New Post

ABUBUWA BAKWAI (7) ABIN KULA GA DAN'ADAM

1. Duniyar da za a barta, me ya kawo hadama? 2. Dukiyar da za a lissafa daya bayan daya, me ya kawo tarata? 3. Rayuwar da zata kare, ina wani farin ciki? 4. Yarintar da tsufa zai zo mzta, me ya kawo takama? 5. Ana sauraren mutuwa, ina wata walwala? 6. Jikin da zai zama gawa, me ya jawo dagawa? 7. Karshe dai makomarsa kabari, me zai sa alfahari? Wanda ya manta da wadannan a ina ya bar hankalinsa? Allah yasa mu dace, yayi mana kyakkaywan karshe. Ameen!

KADA KA RAMA CUTA GA WANDA YA CUCEKA!

Kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka, kai kayi hakuri. Zaka samu abu biyu sakamakon hakan; * Na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. * Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

KADA KA BARI ZUCIYARKA TA ZALUNCEKA!

Kada ka sale zuciyarka ta zalunceka, tabbas zaluncin zuciya ga gangar jiki yake komawa, idan akayi wasa ya zamanto ya shafi rayuwa. Assasa bak'in tunani, yawan zargi da rashin tabbas akan wani aiki, zato, shakku ko kokwanto akan wani al'amari batare da tantance gaskiyarsa ba, shine zaluncinzuciya akan dan Adam. Maza ka hana zuciyarka don akwai hadurra dubu akan hakan.

MAHAKURCI MAWADACI

Tabbas ba kowane dandanon magani ne ke da dadi ba, amma babu shakka shine abu mafi dacewa ga dukkan mara lafiya. A lokuta da dama rayuwa takan dakeka da guduma ta jefaka acikin wani mawuyacin hali, kayi ta fama amma tayi maka tutsu. Amma idan kayi hakuri sannu ahankali zata kwaranye. Hakika ba duk abinda rai yake so yakan samu ba, amma bukata bata taba sauyawa ba kuma bata taba karewa ba. Don haka ka shirya bukatunka da kyau ka bisu daya bayan daya sannu a hankali, kayi gwa- gwarmaya, sannan kayi juriya. Tabbas mafarkinka zai zama gaskiya.

KO KA SAN?

Rayuwa bakin alqalami ce tana bukatar kaifi sannan tana son tsini. Kaifin don ka yanki magauta, tsinin kuwa don ka soki makiya. Haka zalika rayuwa kamar randar ruwan sanyi ce ta kasa tana bukatar tanaji da adani, kodn wata rana ka shayar da masoyanka. Da kyau ka lura da abu biyu a rayuwa; 1. Ka lura da mai zaginka mai aibantaka wata kila wata rana zai iya zama masoyinka mai yabonka 2. Ka lura da masoyinka na kusa mai yawan ambaton alkhairinka, wata kila wata rana zai iya zama makiyinka mai zaginka.

Thursday, 17 August 2017

BABBAN KUSKURE.... 237-238

[4:50PM, 7/22/2016] Rash Kardam��: ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-237~238.*

Falmi ta ci gaba da ce wa"a yanzu kam na gane hanya kuma na rungumi kawaye na na kirki sune Mesha luv da Zahra BB sune masu sona da gaskiya, kamar yanda naga 'Yar uwata Aisha bata da kawayen da suka fi mata Sanah da Sadeey don haka tashi ki fita bana son ganinki". Gwantsi ta tsaya tana mata kallon mamaki ganin bazata fita ba Falmi ta d'auko waya ta ce"ko ki fita ko na kira Haiydar", jin haka yasa Gwantsi fita ba shiri tana zuwa k'ofa taga Haiydar wanda duk abunda sukeyi yaji, Falmi da sauri taje ta rungumesa ta masa sannu da dawo hannusa ta kama ta kaishi d'aki tare da rugemasa kayan jikinsa sai da yayi wanka ta kawo masa abinci a baki take basa, Haiydar ya kalleta ya ce"Alhamdulilah! Tabbas yau ina farin ciki kuma na yarda matata Fatima ta nutsu kuma ina gode ma Allah da ya kawo Aisha cikin rayuwan mu don yanda nake samun kulawa da k'auna daga Falmi ba tare da na biya kud'i ba". Ya karashe maganar cikin zolaya dukan wasa ta kai masa tare da rungumesa ta na sha fa kansa, suna haka aka kwan-kwasa k'ofat suka bada izini a shigo Aisha ce tashi go rik'e da hannu Abdul~shakur yaro mai kyau da gudu yazo ya haye Baban sa yana masa oyoyo Aisha da Falmi sai dariya suke masa nan ya biye masa sukayita wasa.

              *ALHAMDULILAH!*
   
Dukkan yabo ya tabbata ga ubangiji sammai da kassai , nan na kawo k'arshen wannan labari na *BABABN KUSKUREN DANA TAFKA* kuskuren dana yi aciki ya Allah ka yafe min ka bani ikon gyarawa Ameen.

         
   *KIRA GARE KU MAKARANTA*

Ina fatan kun gane sak'on da na isar a ciki kusani ba wai ina nufin d'aukar 'Yar aiki da matsala ba a'a sai dai kamar yanda Falmi ta sake ma 'Yar aiki komai na Mijinta hakan ba dai-dai bane, sannan kuma da masu halayyan hana mijinsu hakkinsu sukuma nuna cewa sai aun basu kud'i kafin su biya musu buk'atarsu na Auratayya wannan ba dai-dai bane haramun ne ke/ni dukkan kowace ta san kanta inda mai yi sai ku gyara Allah ya bamu ikon bin dai-dai Ameen.

           *SADAUKARWA*

  Na d'auki wannan *LITTAFIN* mai suna *BABAN KUSKUREN DANA TAFKA*na sadaukar wa *AISHA MUHAMMAD (MAMAN ADUL~SHAKUR)* Allah ya bar k'auna.

   
               *KUN CAN-CANCI IN YABA MUKU*
Kungiyar *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* Allah ya bar mu tare ya kuma bar k'auna.

           *GODIYA TA  MUSAMMAN*

       Dole na ambace ku don yanda kuka bada gudumawa a cikin littafinnan kuma ina alfahari da ku a ko da yaushe Godiya mai tarin yawa gareku;

MARYAM ALKALI(MAMU)
SANAH S MATAZU
MUNAY.

          *JIN-JINA GA K'UNGIYA*

  *_EXCELLENT WRITERS, EXTREME HAUSA WRITER, WISDOMS HAUSA WRITERS, GALAZY HAUSA WRITERS, BEST HAUSA WRITERS,_*

           *INA GAIDA 'YAN GROUPS 'DINA*

   _*RASH KADAM HAUSA NOVEL 1,2*_

         *MASOYANA*

      Ina mik'a godiya ga dukkan masoyana ina ganin sak'onnin ku kuma *Allah* yabar k'auna Ameen.

*_MY LOVELY AISHA S MAZOJI KINA NAN ARAINA BAN BAN MANTA KI BA ALLAH YA BAR K'AUNA_*

    
*SAI KUNJINI A SABON LITTAFINA MAI SUNA*

_*'YAR MAFIYA, 'YAR MAFIYA*_

For corrections/comments
      Here is my number����

     08069420822

Taku a kullum mai k'aunar ku

*Rashida Abdullahi Kardam*
*Rash Kardam��.*

BABBAN KUSKURE... 235-236

[4:42PM, 7/22/2016] Rash Kardam��: ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-235~236.*

4yrs latter
Wani kyakyawan Yaro na hango rik'e da teddy a hannusa yana gudu yana dariya ko dana kalli wanda yake bi wani kyakyawa ne fari sol tamkar shi yayi kansa ko dana kalleshi da kyau sai naga kaman Haiydar wata kyakkyawar mace ce ta fito ta ce"Abban Abdul in kun fara wasa kai ma sai kadawo kamar wani k'aramin yaro ya tsaya jin maganar ta Abdul~shakur ne yazo ya kama Abban sa ya dariya ya ce"na kama na kama". Haiydar yayi dariya ya d'agashi ya cilla shi sama duka suna dariya, Assalamu'alaikum jin sallama duka suka juya sai da suka kalli mai sallaman sosai suka gane Falmi ce da sauri tazo ta durk'usa tana basu hak'uri Haiydar ya kau da fuska ya tashi zai tafi Aisha ce tazo ta rungume Falmi ta ce"Aunty na ni bakimin komai ba na yafe miki Aunty na", Falmi ta share hawaye ta ce"nagode ina rokinki dan Allah ki rok'ar min Haiydar da ya mayarni d'akina wallahi nayi nadama". Ta karashe maganan tana kuka Aisha ta rungume ta tace"Aunty kar ki damu Haiydar zai mai daki kuma Haiydar na sonki kawai zugan kawaye ne daman". Falmi tayi godiya ta tafi, Aisha da daddare tasamu Haiydar da maganan dawo da Falmi ya nuna bazai dawo da ita ba, ganin tayi yaki hakan yasa tayi fushi ta juya masa baya kusan kwanan su uku basa magana kafin Haiydar yaga bazai iya jure rashinta ba da kansa yazo ya bata hak'uri ta ce"in ka ga na hak'ura ka mayar da Aunty na". Haiydar da kyar ya yarda sai da suka sanar da su Hajiya tayi murna don ita ma Falmi har gida taje ta bata hakuri.
Aisha ita da Hasna sukayi ta jagale Haiydar shi ya basu kud'i suka had'a kayan akwati aka biya sadaki ranar jumma'a aka d'aura aure, dadadare amarya ta tare a gidan ta Haiydar bayan ya shigo sai da ya tarasu ya musu nasiha tare da kashedi banda fad'a bare hayaniya suka amsa, Aisha ita taje ta taya Haiydar shiryawa ta basa jallabiya mai kyau sabo ta fesheshi da turare ta kama Hannusa kafin ta rakosa Har d'akin Falmi bayan sun shiga da sallama Aisha tana ta addu'a a zuciyar ta don wani irin kishi takeji amma tana ta addu'a ta kori shaid'an cikin sanyi murya ta ce"Aunty ga Ango ki na kawo miki ina muku fatan alkairi sai da safe". Tana fita da gudu tayi d'aki tanahawaye niko Rash na ce"hmm kishi kumallon mata",  Falmi ita ta matso kusa dashi ta fara shafa sa daga haka na fito, washe gari Aisha ta shirya musu karin kumalo mai lafiya.
Bayan kwana biyu zaman lafiya a gidan Haiydar ba'a magana dukkansu suna girmama junasu, yau k'awar Falmi ne Gwantsi ta kawo mata ziyara ganin irin zaman da sukeyi nan ta fara hure mata kunne tun kafin tayi nisa Falmi ta ce"kee tsaya da fa da yanzu ba d'aya band in ada kin zugani na d'auka yanzu na nutsu nasan mai nakeyi, dakam nasan *NA TAFKA BABBAN KUSKURE* amma yanzu ina cikin hankali na kinaso in fito muna yawon kan titi tare tare".

                *®NWA*

                *DEDICATED TO*
          *AISHA MUHAMMAD*
    *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

           *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 233-234

[4:09PM, 7/22/2016] Rash Kardam:
BABBAN KUSKEREN
       DANA TAFKA
                
                   
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-233~234.*

Zuwa yayi ya rungumeta ya ce"baby na kinyi kyau sosai", murmushi tayi ya lakaci hancinta ya ce"kullum kyau kike k'arayi ina rok'on Allah banu baby mai kama da ke". Da irin wannan kalaman ya lallab'a Aisha suka lula duniyar masoya. Washe gari Haiydar ya fita zuwa aiki Falmi ta tattari kawayen ta 'Yan bariki suka zo da niyar dukan Aisha kowacce da bulalarta a hannu ana haka sai ga Haiydar ya dawo ganin su yasa ya kira jami'an tsaro aka tattaresu ko wacce taji a jikinta suna kulle a gurin jami'an tsaro, cikin Falmi ya faro ciwo kafin me sai ga jini wanda hakan yasa aka kira Haiydar da gaggawa aka kaita asibiti suna zuwa ana dubata cikin inkon Allah suka zai da jinin suka shaida ma Haiydar cewa magani Hana Haihuwa ta sha wanda yayi wa haifarta illa, nan ran Haiydar ya k'ara b'aci sosai, sai da aka taimaka mata jini ya tsaya, tana farfad'owa ya ce"Fatima naga abu abunki yayi yawa don haka in kin samu sauki ki wuce gidan ku". Ya juya ya fita hawaye ke zuba afiskansa tabbas Haiydar na son Falmi amma ita tana bin zugar kawayen banza shi yasa da kishin hauka dake damunta.
Bayan kwana biyu Haiydar, da Sarkin Fulani dasu Lamid'o da Hajiya suka tafi Yola tabbas Aisha taga ga tanta da dangin ta ko ina sai murnan ta akeyi. Batun gona ko Sarkin Fulani ba k'aramin kud'i ya kashe a gun ba an k'awata gun sosai gwanin burgewa wanda aka sanya masa suna *AISHA VILLA GARDEN* sai da akayi bikin bud'e gurin Lamid'o ya damk'a amanar gurin wa Maharbin nan daga nan kuma aka d'ibi ma'aikata a kauye da birnin Yola, kafin suka dawo lokacin Aisha ta k'ara kyau tayi haske ga wani kwad'ayin da takeyi kulum sai tasha ice cream rigimar yau daban na gobe daban. Yau ma kamar kulum Haiydar ya dawo Aisha ta tasashi gaba da shagwab'a dole sai sunje shan ice cream ba yanda ya iya dole ya fita su tafi, bayan sun saya ice cream dai-dai zasu shiga mota Aisha ta hango wasu mutane take ta rud'e tafara kuka ta mak'ale Haiydar yayi ta tambayan ta duk ta rud'e sai da Haiydar ya sanya bakinsa cikin nata ya bata wani sassayan kisses kafin ta dawo hayyacinta rungeta yayi ya ce"mai ya faru wa ya tab'a ki mai ya tsorata ki". Cikin kuka ta ce"sune sune". Haiydar ya ce"waye su d'in?". Aisha ta ce"sune suka d'aukeni lokacin dana b'ata". Haiydar ya ce"what!!" Gwada min su nan ta nuna masa su suna shiga gun shan ice cream d'in Haiydar yasa ta a mota ya ce"ki zauna anan karki fito", rikesa tayi ta fara kuka dan Allah ka kyalesu kar su cutar da kai". Murmushi yayi ya ce"karki damu kimin addu'a Allah zai kareni". Kai ta gir-giza masa wayansa ya d'aga ya kira 'Yan sanda da suke kusa ya na zuwa ya bada umurni aka rufe gun aiko saiga police nan suka shiga aka kamasu duka, nan yasa aka tafi dasu ya ce"bari ya mayar da matar sa gida". Gidan Hajiya ya kaita ya koma gun aiki. Azaba akayi ta gana wa mutane nan da kyar suka fad'i wacce ta sa su ran Haiydar ya k'ara b'aci da kansa yaje har gidansu Falmi yasa aka kamota sai da ta daku a gunsa sosai kafin ya ce"ki sani na sakeki saki d'aya tunda har haukan ki ya kai kiyi tunanin kisa". Falmi taji wahala har tayi nadama abunda ta aika, ga wahala ga auren ta ya mutu,.***************
Bayan wata takwas Aisha na hango da zungureren ciki tana tafiya tana ciza baki ta dafe cikin ta Haiydar ne ya fito daga d'aki da sauri ya riketa ganin kamar nak'uda ne da gudu yayi d'aki ya d'auko akwatin kayan haihuwar ta ya fitar ya dawo ya sun kuceta sai asibiti cikin ikon Allah bata dad'e tana nak'uda ba ta haifo baby boy d'inta, nan fa Haiydar yayi ta kiran 'Yan uwa yana fad'a musu kasancewan lafiyarta lau ta haihu hutawa tayi aka sallame su kafin kace me gida ya cika da 'Yan uwa da abokan arziki.
Bayan kwana bakwai ranan suna yaro yaci sunan *_ABDUL SHAKUR_*  Yaro kyakyawa gwanin burgewa bikin suna yayi kyau ida muka samu kyatuttuk'an zannuwa ne mai hoton yaro da Al-qur'ani mai girma abun sai wanda ya gani haka aka watse.

               *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHA MUHAMMAD*
     *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                *RASH KARDAM*

BABBAN KUSKURE....231-232

[3:18PM, 7/22/2016] Rash Kardam��: ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-231~232.*

Tuni ya fara rikita ta da salon soyayyan sa wanda ganin yafi k'arfin idona yasa na tattara 'yan matan k'afana nayi gaba, ina daga k'ofar d'aki ina jiyo kukan Aisha wanda ba halin na kai mata taimako haka na zauna jigum, sai kusan k'arfe uku Haiydar ya saurara mata, Aisha in banda hawaye ba abunda takeyi ni ko Rash ina gefe na ce"yau Ashanty anji maza bakin tsiwa ya mutu.....lol..". Haiydar ruwan zafi ya had'amata sai da yayi wanka kafin yazo ya taimaka mata sam tak'i yarda su had'a ido da kanshi ya mata wanka tukun ya barta tayi wankan tsarki, sai da tafito ya mik'a mata wasu kaya kafin ta sanya harda hijab a ciki tayi sallah kafin ya kawo musu abinci suka ci. Haiydar ya kalli Aisha ita duk kunyansa takeji sabida in ta tuna irin sambatun da yayi jiya sam bata son su had'a ido, hab'arta ya kama ya d'ago fiskanta ido ta lumshe cikin sanyin murya Haiydar ya ce"Aisha Allah yayi miki albarka na rasa kalman da zan gode miki ila wannan yukurci". wani d'an k'aramin a kwati yaciro mai kyalli ya bud'e tare da zaro wani zobe white gold mai kyalli da haske wanda ni kaina Rash sai dana kare fuskata da tafin hannuna sabida hasken yana kashe min ido, ko da na duba da kyau jikin zoben naga ansa A&A forever, yana sanya mata yayi kiss d'in zoben don bak'aramin kyau yayi mata ba hannu ya rike yana murzasu tare da janyota jikinsa yana mata wasu kalamu masu dad'i acikin kunnenta wanda duk sonjin gulmata ban jiyo mai ya ce ba.
Hajiya ko ganin sak'on sai da hankalinta ya tashi tabbas tasan Haiydar yayi hak'uri sosai, dole ta bashi matarsa don taga ya nitsu sosai kuma ya damu da Aisha, ganin matarsa ce bata kawo komai ba amma zuciyarta na d'ar-d'ar. Basu bar gidan ba sai bayan magriba suka d'au hanya sai da yabiya da ita super market ya mata sayya masu yawa suna isa harabar gidan sai da yaga tashiga falo ya juya ya tafi sabida yasan bai da gaskiya shiyasa bai shiga ba. Aisha tana shiga sai da ta d'an lek'a bata ga kowa ba hakan yasa ta fara tafiya a hankali, Hajiya da tafito daga kitchen ta hangota ganin tafiyar da takeyi tuni ta d'ago abunda ya faru a zuciyar ta ta ce"lalle Haiydar ya gwada min shi d'an yau ne ai ban isa ba tun kafin ya sanya na fara jin kunya gwara ya d'au matarsa su k'ara gaba". Tana fitowa dai-dai Aisha na hawa matakala Hajiya ta ce"ah! Aisha har kun dawo", cikin jin kunya ta sun kuryar da kanta ta amsa da "eh mun dawo". Hajiya ta ce"to yayi kyau kije d'aki Hasna zata kawo". Miki abinci, Aisha ta ce"Hajiya a k'oshe nake naci abinci a can"  Hajiya ta ce" to shikenan". Aisha ta wuce d'akinta sai da tasha maganin  Haiydar ya bata kafin ta kwanta sai ido ta lumshe tana mai tuna abunda ya faru tsakanin su da nan wani tunani ya fad'o mata yanzu fa in da rabo hala ciki ya shigeki, murmushi tayi kafin ta shafa cikinta haka har bacci ya d'auketa.
Yau Aisha ta kammala jarabarwata wanda aka shirya musu liyafa nagani na fad'a Sarkin Fulani da shi da Lamid'o sun halarci bikin walimar abun dai sai wanda ya gani walima akayi na gani na fad'a, bayan walima da kwana biyu Hajiya ta shirya 'Yarta da kanta ta mayar ta gidan Haiydar tare da mata nasihu masu sayaya jiki. Da dadare Haiydar da wuri ya dawo Falmi ya samu a falo tayi d'aurin rashin mutunci sai kad'a k'afa takeyi. Ganin ko kallonta bai yi ba zai shiga d'akin sa tazo tasha gabansa ta ce"to muna fuki wai mai kake nufi ne kasani lokaci yayi da zaka saki Indo, ko ka manta kai da bakin ka kace baka sonta sai yanzu kuna neman ku kareta wai tasamu ubanta mtss zaku raina min Hankali ai 'Yar shehe 'Yar she......". Wani kyawawan mari Haiydar ya bata nan tafara shirin kama sa da kokuwa shi kuma bai son yawan dukar mace kawai ya jata zuwa d'akinta ya kulleta ta baya, d'akin sa yaje yayi wanka kafin yasaka kayan bacci d'akin Aisha ya shiga ya ganta cikin wasu mayun kayan bacci wanda dashi da babu duk d'aya.

                 *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHA MUHAMMAD*
      *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                 *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 229-230

[10:50PM, 7/21/2016] Rash Kardam��: ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-229~230.*

Da daddare haka suka sha hiransu cike da k'aunan juna sai kusan goma Sarkin Fulani ya musu sallama shima Lamid'o d'akinsa ya tafi da ya kwanta yau jinsa yake cikin farin ciki, Hajiya ta kalli su Aisha ta ce"kuma ku tashi ku tafi d'aki ku kwanta dare ya soma yi". Duka suka mik'e tare da mata sallama, Haiydar ko ya marai-raice fuska Hajiya duk ta d'ago nufinsa ta ce"kai kuma mai ka tsaya yi da bazaka tafi masaukinka ba ne?". Jiki ba kwari Haiydar ya mik'e ya nufi d'akin sa shima tukun Hajiya ta tafi nata. Aisha tana shiga d'aki wanka ta fad'a Hasna kuwa kitchen taje had'a ruwan zafi take so tasha kafin ta kwanta, Haiydar ganin Hajiya ta tafi d'akin ta ya dawo cikin sand'a ya tura d'akin su Aisha nan ya ga ba kowa sai da ya rufe k'ofar tukun ya k'arasa ciki  k'aran ruwa yaji a bayi gefen gadon kusa da bayi ya zauna don kar ma tana fitowa ta gansa, Hasna da take shirin fitowa ganin Haiydar ya shiga d'akin su tayi murmushi sai ta nufi dining kawai don ta sha ruwan zafinta a can.
Aisha da 'yar wakanta fito d'aure da tawul iya cinya sam bata lura da mutum ba dake ta na goge kanta zagawa yayi ta bayanta ya rungumeta tare da zare d'an k'aramin tawul d'in, cikin razana tayi tana shirin sakin ihu ya toshe mata baki da hannusa a kunne ta ya rad'a mata" nine mijiki Haiydar kuma d'an uwanki", dumm! Taji gabanta ya fad'i juyo da ita yayi duk kunya ya ishe ta, hannu tasa tana kare k'irjinta, ya saki murmushi ya ce"mai yasa kike rufe min abunda yake halal a gareni kuma nake marari ganinsu tare da begen...". Magana kunya ta bata sai ta rufe ido hannuta ya kama ya kawar daga k'irjinta tare da janta zuwa gado cikin muryan kuka ta ce"Ya Haiydar miye haka? Dan Allah ka bari mai kazo yi a nan?". Murmushi yayi ya ce"yau nazo karb'an hakkina da ya dad'e shekara da shekaru ana min rowa kai ta gir-giza masa tare da k'ok'arin turjewa sai da ya kaita kan gado ya kwantar da ita, salon k'auna iri-da-kala yasoma nuna mata wanda ya fi k'arfin in tsaya zayya ne mu ku acin nan. Hasna ko ganin haka da man akwai d'aki wanda da komai a ciki d'akin hajiya ta koma ta dauko kayan bacci, tazo tayi wanka ta kwanta a nan. Haiydar ko sai da yayi wasa da Aisha son ransa ya kuma tabbatar da ya gamsu kafin ya mik'e cike da nishad'i ya fito cikin sand'a ya koma d'akinsa wanka yayi ya kwanta yau yana mai jinsa cikin farin ciki kasa bacci yayi can iya tuna mai ya faru sai ya saki lallausar murmushi tare da buga hannusa a katifa alamar jin dad'i.
Aisha ma wanka ta sakeyi kafin tazo ta kwanta tana mai tunano abunda ya faru haka har bacci ya d'auketa. Da safe bayan sun karya sun dawo falo an gaggaisa yau Aisha sai wani sunne kai takeyi Haiydar ko idonsa akan ta yake suna had'a ido zai kashe mata ido d'aya, Sarkin Fulani ne yayi gyan murya sai da yayi addu'a kafin ya fara da cewa"hukuncin dana yanke shine da zaran Aisha ta kammala jarabawan ta zamu tafi Yola a kaita taga dangin Mahaifiyar ta sanna  gonar Lamid'o inaso zamu mayar dashi kamfanin yin su Madara da yogurts san nan gefe d'aya kuma a mayar dashi gidan gona gefe d'aya kuwa zamu k'awata shi ya dawo gun tutawa zamu zuba k'ananun namun daji don su kawata gun da d'akunan hutawa da gun abinci mai kyau, hakan zai kawo kud'i kuma wasu manya zasuna zuwa gun kasancewar yayi wajen gari kuma ba hayaniya a gun". Ya d'ago ya kallesu ya ce"kunaga hakan yayi ko da wani tsarin da yafi hakan?". Hajiya da Lamid'o suka amsa da yayi nan ya ce"to na nasa an muku komai sabida komawarku Bauchi don gobe Aisha tana da jarabawa". Daga nan kuma suka ci gaba da hiransu. Da yamma kuwa sarkin Fulani har dashi da Lamid'o aka musu rakiya zusa filin jirgi suka dawo Bauchi. Washe gari Aisha ta nufi makaranta nan taba masu Sadeey da Sanah labari ba k'aramin murna suka mata ba da samun Mahaifinta.
Haiydar ko yana komawa gida ya samu Falmi amma sai me fiskanta yaga kamar alamun nadama da murna ta tarbesa don ita damuwarta taji ina yaje sai da ya huta cikin kissa take tambayarsa ko da yabata labari nan fa ta dira tsalle ta mik'e ta ce"ina wannan k'arya ne kawai baki kuka had'a don ku rufa mata asiri"  nan fa rikici ya kaure a tsakanin su daga k'arshe falon ya barmata ya koma d'akinsa. Bayan kwana biyu duk damuwar sa ya ga Aisha gashi yanzu saura mata jarabawa d'aya ta gama, zuwa makarantar yayi yasamu suna jarabawa ya tsaya ya jirata sai da suka fito yasa aka kirata tana zuwa ya ce"ki shiga mota", sam fiskan sa ba alamar dariya hakan yasa ta shiga da sauri ya ja motar ya bar harabar makarantar gudu yakeyi sosai hanyar UNGUWAN SARAKUNA ya nufa, cikin razana Aisha ta ce"lafiya yanaga ba hanyan gida ka nufa ba?". Wani kallon da ya aika mata dashi yasa tayi shiru har suka isa wani k'ofar madai-daicin gida mai kyau horn yayi mai gadi ya bud'e masa yana shiga ya ajiye motarsa ya zago ta gun Aisha fiska a d'aure ya ce"matsawan in kika min gardama to kinsan sauran". Yau kam ya dawo mata Haiydar d'insa na da tuni wani tsoro ya shige ta hannun ta ya kama tare da mannata da jikinsa suka nufi cikin gidan suna shiga ya kulle k'ofar tare da zare makullin yasa a aljihun sa, wani d'aki ya nufa da ita, suna shiga ta ja ta tsaya a k'ofar d'akin cikin dauriya ta ce"wai lafiya yau kuwa mai yasa ka kawo ni nan gidan?". Wani mayen kallo ya bita da shi tare da matsowa kusa da ita ya ce"yau hakkina nake buk'ata a gunki nagaji da jamin rai da kikeyi". Janyota yayi ta fad'a jikinsa tare da rufe k'ofar d'akin tafara k'ok'arin kwace kanta wani tsawa ya daka mata ai ba shiri tayi shiru sai hawaye ke sauka, wayarsa ya ciro ya tura ma Hajiya message kamar haka.

           *_Assalamu'alaikum_*

        _Hajiya barka da rana kar a tura d'auko Aisha naje d'auko ta muna tare yanzu haka da ita, zamuje unguwa karkuga shiru sai mun dawo_.

Yana tura ma Hajiya yana ganin ta bud'e sak'on ya kashe wayarsa ya sa a gen gado, hannunsa yasa ya janye karamin hijab d'in Aisha tare da sanya hannusa a gashin kanta ya fara shafawa Aisha ko sai hawaye takeyi, hannusa ya zura ta cikin riganta ya balle bra d'in ya fara.....

             *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHA MUHAMMAD*
       *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                 *_RASH LUV_��*

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE.... 227-228

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-227~228.*

Na tattara dukkan shanuna da 'yar sanda na muka d'au hanya sai da mukanshiga cikin daji kawai mutanen nan suka b'ullo mana ba k'aramin razana mukayi ba amma duk da haka nayi iya k'ok'arina akan su amma Allah baiyi ina da nasara ba haka suka kwad'a min sanda a kafad'a ganin bazan iya kare kaina ba shine na wurgo ma Safinatu jakata da kud'i a ciki da awarwaron da Hajiya ta ban sannan da hoton mu da ku da nawa ni da ita wanda mukayi a auren mu". Ya nisa tare da gyara zama ya d'an kurb'i ruwan Faron da ke gefensa ya ce"kunji yanda muka rabu da Safinatu". Duk fiskan su d'auke da hawayen tausayi Sarkin Fulani ya share kwala ya ce"muna jinka yanda ku ka k'are da mutanen". Lamid'o ya ci gaba da ce wa"bayan tafiyar Safinatu tana kuka tana waige na haka mutanen nan suka kwada min sanda na suma a gun, sukuma suka kad'a shanuna suka tafi, ana haka sai ga wani Maharbi ya zo ganin halin da nake ciki ya d'aukeni yaje ya ta min magani, da ikon Allah ciwukan dana ji duk sun warke amma me sai na samu tab'in hankali haka Maharbin nan yayi ta jinyana tsawan shekara goma sha bakwai kafin da ikon Allah ya samomin magani shekara guda da rabi yayi yana min jinya da maganin cikin ikon Allah na samu lafiya, daga nan ya tambayeni labari na na basa labarina tun daga kawo ni da akayi Yola har zuwa lokacin. Maharbin nan shi ya tara 'Yan uwansa da mai gari aka karb'a min shanuna ko da suka dawo hannuna sai na saida guda uku a cikin garin yola na dawo kauyen fofure na sai babban fili a jeji wanda filin ba k'arami bane(kunsan filin kauye ba zada sosai). Nan na sake biyan kud'i aka kewaye min da wayoyi nazuba shanuna aciki sannan nasaka su kaji da raguna da akuyoyi da talotalo da agwagi ruwa, bayan dana gama aikin sai na damk'a wa Maharbin nan gonan a hannusa zai na kula dasu don ana saran koyayen zabbi da sayan madaran shanu a gun na masa sallama na sanar da shi zanzo Mahaifata na ga iyayena da Matata da na turota tare da cikin da ke jikinta nan na kamo hanya zuwa Gombe, to kunji labarina". Wannan karon harda Haiydar a 'Yan yin kwalla labarin gwanin ban tausayi. Sarkin Fulani cikin fushi ya ce"yanzu abinda Hajiya k'arama zata min kena  batare da b'ata lokaci ba ya kira police ya ce su zo gidan sa yanzu-yanzu".
Hajiya k'arama da ta lab'e tana jin duk abunda ya faru cikin sauri ta koma d'akin ta tafara shirya kayanta a k'aramin jaka sai ta nufi d'akin Sarkin Fulani ta d'ibi kud'i da dollars cikin jaka, nan ta fara dariyan mugunta tasan wa'yan na  kud'in sun isheta rayuwa a ko ina take ga kuma wanda ta tarasu a account d'inta K'ofar baya tabi tayanda sarki bazai ga fitarta ba cikin hanzari take tafiya dan kar a ganta.
A falo kuwa police sunzo d'akinta aka nufa kai tsaye amma me sai wayam suka gani ba kowa nan suka bazama aiko suna zuwa k'ofar baya suka ga ta k'ofar a bud'e cikin hanzari suka bazama bakin titi suka hango ta tana shirin shiga napep ganin haka wasu suka tsari mashin aka bita wasu a mota
[10:29PM, basuyi nisa ba aka kamata aka sa mata ankwaf aka nufi C.I.D da ita ana kamata aka sanar ma Sarkin Fulani nan ya ce"Lamid'o muje C I D tare suka fita a jikin mota ko da suka je nan ma aka basa duk abunda aka kama a hannuta, ransa ya k'ara b'aci sai da yabata kyawawan mari masu lafiya ya kuma ce" wallahi kin cucen na yarda da ke sakayyar da ki ka min ke nan ki sani ba amfanin zamana da ke na datse igiyar aurena uku da ke kanki". Nan ya ba da umurnin abata wahala sosai tukun a turata kutu.
Haiydar ko Hajiya na mik'ewa ya nufo gun Aishat Hasna na ganin haka ta ja 'yan matan k'afar ta ta bar falon, Aisha cikin hanzari itama ta mik'e har ta fita a falon taku k'alilan yayi ya fisgota sai a k'irjinshi ta fad'o nan wani kamshi mai tattare da sanyi ya daki hancinta Haiydar cikin kwayan idonta ya fara kallo ganin haka ta lumshe ido dul jikinta b'ari yakeyi, hancinsa ya d'aura akan nata ya fara gogawa tare da sanya bakinsa cikin nata nan yaji wani laushi a labb'an ta, tun da yake da Aishat sai yau yasamu wannan damar Aisha ko k'ok'arin ta gudu take amma me hannuta ya manna da garu tare da d'aura hannusa akan nata yasona kiss d'inta kamar wani mayunwaci, duk yanda taso ta kauce ba hali gashi jikin ta na b'ari sosai hawaye ke zuba harshensa yasaka yana lasar hawayen sai da ya lashe tass, Aisha gashi ba halin tayi magana ya had'a bakinsa danata dai da ya jagwa-gwata son ransa ya saketa da gudu tayi hanyan cikin d'akinsu sai hakki takeyi cikin sa'a ba Hasna a d'akin kan gado ta fad'a tana maida numfashi sama-sama tare da lumshe ido cikin zuciyarta ko cewa take" a sai haka kiss d'innan ke da...

               *®NWA*

                    *DEDICATED TO*
             *AISHA MUHAMMAD*
      *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                 *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 225-226

Rash Kardam��  ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-225~226.*

Ba kowa bane ya turo k'ofar illa Muhammad Lamid'o d'a d'aya tilo Namiji kuma magaji ga Sarkin Fulani Gombe cikin razana da firgici Hajiya k'arama ta mik'e don ba k'aramin kid'ima tayi da ganin sa ba nan take taji wani fitsari na shirin zubo mata sai zazzare ido takeyi jikinta sai b'ari ya farayi Sarkin Fulani da kansa ya taka ya je ya rik'o hannu Lamid'o yana hawaye bai san lokacin da ya rungume sa ba farin ciki ba'a cewa komai baran Aishat da ganin fuskan sa ba tam-tama ta gane Mahaifinta ne don yawan kalon sa da takeyi a hoto, Sarkin Fulani ya kamo hannu sa ya zaunar da shi Hajiya ma kukan murna takeyi ikon Allah kenan, sai da suka zauna Sarkin Fulani ya ce"Lamid'o kaine?". Lamid'o ya ce"eh nine Abba". Sarkin Fulani ya furta ikon Allah kenan ya wuci wasa". Ya kalli Hajiyan su Haiydar ya ce"kije d'akina ki had'a masa ruwan wanka tukun ya ci abinci don naga da gajiya a tattare da shi ga alamar yunwa". Haka ko akayi nan take ta kaisa d'akin Babansu ta dawo kitchen da ita da su Aishat suka had'a masa girki mai k'ayatarwa, yana fitowa a wanka ya tarar da sabbin kayan da aka ajiye masa ya sanya ya gyara jikinsa, falo ya fito ya tarar da su, sai a lokacin idonsa ya kai kan Aishat da ta k'ura masa ido shima kallonta ya farayi cikin zuciyar sa ya ce" wannan tamkar Safinatun sa, ayya ko dai ita ce yar cikin Safinatu da taho da shi?". Hannusa yaji an rike ko da ya duba Sarkin Fulani ne ya kama hannusa duka suka nufi dining, Hajiya da kanta ta sanya ma kowa abinci ta zauna Sarkin Fulani yana mak'ale da Lamid'on sa sai Hajiya da ke kusa dashi sai Aishat a kusa da Hajiya yayin da Haiydar ke kusada Lamid'o sai Hasna a kusa dashi. Haiydar yana kallon Aishat yana aika mata da wasu sak'on ninsa, gun shiru kowa yana fama da abinci fiskan kowanne su yana d'auke da murmushi don suna cikin farin ciki bana wasa ba.
Haiydar ne ya mik'ar da k'afan sa ta k'asan dining table d'in yanda zai na tab'a k'afar Aishat babban yatsan k'afarsa ya sanya a tafin k'afar Aishat ya fara mata tafiyan tsutsa a take taji wani yarrr! saurin d'ago fiskan ta tayi karaf su ka had'a ido wani lalalusar murmushi ya sakar mata ya kashe mata ido d'aya. Sai da ta d'an saci kalon su Hajiya taga kowa na ta kai da abincin sa ta murgud'a masa baki, Haiydar yayi murmushi ya sake sosa mata k'afa harda wuce wansa zuwa sawun k'afar ta da sauri ta kau da k'afar asai Hajiya tana lura dasu ta share ne kuma taji dad'in hakan suna kammala cin abinci suka koma babban falo suka zazzauna. Sarkin Fulani ya kalli Hajiya ya ce"wai ina Hajiya k'arama ne banganta ba har a gurin cin abinci kuma yanzu ma bata fito ba ko lafiya?". Hajiya ta ce"ina ga lafiya zata fito". Sarkin Fulani ya kalli Lamid'o ya ce" zaka iya gane wannan fuska kuma da wa ta ke maka kama?". Lamid'o ya kalli Aisha sosai ya ce"tun shogowata fuskanta ke min kama da fiskan Matata Safinatu". Sarkin Fulani ya murmusa ya ce"tabbas wannan d'iyarka ce da Safinatu". nan suka kwashe labarin komai suka fad'a masa sosai Lamid'o yayi kuka ya tausaya wa Matarsa da 'Yar sa tare da mik'o hannu ma Aishat tazo yana kuka ya rungumi d'iyarsa take Aisha taji sanyi dad'i na ratsa ta wai yau ita ce take tare da Mahaifin ta daman ita ba 'Yar shege bane da ake kiranta, zanso Falmi taga gatana taga Mahaifina asai mu 'Yan uwa ne da Haiydar nan tasaki sassanyan Ajiyar zuciya, Sarkin Fulani ya ce"zan so kabamu labarin bayan barin ka Gombe yanda al'amura suka kasance". Lami'o ya nisa tare da gyara zama ya ce"bayan da muka shiga mota munyi nisa sai da muk'a k'usa shiga Alkaleri Idi driver ya tsaya", ya ce" Lamid'o bazanso na kashe ka da hannuna ba don an bani kwangilan kasheka ne Hajiya k'arama amma sabida kirkin Hajiya babba bazan ci *AMANAN* ta ba ta rik'e mu da gaskiya" Lamid'o ya ci gaba da cebwa"kafin nayi wani magana kawai ya shafamin wani abu a hanci na tun daga lokacin ban san inda kaina yake ba sai a cikin wasu kauyukan Yola na samu kai na tare da wani mutumi wanda aka had'a ni dashi dan ya baro bauchi dani gudun kar Hajiya k'arama ta ganni, mutumin nan sai da ya tabbatar da na dawo cikin hayyacina shima ya zame ya barni, a tasha kauyen ribad'o na zauna nan yunwa ya fara damuna daga nan na fara aikin k'arfi ina kula da kaina kuma na samu wani Bafulatani mukayi dashi zanna tayasa kiyo yana biya na haka muka fara randa ba kiwo inje niman kud'ina da haka har na tara kud'ad'e na sai na sayi saniya ta mace nan muka fara kiwo cikin ikon Allah ya sanya ma saniyar nan albarka tayi ta haihuwa kuma inayi niman kud'ina na sai na sai wasu da haka Allah ya azurtani da garken shanu na kuma yi suna a cikin kauyukan da ke yanki don ba mai shanuna a haka har Allah yayi na auri Matana Safinatu muna zaman lafiyan mu wasu daga cikun yan kauyen suka fara adawa da dukiyata hakan yasa suke min barazanan kisa, a haka wasu daga cikin ranar laraba da bazan manta ba suka fara bina suna neman kashe ni cikin hanzari na taho gida na umurci matata da tazo mu gudu.

