New Post

ABUBUWA BAKWAI (7) ABIN KULA GA DAN'ADAM

1. Duniyar da za a barta, me ya kawo hadama? 2. Dukiyar da za a lissafa daya bayan daya, me ya kawo tarata? 3. Rayuwar da zata kare, ina wani farin ciki? 4. Yarintar da tsufa zai zo mzta, me ya kawo takama? 5. Ana sauraren mutuwa, ina wata walwala? 6. Jikin da zai zama gawa, me ya jawo dagawa? 7. Karshe dai makomarsa kabari, me zai sa alfahari? Wanda ya manta da wadannan a ina ya bar hankalinsa? Allah yasa mu dace, yayi mana kyakkaywan karshe. Ameen!

KADA KA RAMA CUTA GA WANDA YA CUCEKA!

Kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka, kai kayi hakuri. Zaka samu abu biyu sakamakon hakan; * Na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. * Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

KADA KA BARI ZUCIYARKA TA ZALUNCEKA!

Kada ka sale zuciyarka ta zalunceka, tabbas zaluncin zuciya ga gangar jiki yake komawa, idan akayi wasa ya zamanto ya shafi rayuwa. Assasa bak'in tunani, yawan zargi da rashin tabbas akan wani aiki, zato, shakku ko kokwanto akan wani al'amari batare da tantance gaskiyarsa ba, shine zaluncinzuciya akan dan Adam. Maza ka hana zuciyarka don akwai hadurra dubu akan hakan.

MAHAKURCI MAWADACI

Tabbas ba kowane dandanon magani ne ke da dadi ba, amma babu shakka shine abu mafi dacewa ga dukkan mara lafiya. A lokuta da dama rayuwa takan dakeka da guduma ta jefaka acikin wani mawuyacin hali, kayi ta fama amma tayi maka tutsu. Amma idan kayi hakuri sannu ahankali zata kwaranye. Hakika ba duk abinda rai yake so yakan samu ba, amma bukata bata taba sauyawa ba kuma bata taba karewa ba. Don haka ka shirya bukatunka da kyau ka bisu daya bayan daya sannu a hankali, kayi gwa- gwarmaya, sannan kayi juriya. Tabbas mafarkinka zai zama gaskiya.

KO KA SAN?

Rayuwa bakin alqalami ce tana bukatar kaifi sannan tana son tsini. Kaifin don ka yanki magauta, tsinin kuwa don ka soki makiya. Haka zalika rayuwa kamar randar ruwan sanyi ce ta kasa tana bukatar tanaji da adani, kodn wata rana ka shayar da masoyanka. Da kyau ka lura da abu biyu a rayuwa; 1. Ka lura da mai zaginka mai aibantaka wata kila wata rana zai iya zama masoyinka mai yabonka 2. Ka lura da masoyinka na kusa mai yawan ambaton alkhairinka, wata kila wata rana zai iya zama makiyinka mai zaginka.

Thursday, 17 August 2017

BABBAN KUSKURE.... 237-238

[4:50PM, 7/22/2016] Rash Kardam��: ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-237~238.*

Falmi ta ci gaba da ce wa"a yanzu kam na gane hanya kuma na rungumi kawaye na na kirki sune Mesha luv da Zahra BB sune masu sona da gaskiya, kamar yanda naga 'Yar uwata Aisha bata da kawayen da suka fi mata Sanah da Sadeey don haka tashi ki fita bana son ganinki". Gwantsi ta tsaya tana mata kallon mamaki ganin bazata fita ba Falmi ta d'auko waya ta ce"ko ki fita ko na kira Haiydar", jin haka yasa Gwantsi fita ba shiri tana zuwa k'ofa taga Haiydar wanda duk abunda sukeyi yaji, Falmi da sauri taje ta rungumesa ta masa sannu da dawo hannusa ta kama ta kaishi d'aki tare da rugemasa kayan jikinsa sai da yayi wanka ta kawo masa abinci a baki take basa, Haiydar ya kalleta ya ce"Alhamdulilah! Tabbas yau ina farin ciki kuma na yarda matata Fatima ta nutsu kuma ina gode ma Allah da ya kawo Aisha cikin rayuwan mu don yanda nake samun kulawa da k'auna daga Falmi ba tare da na biya kud'i ba". Ya karashe maganar cikin zolaya dukan wasa ta kai masa tare da rungumesa ta na sha fa kansa, suna haka aka kwan-kwasa k'ofat suka bada izini a shigo Aisha ce tashi go rik'e da hannu Abdul~shakur yaro mai kyau da gudu yazo ya haye Baban sa yana masa oyoyo Aisha da Falmi sai dariya suke masa nan ya biye masa sukayita wasa.

              *ALHAMDULILAH!*
   
Dukkan yabo ya tabbata ga ubangiji sammai da kassai , nan na kawo k'arshen wannan labari na *BABABN KUSKUREN DANA TAFKA* kuskuren dana yi aciki ya Allah ka yafe min ka bani ikon gyarawa Ameen.

         
   *KIRA GARE KU MAKARANTA*

Ina fatan kun gane sak'on da na isar a ciki kusani ba wai ina nufin d'aukar 'Yar aiki da matsala ba a'a sai dai kamar yanda Falmi ta sake ma 'Yar aiki komai na Mijinta hakan ba dai-dai bane, sannan kuma da masu halayyan hana mijinsu hakkinsu sukuma nuna cewa sai aun basu kud'i kafin su biya musu buk'atarsu na Auratayya wannan ba dai-dai bane haramun ne ke/ni dukkan kowace ta san kanta inda mai yi sai ku gyara Allah ya bamu ikon bin dai-dai Ameen.

           *SADAUKARWA*

  Na d'auki wannan *LITTAFIN* mai suna *BABAN KUSKUREN DANA TAFKA*na sadaukar wa *AISHA MUHAMMAD (MAMAN ADUL~SHAKUR)* Allah ya bar k'auna.

   
               *KUN CAN-CANCI IN YABA MUKU*
Kungiyar *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* Allah ya bar mu tare ya kuma bar k'auna.

           *GODIYA TA  MUSAMMAN*

       Dole na ambace ku don yanda kuka bada gudumawa a cikin littafinnan kuma ina alfahari da ku a ko da yaushe Godiya mai tarin yawa gareku;

MARYAM ALKALI(MAMU)
SANAH S MATAZU
MUNAY.

          *JIN-JINA GA K'UNGIYA*

  *_EXCELLENT WRITERS, EXTREME HAUSA WRITER, WISDOMS HAUSA WRITERS, GALAZY HAUSA WRITERS, BEST HAUSA WRITERS,_*

           *INA GAIDA 'YAN GROUPS 'DINA*

   _*RASH KADAM HAUSA NOVEL 1,2*_

         *MASOYANA*

      Ina mik'a godiya ga dukkan masoyana ina ganin sak'onnin ku kuma *Allah* yabar k'auna Ameen.

*_MY LOVELY AISHA S MAZOJI KINA NAN ARAINA BAN BAN MANTA KI BA ALLAH YA BAR K'AUNA_*

    
*SAI KUNJINI A SABON LITTAFINA MAI SUNA*

_*'YAR MAFIYA, 'YAR MAFIYA*_

For corrections/comments
      Here is my number����

     08069420822

Taku a kullum mai k'aunar ku

*Rashida Abdullahi Kardam*
*Rash Kardam��.*

BABBAN KUSKURE... 235-236

[4:42PM, 7/22/2016] Rash Kardam��: ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-235~236.*

4yrs latter
Wani kyakyawan Yaro na hango rik'e da teddy a hannusa yana gudu yana dariya ko dana kalli wanda yake bi wani kyakyawa ne fari sol tamkar shi yayi kansa ko dana kalleshi da kyau sai naga kaman Haiydar wata kyakkyawar mace ce ta fito ta ce"Abban Abdul in kun fara wasa kai ma sai kadawo kamar wani k'aramin yaro ya tsaya jin maganar ta Abdul~shakur ne yazo ya kama Abban sa ya dariya ya ce"na kama na kama". Haiydar yayi dariya ya d'agashi ya cilla shi sama duka suna dariya, Assalamu'alaikum jin sallama duka suka juya sai da suka kalli mai sallaman sosai suka gane Falmi ce da sauri tazo ta durk'usa tana basu hak'uri Haiydar ya kau da fuska ya tashi zai tafi Aisha ce tazo ta rungume Falmi ta ce"Aunty na ni bakimin komai ba na yafe miki Aunty na", Falmi ta share hawaye ta ce"nagode ina rokinki dan Allah ki rok'ar min Haiydar da ya mayarni d'akina wallahi nayi nadama". Ta karashe maganan tana kuka Aisha ta rungume ta tace"Aunty kar ki damu Haiydar zai mai daki kuma Haiydar na sonki kawai zugan kawaye ne daman". Falmi tayi godiya ta tafi, Aisha da daddare tasamu Haiydar da maganan dawo da Falmi ya nuna bazai dawo da ita ba, ganin tayi yaki hakan yasa tayi fushi ta juya masa baya kusan kwanan su uku basa magana kafin Haiydar yaga bazai iya jure rashinta ba da kansa yazo ya bata hak'uri ta ce"in ka ga na hak'ura ka mayar da Aunty na". Haiydar da kyar ya yarda sai da suka sanar da su Hajiya tayi murna don ita ma Falmi har gida taje ta bata hakuri.
Aisha ita da Hasna sukayi ta jagale Haiydar shi ya basu kud'i suka had'a kayan akwati aka biya sadaki ranar jumma'a aka d'aura aure, dadadare amarya ta tare a gidan ta Haiydar bayan ya shigo sai da ya tarasu ya musu nasiha tare da kashedi banda fad'a bare hayaniya suka amsa, Aisha ita taje ta taya Haiydar shiryawa ta basa jallabiya mai kyau sabo ta fesheshi da turare ta kama Hannusa kafin ta rakosa Har d'akin Falmi bayan sun shiga da sallama Aisha tana ta addu'a a zuciyar ta don wani irin kishi takeji amma tana ta addu'a ta kori shaid'an cikin sanyi murya ta ce"Aunty ga Ango ki na kawo miki ina muku fatan alkairi sai da safe". Tana fita da gudu tayi d'aki tanahawaye niko Rash na ce"hmm kishi kumallon mata",  Falmi ita ta matso kusa dashi ta fara shafa sa daga haka na fito, washe gari Aisha ta shirya musu karin kumalo mai lafiya.
Bayan kwana biyu zaman lafiya a gidan Haiydar ba'a magana dukkansu suna girmama junasu, yau k'awar Falmi ne Gwantsi ta kawo mata ziyara ganin irin zaman da sukeyi nan ta fara hure mata kunne tun kafin tayi nisa Falmi ta ce"kee tsaya da fa da yanzu ba d'aya band in ada kin zugani na d'auka yanzu na nutsu nasan mai nakeyi, dakam nasan *NA TAFKA BABBAN KUSKURE* amma yanzu ina cikin hankali na kinaso in fito muna yawon kan titi tare tare".

                *®NWA*

                *DEDICATED TO*
          *AISHA MUHAMMAD*
    *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

           *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 233-234

[4:09PM, 7/22/2016] Rash Kardam:
BABBAN KUSKEREN
       DANA TAFKA
                
                   
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-233~234.*

Zuwa yayi ya rungumeta ya ce"baby na kinyi kyau sosai", murmushi tayi ya lakaci hancinta ya ce"kullum kyau kike k'arayi ina rok'on Allah banu baby mai kama da ke". Da irin wannan kalaman ya lallab'a Aisha suka lula duniyar masoya. Washe gari Haiydar ya fita zuwa aiki Falmi ta tattari kawayen ta 'Yan bariki suka zo da niyar dukan Aisha kowacce da bulalarta a hannu ana haka sai ga Haiydar ya dawo ganin su yasa ya kira jami'an tsaro aka tattaresu ko wacce taji a jikinta suna kulle a gurin jami'an tsaro, cikin Falmi ya faro ciwo kafin me sai ga jini wanda hakan yasa aka kira Haiydar da gaggawa aka kaita asibiti suna zuwa ana dubata cikin inkon Allah suka zai da jinin suka shaida ma Haiydar cewa magani Hana Haihuwa ta sha wanda yayi wa haifarta illa, nan ran Haiydar ya k'ara b'aci sosai, sai da aka taimaka mata jini ya tsaya, tana farfad'owa ya ce"Fatima naga abu abunki yayi yawa don haka in kin samu sauki ki wuce gidan ku". Ya juya ya fita hawaye ke zuba afiskansa tabbas Haiydar na son Falmi amma ita tana bin zugar kawayen banza shi yasa da kishin hauka dake damunta.
Bayan kwana biyu Haiydar, da Sarkin Fulani dasu Lamid'o da Hajiya suka tafi Yola tabbas Aisha taga ga tanta da dangin ta ko ina sai murnan ta akeyi. Batun gona ko Sarkin Fulani ba k'aramin kud'i ya kashe a gun ba an k'awata gun sosai gwanin burgewa wanda aka sanya masa suna *AISHA VILLA GARDEN* sai da akayi bikin bud'e gurin Lamid'o ya damk'a amanar gurin wa Maharbin nan daga nan kuma aka d'ibi ma'aikata a kauye da birnin Yola, kafin suka dawo lokacin Aisha ta k'ara kyau tayi haske ga wani kwad'ayin da takeyi kulum sai tasha ice cream rigimar yau daban na gobe daban. Yau ma kamar kulum Haiydar ya dawo Aisha ta tasashi gaba da shagwab'a dole sai sunje shan ice cream ba yanda ya iya dole ya fita su tafi, bayan sun saya ice cream dai-dai zasu shiga mota Aisha ta hango wasu mutane take ta rud'e tafara kuka ta mak'ale Haiydar yayi ta tambayan ta duk ta rud'e sai da Haiydar ya sanya bakinsa cikin nata ya bata wani sassayan kisses kafin ta dawo hayyacinta rungeta yayi ya ce"mai ya faru wa ya tab'a ki mai ya tsorata ki". Cikin kuka ta ce"sune sune". Haiydar ya ce"waye su d'in?". Aisha ta ce"sune suka d'aukeni lokacin dana b'ata". Haiydar ya ce"what!!" Gwada min su nan ta nuna masa su suna shiga gun shan ice cream d'in Haiydar yasa ta a mota ya ce"ki zauna anan karki fito", rikesa tayi ta fara kuka dan Allah ka kyalesu kar su cutar da kai". Murmushi yayi ya ce"karki damu kimin addu'a Allah zai kareni". Kai ta gir-giza masa wayansa ya d'aga ya kira 'Yan sanda da suke kusa ya na zuwa ya bada umurni aka rufe gun aiko saiga police nan suka shiga aka kamasu duka, nan yasa aka tafi dasu ya ce"bari ya mayar da matar sa gida". Gidan Hajiya ya kaita ya koma gun aiki. Azaba akayi ta gana wa mutane nan da kyar suka fad'i wacce ta sa su ran Haiydar ya k'ara b'aci da kansa yaje har gidansu Falmi yasa aka kamota sai da ta daku a gunsa sosai kafin ya ce"ki sani na sakeki saki d'aya tunda har haukan ki ya kai kiyi tunanin kisa". Falmi taji wahala har tayi nadama abunda ta aika, ga wahala ga auren ta ya mutu,.***************
Bayan wata takwas Aisha na hango da zungureren ciki tana tafiya tana ciza baki ta dafe cikin ta Haiydar ne ya fito daga d'aki da sauri ya riketa ganin kamar nak'uda ne da gudu yayi d'aki ya d'auko akwatin kayan haihuwar ta ya fitar ya dawo ya sun kuceta sai asibiti cikin ikon Allah bata dad'e tana nak'uda ba ta haifo baby boy d'inta, nan fa Haiydar yayi ta kiran 'Yan uwa yana fad'a musu kasancewan lafiyarta lau ta haihu hutawa tayi aka sallame su kafin kace me gida ya cika da 'Yan uwa da abokan arziki.
Bayan kwana bakwai ranan suna yaro yaci sunan *_ABDUL SHAKUR_*  Yaro kyakyawa gwanin burgewa bikin suna yayi kyau ida muka samu kyatuttuk'an zannuwa ne mai hoton yaro da Al-qur'ani mai girma abun sai wanda ya gani haka aka watse.

               *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHA MUHAMMAD*
     *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                *RASH KARDAM*

BABBAN KUSKURE....231-232

[3:18PM, 7/22/2016] Rash Kardam��: ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-231~232.*

Tuni ya fara rikita ta da salon soyayyan sa wanda ganin yafi k'arfin idona yasa na tattara 'yan matan k'afana nayi gaba, ina daga k'ofar d'aki ina jiyo kukan Aisha wanda ba halin na kai mata taimako haka na zauna jigum, sai kusan k'arfe uku Haiydar ya saurara mata, Aisha in banda hawaye ba abunda takeyi ni ko Rash ina gefe na ce"yau Ashanty anji maza bakin tsiwa ya mutu.....lol..". Haiydar ruwan zafi ya had'amata sai da yayi wanka kafin yazo ya taimaka mata sam tak'i yarda su had'a ido da kanshi ya mata wanka tukun ya barta tayi wankan tsarki, sai da tafito ya mik'a mata wasu kaya kafin ta sanya harda hijab a ciki tayi sallah kafin ya kawo musu abinci suka ci. Haiydar ya kalli Aisha ita duk kunyansa takeji sabida in ta tuna irin sambatun da yayi jiya sam bata son su had'a ido, hab'arta ya kama ya d'ago fiskanta ido ta lumshe cikin sanyin murya Haiydar ya ce"Aisha Allah yayi miki albarka na rasa kalman da zan gode miki ila wannan yukurci". wani d'an k'aramin a kwati yaciro mai kyalli ya bud'e tare da zaro wani zobe white gold mai kyalli da haske wanda ni kaina Rash sai dana kare fuskata da tafin hannuna sabida hasken yana kashe min ido, ko da na duba da kyau jikin zoben naga ansa A&A forever, yana sanya mata yayi kiss d'in zoben don bak'aramin kyau yayi mata ba hannu ya rike yana murzasu tare da janyota jikinsa yana mata wasu kalamu masu dad'i acikin kunnenta wanda duk sonjin gulmata ban jiyo mai ya ce ba.
Hajiya ko ganin sak'on sai da hankalinta ya tashi tabbas tasan Haiydar yayi hak'uri sosai, dole ta bashi matarsa don taga ya nitsu sosai kuma ya damu da Aisha, ganin matarsa ce bata kawo komai ba amma zuciyarta na d'ar-d'ar. Basu bar gidan ba sai bayan magriba suka d'au hanya sai da yabiya da ita super market ya mata sayya masu yawa suna isa harabar gidan sai da yaga tashiga falo ya juya ya tafi sabida yasan bai da gaskiya shiyasa bai shiga ba. Aisha tana shiga sai da ta d'an lek'a bata ga kowa ba hakan yasa ta fara tafiya a hankali, Hajiya da tafito daga kitchen ta hangota ganin tafiyar da takeyi tuni ta d'ago abunda ya faru a zuciyar ta ta ce"lalle Haiydar ya gwada min shi d'an yau ne ai ban isa ba tun kafin ya sanya na fara jin kunya gwara ya d'au matarsa su k'ara gaba". Tana fitowa dai-dai Aisha na hawa matakala Hajiya ta ce"ah! Aisha har kun dawo", cikin jin kunya ta sun kuryar da kanta ta amsa da "eh mun dawo". Hajiya ta ce"to yayi kyau kije d'aki Hasna zata kawo". Miki abinci, Aisha ta ce"Hajiya a k'oshe nake naci abinci a can"  Hajiya ta ce" to shikenan". Aisha ta wuce d'akinta sai da tasha maganin  Haiydar ya bata kafin ta kwanta sai ido ta lumshe tana mai tuna abunda ya faru tsakanin su da nan wani tunani ya fad'o mata yanzu fa in da rabo hala ciki ya shigeki, murmushi tayi kafin ta shafa cikinta haka har bacci ya d'auketa.
Yau Aisha ta kammala jarabarwata wanda aka shirya musu liyafa nagani na fad'a Sarkin Fulani da shi da Lamid'o sun halarci bikin walimar abun dai sai wanda ya gani walima akayi na gani na fad'a, bayan walima da kwana biyu Hajiya ta shirya 'Yarta da kanta ta mayar ta gidan Haiydar tare da mata nasihu masu sayaya jiki. Da dadare Haiydar da wuri ya dawo Falmi ya samu a falo tayi d'aurin rashin mutunci sai kad'a k'afa takeyi. Ganin ko kallonta bai yi ba zai shiga d'akin sa tazo tasha gabansa ta ce"to muna fuki wai mai kake nufi ne kasani lokaci yayi da zaka saki Indo, ko ka manta kai da bakin ka kace baka sonta sai yanzu kuna neman ku kareta wai tasamu ubanta mtss zaku raina min Hankali ai 'Yar shehe 'Yar she......". Wani kyawawan mari Haiydar ya bata nan tafara shirin kama sa da kokuwa shi kuma bai son yawan dukar mace kawai ya jata zuwa d'akinta ya kulleta ta baya, d'akin sa yaje yayi wanka kafin yasaka kayan bacci d'akin Aisha ya shiga ya ganta cikin wasu mayun kayan bacci wanda dashi da babu duk d'aya.

                 *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHA MUHAMMAD*
      *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                 *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 229-230

[10:50PM, 7/21/2016] Rash Kardam��: ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-229~230.*

Da daddare haka suka sha hiransu cike da k'aunan juna sai kusan goma Sarkin Fulani ya musu sallama shima Lamid'o d'akinsa ya tafi da ya kwanta yau jinsa yake cikin farin ciki, Hajiya ta kalli su Aisha ta ce"kuma ku tashi ku tafi d'aki ku kwanta dare ya soma yi". Duka suka mik'e tare da mata sallama, Haiydar ko ya marai-raice fuska Hajiya duk ta d'ago nufinsa ta ce"kai kuma mai ka tsaya yi da bazaka tafi masaukinka ba ne?". Jiki ba kwari Haiydar ya mik'e ya nufi d'akin sa shima tukun Hajiya ta tafi nata. Aisha tana shiga d'aki wanka ta fad'a Hasna kuwa kitchen taje had'a ruwan zafi take so tasha kafin ta kwanta, Haiydar ganin Hajiya ta tafi d'akin ta ya dawo cikin sand'a ya tura d'akin su Aisha nan ya ga ba kowa sai da ya rufe k'ofar tukun ya k'arasa ciki  k'aran ruwa yaji a bayi gefen gadon kusa da bayi ya zauna don kar ma tana fitowa ta gansa, Hasna da take shirin fitowa ganin Haiydar ya shiga d'akin su tayi murmushi sai ta nufi dining kawai don ta sha ruwan zafinta a can.
Aisha da 'yar wakanta fito d'aure da tawul iya cinya sam bata lura da mutum ba dake ta na goge kanta zagawa yayi ta bayanta ya rungumeta tare da zare d'an k'aramin tawul d'in, cikin razana tayi tana shirin sakin ihu ya toshe mata baki da hannusa a kunne ta ya rad'a mata" nine mijiki Haiydar kuma d'an uwanki", dumm! Taji gabanta ya fad'i juyo da ita yayi duk kunya ya ishe ta, hannu tasa tana kare k'irjinta, ya saki murmushi ya ce"mai yasa kike rufe min abunda yake halal a gareni kuma nake marari ganinsu tare da begen...". Magana kunya ta bata sai ta rufe ido hannuta ya kama ya kawar daga k'irjinta tare da janta zuwa gado cikin muryan kuka ta ce"Ya Haiydar miye haka? Dan Allah ka bari mai kazo yi a nan?". Murmushi yayi ya ce"yau nazo karb'an hakkina da ya dad'e shekara da shekaru ana min rowa kai ta gir-giza masa tare da k'ok'arin turjewa sai da ya kaita kan gado ya kwantar da ita, salon k'auna iri-da-kala yasoma nuna mata wanda ya fi k'arfin in tsaya zayya ne mu ku acin nan. Hasna ko ganin haka da man akwai d'aki wanda da komai a ciki d'akin hajiya ta koma ta dauko kayan bacci, tazo tayi wanka ta kwanta a nan. Haiydar ko sai da yayi wasa da Aisha son ransa ya kuma tabbatar da ya gamsu kafin ya mik'e cike da nishad'i ya fito cikin sand'a ya koma d'akinsa wanka yayi ya kwanta yau yana mai jinsa cikin farin ciki kasa bacci yayi can iya tuna mai ya faru sai ya saki lallausar murmushi tare da buga hannusa a katifa alamar jin dad'i.
