsaya yana tunani sai ga wasu motocin police('Yan sanda) sun iso mota uku nan suka kasu kashi uku d'aya yabi Haiydar biyu suka bi sauran hanyoyin. Abu wasa-wasa suna neman Aishat ba labarinta  gashi har anyi sallah isha'i.
Aishat tare da 'Yan iska tafiya sukeyi sai shiga cikin daji sukeyi yayinda jinin jikinta sai zuba yakeyi kasancewar ta mai yawan cin abinci mai kyau tanada wadattace jini amma sanadin zuban da yayi da yawa ya haddasa mata jin jiri, idanunta suna wani iri, hakan baisa Ogan 'Yan iskan nan yayi niyan saurara mata ba sai aika mata da mayen kalo yakeyi.
Su Haiydar ko sunyi nima harsun gaji amma shi baijin gajiya a tare da shi zuciyarsa suya yake masa yama rasa wani irin kalan hukunci zai yanke ma wanda ya d'au Aishat d'insa tabbas ba zai iya saurara masa ba baran yanda yanzu yake jin tsananin k'aunar Aishat na yawo a jinin jikinsa da jijiyoyinsa tafiya suke ga dare yayi ko da ya kali agogon da ke hannusa 11:49 wani kwana ya gani wanda ya lula cikin deji kuma hanyar k'aramace mota bazata sake acikin hanyan ba wasu suna cewa kar abi hanyan halane ko sunbi ta gun gashi yayi daji ko  da Haiydar batunsu ransa da ya b'aci ya finciki motar ya shiga cikin dajin, sauran suna ganin ya shiga suka bisa a baya sai yayi tafiya sosai sai yaga wani abu a gefe kamar mutum ne ko tudu, da sauri ya tsaya ya fito da wani touch light d'insu mai haske yana haskawa ya hango Aishat kwance bata motsi da gudu yayi gunta yana haskawa yaga jini na fitowa daga k'asan skirt d'in makarantarta wani razazane k'ara ya saki ya soma jijigata ganin bata motsaba, dai-dai lokacin sauran police d'in suka iso, bai bi ta kansu ba da gudu yayi mota da ita ya sanya ta a mota ya juyo ya ce"ku tabbatar da kunbi mutanenan kuma kun kamosu zan turo wasu motocin su biku". Bai jira amsansu ba ya juya ya shiga mota ya figeta da gudu ya nufi cikin gari.

               *®NWA*

                *DEDICATED TO*
         *AISHAT MUHAMMAD*
     *(MAMA ABDUL SHAKUR)*

              *RASH KARDAM��*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts