[7/6/2016 Rash Kardam]
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-170~173.
Ko da suka dawo gida, Hajiya ta zaunar da Indo tayi mata nasiha, game da aurenta, sanan ta k'ara da cewa"Aisha kiyi hak'uri ina sane, da duk irin abunda Aliyu yake miki.
"Abunda yasa ba zan takurasa ba a kwai lokacin dana ke jira, zan ramamiki duk abunda ya ke miki, inaso ki nutsu kiyi karatu nan gaba sai Haiydar yazo da kansa yana baki hakuri.
"Alokacin ne zamu rama duk abunda ke mana, Hajiya wani murmushin mugunta tayi, kafin taci gaba da cewa"zan saki a makaranta islamiya, don ki rage yawan zaman gida.
"Sannan ki k'ara hak'uri da duk abunda zasu miki, wataran zakici riban hak'urin ki, har sai ni da kaina nazo, ina cewa Aisha ki d'an ji tausayin Yayanki, ki sassauta ma Haiydar. Hasna ne tayi murmushi don itama tanason ta ga wannan ranan.
Hajiya tace" a kwai motar da Abban na, Sarkin Fulani(Gakansu Haiydar ) ya ban range rover zan baki ita, tadawo naki halal malak.
"Zansa Hasna ta koya miki mota amma sai naga kunyi jarabawa, da irin sakamakon da kika fito da shi kafin na damk'a miki motarki a hannuki.
"Sai gobe zaki fara zuwa school, in kin dawo da kaina zan maidaki gida, kuma zansa driver yana kaiki makaranta.
"Ku tashi kuje ku huta Allah ya muku Albarka.
Suka amsa da"ameen.
Gidan Haiydar ko yau ya dawo da niyar ko ta kwana, don yau yayi niyar karb'a hakkinsa a gun Falmi.
Don yayi hak'uri har ya gaji, rabonsa da ya kusanceta har ya manta.
Wanka yayi ya nufi d'akinta, yana zuwa ya tarar ta baje a gado, tana sharan baccin ta.
Hawa gadon yayi, yazo kusa da ita ya kwanta.
Salon sa da yake rikitar da mace, ya fara aika mata sak'onsa.
Cikin bacci Falmi taji ana shafata, farat ta farka ganin Haiydar yasa ta rik'e hannusa, tace"mai kake shirin yine?.
"Ko ka manta dokata ne?.
"Matsawan kana son biyan buk'atarka sai ka ajiye min kud'i.
Cikin da shashiyar murya Haiydar yace"haba Falmi anya kina tsoron Allah kuwa?.
"Matar aure na na sunnah, don zan kusanceki sai na biya kud'i.
"Kisani fa hakan haramun ne.
"Kisani mala'iku su tsine miki fa?.
Falmi tace"ai yau in har kaga ka samu abunda kakeso to kasaka min kud'i har 200k.
Haiydar yace"Falmi bayan kud'in sadakin dana biya?.
"Ki sani bana son miki ta k'arfi.
"Ina rok'onki da kiji tausayina, ba wai don bana da kud'in da zan baki ba, a'a saidan hakan baida kyau.
"Kuma duk irin k'yautata miki danakeyi ba k'ya gani?.
"Yaushe na baki 300k fa falmi?.
Tsaki ta ja ta mik'e, za ta sauk'a daga kan gadon, ya fincikota, sak'onni yasoma aika mata dashi.
Duk iya k'arfinta ta kasa kwacewa sai tasoma masa ihu.
( kira gareku mata masu irin wannan halin, kusani baida kyau, Allah da mala'ikunsa, suna tsine wa duk matar da mijinta ya nimeta, ta juya masa baya. Ko kuma ta nimi sai ya bata kud'i kafin ya kusance, ta kamar yanda Falmi takeyi. Dan Allah ku kiyaye inda maiyin haka ku daina. Kisani duk randa kika faranta wa mijinki rai shi da kanshi zakiga canji a gunsa kuma komai kika roka matsawan na dashi zai baki, amma ba kice sai ya baki kafin ki basa hakkinsa ba, hakan haramu ne. Allah ya tsaremu da aikata hakan ameen).
Bai k'yaleta ba sai kusan asuba, wanka yaje yayi ya kwanta, yana tunani irin halin Falmi sam baida k'yau.
Gidan Hajiya kuwa, da safe Indo tayi wanka tasaka Uniform d'inta purple da light purple, riga da skirt sai barret. Hijab ta d'auko ta d'aura akan kayan, Indo tayi kyau sosai,
Hasna ne ta kaita school d'in.
Suna zuwa school d'in registration office suka nufa.
Bayan sun gaisa da uncle d'in jiya, Hasna tace"gata nan mun kawota.
Uncle d'in yace"ok wata yarinya ya kira, yace"ta je SSS1A ta kira masa Sadeey S Adam da Sanah S Matazu.
Ko da yarinyan ta tafi, bata dad'e ba saiga su sunzo.
Nan ya had'a su yace"su je su zauna tare.
Sanah da Sadeey suka kama hannu Indo suka nufi class. Hasna kuma ta wuce school d'inta itama.
*MASU NIMAN WANNA BOOK 'DIN DA WA'YAN DA SUKE MIN MAGANA TA PRVT, PLS KUYI HAK'URI SAK'ONNI YANA YAWA, BA WULA'KANCI BA. KUNA TAMBAYA A GROUP DAN ALLAH. KUMA 'YAN GROUP MAI SHI KUNA BAYARWA COS MUTANE SUNA YAWA, KUMA GA MESSAGES 'DIN MASU YIN COMMENTS, SUMA ZAN MUSU REPLY, INA HÀU DA NIYAR INA GA SAK'O IN CIGABA DA TYPING, AMMA SAI NA TSAYA TURAWA MUNAE, WASU IN BAN TURA MUSU AKAN LOKACIBA SUNA FA'DAN BAK'AR MAGANA DUK IYA K'OKARIN DANAKE AMMA BASA GANI, DAN ALLAH FANZ A TAIMAKA ANA TURAWA A GROUPS IN AN TAMBAYA PLS N PLS*
GA WANNAN KUYI HAK'URI BAYAWA KAINA YA DAMEN DA CIWONE NASO NAYI YA FI HAKA.
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
0 comments:
Post a Comment