Aisha ma wanka ta sakeyi kafin tazo ta kwanta tana mai tunano abunda ya faru haka har bacci ya d'auketa. Da safe bayan sun karya sun dawo falo an gaggaisa yau Aisha sai wani sunne kai takeyi Haiydar ko idonsa akan ta yake suna had'a ido zai kashe mata ido d'aya, Sarkin Fulani ne yayi gyan murya sai da yayi addu'a kafin ya fara da cewa"hukuncin dana yanke shine da zaran Aisha ta kammala jarabawan ta zamu tafi Yola a kaita taga dangin Mahaifiyar ta sanna  gonar Lamid'o inaso zamu mayar dashi kamfanin yin su Madara da yogurts san nan gefe d'aya kuma a mayar dashi gidan gona gefe d'aya kuwa zamu k'awata shi ya dawo gun tutawa zamu zuba k'ananun namun daji don su kawata gun da d'akunan hutawa da gun abinci mai kyau, hakan zai kawo kud'i kuma wasu manya zasuna zuwa gun kasancewar yayi wajen gari kuma ba hayaniya a gun". Ya d'ago ya kallesu ya ce"kunaga hakan yayi ko da wani tsarin da yafi hakan?". Hajiya da Lamid'o suka amsa da yayi nan ya ce"to na nasa an muku komai sabida komawarku Bauchi don gobe Aisha tana da jarabawa". Daga nan kuma suka ci gaba da hiransu. Da yamma kuwa sarkin Fulani har dashi da Lamid'o aka musu rakiya zusa filin jirgi suka dawo Bauchi. Washe gari Aisha ta nufi makaranta nan taba masu Sadeey da Sanah labari ba k'aramin murna suka mata ba da samun Mahaifinta.
Haiydar ko yana komawa gida ya samu Falmi amma sai me fiskanta yaga kamar alamun nadama da murna ta tarbesa don ita damuwarta taji ina yaje sai da ya huta cikin kissa take tambayarsa ko da yabata labari nan fa ta dira tsalle ta mik'e ta ce"ina wannan k'arya ne kawai baki kuka had'a don ku rufa mata asiri"  nan fa rikici ya kaure a tsakanin su daga k'arshe falon ya barmata ya koma d'akinsa. Bayan kwana biyu duk damuwar sa ya ga Aisha gashi yanzu saura mata jarabawa d'aya ta gama, zuwa makarantar yayi yasamu suna jarabawa ya tsaya ya jirata sai da suka fito yasa aka kirata tana zuwa ya ce"ki shiga mota", sam fiskan sa ba alamar dariya hakan yasa ta shiga da sauri ya ja motar ya bar harabar makarantar gudu yakeyi sosai hanyar UNGUWAN SARAKUNA ya nufa, cikin razana Aisha ta ce"lafiya yanaga ba hanyan gida ka nufa ba?". Wani kallon da ya aika mata dashi yasa tayi shiru har suka isa wani k'ofar madai-daicin gida mai kyau horn yayi mai gadi ya bud'e masa yana shiga ya ajiye motarsa ya zago ta gun Aisha fiska a d'aure ya ce"matsawan in kika min gardama to kinsan sauran". Yau kam ya dawo mata Haiydar d'insa na da tuni wani tsoro ya shige ta hannun ta ya kama tare da mannata da jikinsa suka nufi cikin gidan suna shiga ya kulle k'ofar tare da zare makullin yasa a aljihun sa, wani d'aki ya nufa da ita, suna shiga ta ja ta tsaya a k'ofar d'akin cikin dauriya ta ce"wai lafiya yau kuwa mai yasa ka kawo ni nan gidan?". Wani mayen kallo ya bita da shi tare da matsowa kusa da ita ya ce"yau hakkina nake buk'ata a gunki nagaji da jamin rai da kikeyi". Janyota yayi ta fad'a jikinsa tare da rufe k'ofar d'akin tafara k'ok'arin kwace kanta wani tsawa ya daka mata ai ba shiri tayi shiru sai hawaye ke sauka, wayarsa ya ciro ya tura ma Hajiya message kamar haka.

           *_Assalamu'alaikum_*

        _Hajiya barka da rana kar a tura d'auko Aisha naje d'auko ta muna tare yanzu haka da ita, zamuje unguwa karkuga shiru sai mun dawo_.

Yana tura ma Hajiya yana ganin ta bud'e sak'on ya kashe wayarsa ya sa a gen gado, hannunsa yasa ya janye karamin hijab d'in Aisha tare da sanya hannusa a gashin kanta ya fara shafawa Aisha ko sai hawaye takeyi, hannusa ya zura ta cikin riganta ya balle bra d'in ya fara.....

             *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHA MUHAMMAD*
       *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                 *_RASH LUV_��*

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE.... 227-228

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-227~228.*

Na tattara dukkan shanuna da 'yar sanda na muka d'au hanya sai da mukanshiga cikin daji kawai mutanen nan suka b'ullo mana ba k'aramin razana mukayi ba amma duk da haka nayi iya k'ok'arina akan su amma Allah baiyi ina da nasara ba haka suka kwad'a min sanda a kafad'a ganin bazan iya kare kaina ba shine na wurgo ma Safinatu jakata da kud'i a ciki da awarwaron da Hajiya ta ban sannan da hoton mu da ku da nawa ni da ita wanda mukayi a auren mu". Ya nisa tare da gyara zama ya d'an kurb'i ruwan Faron da ke gefensa ya ce"kunji yanda muka rabu da Safinatu". Duk fiskan su d'auke da hawayen tausayi Sarkin Fulani ya share kwala ya ce"muna jinka yanda ku ka k'are da mutanen". Lamid'o ya ci gaba da ce wa"bayan tafiyar Safinatu tana kuka tana waige na haka mutanen nan suka kwada min sanda na suma a gun, sukuma suka kad'a shanuna suka tafi, ana haka sai ga wani Maharbi ya zo ganin halin da nake ciki ya d'aukeni yaje ya ta min magani, da ikon Allah ciwukan dana ji duk sun warke amma me sai na samu tab'in hankali haka Maharbin nan yayi ta jinyana tsawan shekara goma sha bakwai kafin da ikon Allah ya samomin magani shekara guda da rabi yayi yana min jinya da maganin cikin ikon Allah na samu lafiya, daga nan ya tambayeni labari na na basa labarina tun daga kawo ni da akayi Yola har zuwa lokacin. Maharbin nan shi ya tara 'Yan uwansa da mai gari aka karb'a min shanuna ko da suka dawo hannuna sai na saida guda uku a cikin garin yola na dawo kauyen fofure na sai babban fili a jeji wanda filin ba k'arami bane(kunsan filin kauye ba zada sosai). Nan na sake biyan kud'i aka kewaye min da wayoyi nazuba shanuna aciki sannan nasaka su kaji da raguna da akuyoyi da talotalo da agwagi ruwa, bayan dana gama aikin sai na damk'a wa Maharbin nan gonan a hannusa zai na kula dasu don ana saran koyayen zabbi da sayan madaran shanu a gun na masa sallama na sanar da shi zanzo Mahaifata na ga iyayena da Matata da na turota tare da cikin da ke jikinta nan na kamo hanya zuwa Gombe, to kunji labarina". Wannan karon harda Haiydar a 'Yan yin kwalla labarin gwanin ban tausayi. Sarkin Fulani cikin fushi ya ce"yanzu abinda Hajiya k'arama zata min kena  batare da b'ata lokaci ba ya kira police ya ce su zo gidan sa yanzu-yanzu".
Hajiya k'arama da ta lab'e tana jin duk abunda ya faru cikin sauri ta koma d'akin ta tafara shirya kayanta a k'aramin jaka sai ta nufi d'akin Sarkin Fulani ta d'ibi kud'i da dollars cikin jaka, nan ta fara dariyan mugunta tasan wa'yan na  kud'in sun isheta rayuwa a ko ina take ga kuma wanda ta tarasu a account d'inta K'ofar baya tabi tayanda sarki bazai ga fitarta ba cikin hanzari take tafiya dan kar a ganta.
A falo kuwa police sunzo d'akinta aka nufa kai tsaye amma me sai wayam suka gani ba kowa nan suka bazama aiko suna zuwa k'ofar baya suka ga ta k'ofar a bud'e cikin hanzari suka bazama bakin titi suka hango ta tana shirin shiga napep ganin haka wasu suka tsari mashin aka bita wasu a mota
[10:29PM, basuyi nisa ba aka kamata aka sa mata ankwaf aka nufi C.I.D da ita ana kamata aka sanar ma Sarkin Fulani nan ya ce"Lamid'o muje C I D tare suka fita a jikin mota ko da suka je nan ma aka basa duk abunda aka kama a hannuta, ransa ya k'ara b'aci sai da yabata kyawawan mari masu lafiya ya kuma ce" wallahi kin cucen na yarda da ke sakayyar da ki ka min ke nan ki sani ba amfanin zamana da ke na datse igiyar aurena uku da ke kanki". Nan ya ba da umurnin abata wahala sosai tukun a turata kutu.
Haiydar ko Hajiya na mik'ewa ya nufo gun Aishat Hasna na ganin haka ta ja 'yan matan k'afar ta ta bar falon, Aisha cikin hanzari itama ta mik'e har ta fita a falon taku k'alilan yayi ya fisgota sai a k'irjinshi ta fad'o nan wani kamshi mai tattare da sanyi ya daki hancinta Haiydar cikin kwayan idonta ya fara kallo ganin haka ta lumshe ido dul jikinta b'ari yakeyi, hancinsa ya d'aura akan nata ya fara gogawa tare da sanya bakinsa cikin nata nan yaji wani laushi a labb'an ta, tun da yake da Aishat sai yau yasamu wannan damar Aisha ko k'ok'arin ta gudu take amma me hannuta ya manna da garu tare da d'aura hannusa akan nata yasona kiss d'inta kamar wani mayunwaci, duk yanda taso ta kauce ba hali gashi jikin ta na b'ari sosai hawaye ke zuba harshensa yasaka yana lasar hawayen sai da ya lashe tass, Aisha gashi ba halin tayi magana ya had'a bakinsa danata dai da ya jagwa-gwata son ransa ya saketa da gudu tayi hanyan cikin d'akinsu sai hakki takeyi cikin sa'a ba Hasna a d'akin kan gado ta fad'a tana maida numfashi sama-sama tare da lumshe ido cikin zuciyarta ko cewa take" a sai haka kiss d'innan ke da...

               *®NWA*

                    *DEDICATED TO*
             *AISHA MUHAMMAD*
      *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                 *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 225-226

Rash Kardam��  ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-225~226.*

Ba kowa bane ya turo k'ofar illa Muhammad Lamid'o d'a d'aya tilo Namiji kuma magaji ga Sarkin Fulani Gombe cikin razana da firgici Hajiya k'arama ta mik'e don ba k'aramin kid'ima tayi da ganin sa ba nan take taji wani fitsari na shirin zubo mata sai zazzare ido takeyi jikinta sai b'ari ya farayi Sarkin Fulani da kansa ya taka ya je ya rik'o hannu Lamid'o yana hawaye bai san lokacin da ya rungume sa ba farin ciki ba'a cewa komai baran Aishat da ganin fuskan sa ba tam-tama ta gane Mahaifinta ne don yawan kalon sa da takeyi a hoto, Sarkin Fulani ya kamo hannu sa ya zaunar da shi Hajiya ma kukan murna takeyi ikon Allah kenan, sai da suka zauna Sarkin Fulani ya ce"Lamid'o kaine?". Lamid'o ya ce"eh nine Abba". Sarkin Fulani ya furta ikon Allah kenan ya wuci wasa". Ya kalli Hajiyan su Haiydar ya ce"kije d'akina ki had'a masa ruwan wanka tukun ya ci abinci don naga da gajiya a tattare da shi ga alamar yunwa". Haka ko akayi nan take ta kaisa d'akin Babansu ta dawo kitchen da ita da su Aishat suka had'a masa girki mai k'ayatarwa, yana fitowa a wanka ya tarar da sabbin kayan da aka ajiye masa ya sanya ya gyara jikinsa, falo ya fito ya tarar da su, sai a lokacin idonsa ya kai kan Aishat da ta k'ura masa ido shima kallonta ya farayi cikin zuciyar sa ya ce" wannan tamkar Safinatun sa, ayya ko dai ita ce yar cikin Safinatu da taho da shi?". Hannusa yaji an rike ko da ya duba Sarkin Fulani ne ya kama hannusa duka suka nufi dining, Hajiya da kanta ta sanya ma kowa abinci ta zauna Sarkin Fulani yana mak'ale da Lamid'on sa sai Hajiya da ke kusa dashi sai Aishat a kusa da Hajiya yayin da Haiydar ke kusada Lamid'o sai Hasna a kusa dashi. Haiydar yana kallon Aishat yana aika mata da wasu sak'on ninsa, gun shiru kowa yana fama da abinci fiskan kowanne su yana d'auke da murmushi don suna cikin farin ciki bana wasa ba.
Haiydar ne ya mik'ar da k'afan sa ta k'asan dining table d'in yanda zai na tab'a k'afar Aishat babban yatsan k'afarsa ya sanya a tafin k'afar Aishat ya fara mata tafiyan tsutsa a take taji wani yarrr! saurin d'ago fiskan ta tayi karaf su ka had'a ido wani lalalusar murmushi ya sakar mata ya kashe mata ido d'aya. Sai da ta d'an saci kalon su Hajiya taga kowa na ta kai da abincin sa ta murgud'a masa baki, Haiydar yayi murmushi ya sake sosa mata k'afa harda wuce wansa zuwa sawun k'afar ta da sauri ta kau da k'afar asai Hajiya tana lura dasu ta share ne kuma taji dad'in hakan suna kammala cin abinci suka koma babban falo suka zazzauna. Sarkin Fulani ya kalli Hajiya ya ce"wai ina Hajiya k'arama ne banganta ba har a gurin cin abinci kuma yanzu ma bata fito ba ko lafiya?". Hajiya ta ce"ina ga lafiya zata fito". Sarkin Fulani ya kalli Lamid'o ya ce" zaka iya gane wannan fuska kuma da wa ta ke maka kama?". Lamid'o ya kalli Aisha sosai ya ce"tun shogowata fuskanta ke min kama da fiskan Matata Safinatu". Sarkin Fulani ya murmusa ya ce"tabbas wannan d'iyarka ce da Safinatu". nan suka kwashe labarin komai suka fad'a masa sosai Lamid'o yayi kuka ya tausaya wa Matarsa da 'Yar sa tare da mik'o hannu ma Aishat tazo yana kuka ya rungumi d'iyarsa take Aisha taji sanyi dad'i na ratsa ta wai yau ita ce take tare da Mahaifin ta daman ita ba 'Yar shege bane da ake kiranta, zanso Falmi taga gatana taga Mahaifina asai mu 'Yan uwa ne da Haiydar nan tasaki sassanyan Ajiyar zuciya, Sarkin Fulani ya ce"zan so kabamu labarin bayan barin ka Gombe yanda al'amura suka kasance". Lami'o ya nisa tare da gyara zama ya ce"bayan da muka shiga mota munyi nisa sai da muk'a k'usa shiga Alkaleri Idi driver ya tsaya", ya ce" Lamid'o bazanso na kashe ka da hannuna ba don an bani kwangilan kasheka ne Hajiya k'arama amma sabida kirkin Hajiya babba bazan ci *AMANAN* ta ba ta rik'e mu da gaskiya" Lamid'o ya ci gaba da cebwa"kafin nayi wani magana kawai ya shafamin wani abu a hanci na tun daga lokacin ban san inda kaina yake ba sai a cikin wasu kauyukan Yola na samu kai na tare da wani mutumi wanda aka had'a ni dashi dan ya baro bauchi dani gudun kar Hajiya k'arama ta ganni, mutumin nan sai da ya tabbatar da na dawo cikin hayyacina shima ya zame ya barni, a tasha kauyen ribad'o na zauna nan yunwa ya fara damuna daga nan na fara aikin k'arfi ina kula da kaina kuma na samu wani Bafulatani mukayi dashi zanna tayasa kiyo yana biya na haka muka fara randa ba kiwo inje niman kud'ina da haka har na tara kud'ad'e na sai na sayi saniya ta mace nan muka fara kiwo cikin ikon Allah ya sanya ma saniyar nan albarka tayi ta haihuwa kuma inayi niman kud'ina na sai na sai wasu da haka Allah ya azurtani da garken shanu na kuma yi suna a cikin kauyukan da ke yanki don ba mai shanuna a haka har Allah yayi na auri Matana Safinatu muna zaman lafiyan mu wasu daga cikun yan kauyen suka fara adawa da dukiyata hakan yasa suke min barazanan kisa, a haka wasu daga cikin ranar laraba da bazan manta ba suka fara bina suna neman kashe ni cikin hanzari na taho gida na umurci matata da tazo mu gudu.

                   *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHA MUHAMMAD*
     *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

           *RASH KARDAM��*

Popular Posts

 
]]>All content on thisblog are copyright protected and cannot be reproduced on other websites without permission.