                   *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHA MUHAMMAD*
     *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

           *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 223-224

[10:16PM, 7/18/2016] Kardawiya��: ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-223~224.*

Abban mu ya dawo daga Saudi na zo gida masa sannu da dawowa da wasu dangi bayan ya huta ya ciro tsara ba ya bai ma 'Yan uwa da abokan arziki ya raba musu su Hajiyar mu ko wanna awarwaron ya sayo musu wanda kud'insa bana wasa bane anan yaraba musu ana bama Hajiyar mu nata Lamid'o yasa kuka shidai sai dai abasa wannan awarwaron ne na zinari ya masa kyau ba irin rarrashin da ba'a masa ba yaki nan Hajiya ta d'auka ta bashi kyauta. Haka rayuwa yaci gaba da tafiya Sarkin Fulani na gwada mana gata kasancewar mukad'ai ya haifa 'Ya'ya biyu bayan wasu shekaru Lamid'o ya girma a kwai ranar da bazan manta ba ranar da muka masa ganin k'arshe ranarda kishiyar Hajiyar mu ta aiki driver (mai tuk'a mota) garinsu Lamid'o naji zasu tafi ya ce shi sai ya je Alkaleri kasancewar ita 'Yar garin ne nan Lamid'o ya d'au yar jakarsa yasa kaya kala 2 kasancewarsa mai tsafta ne kuma sai washe gari zasu dawo, kuma duk inda ya ke baya rabuwa da hoton iyayen mu wanda mukayi tare don shima ya shaku da baban mu sosai, suka tafi da driver(mai tuk'a mota) can kusan yamma sai ga wasu mutane da kukan su wai Lamid'o sunyi hatsari harshi kamma ya kone k'urmus sai tokan sa akà gani to kinji labarin rabuwan mu da Lamid'o wanda sanadin rasuwarsa yasa hawan jini ya kama Hajiyar mu itama bata dad'e ba Allah ya mata rasuwa. Aishat wacce take hawaye ta sauke ajiyar zuciya Hajiya ko ta ce"Hasnat je d'aki ki d'auko waya na kira Abba na in sanar masa don na san zaifi kowa farin cikin ganin 'Yar Lamid'on sa" Hasna ta d'auko waya Hajiya ta kira Sarkin Fulani ta koro masa bayani cike da murna wanda sai da yayi kwalla harda sujudu shukur yayi nan take yasa aka bama Aishat suka gai sa. Hajiya ta karb'i wayar Sarkin Fulani ya ce" Gobe ku biyo jirgi da wuri kuzo naga jikata don bana jin dad'i ne ni da yau nazo". Hajiya ta saida masa suna zuwa, take Hajiya ta sanar ma Babansu Haiydar shima yayi murna ya ce"in Allah ya yarda cikin satin nan shima zai dawo". Haiydar shi ya je ya musu komai harda shi a tafiyan, ranan Aishat kasa bacci tayi dan farin ciki da murna harda yi nafiloli ta gode ma Allah tare da addu'a Allah ya jikan mamanta.
Washe gari da safe suka shirya sai gombe, tun daga Airport suka ga jerin dogaraye suna jiransu ga wata rantsaysiyar lemozine k'atuwa da akaje d'aukarsu a cikin ta. Aishat kam in banda kalo ta dawo kamar 'Yar k'auye sai kale-kale takeyi har suka zo wani k'aton katafaren gida wanda in aka bar Aishat sai ta ce wannan shine white house da ake fad'a na Abuja. Suna sauka nan dogaraye suka fara gaishesu har suka shiga falo, Sarkin Fulani dake Falon idonsa nakan Aishat tabbas wanan jinin sa ne take idonsa ya kawo kwalla duk da yana daurewa hannu yamata alamar tazo ya rike hannuta tare da dafa kanta yana hawaye ji yake kamar Lamid'o ya rike sai da suka zauna kowa ka gani fuskan sa d'auke da fara'a da farin ciki in ka d'auke Hajiya k'arama da ko dariya batayi nan Sarkin Fulani ya sake niman jin k'arin bayani Hajiya ta basa labari Aishat ma ta d'aura da iya sanin ta nan ya rungumi jikarsa yana kuka itama tanayi. Ana haka sukaji an turo k'ofa tare da sallama dukkansu suka d'ago kai tare da kallon k'ofar ko ni ma Rash dana kalli k'ofar wani farin bafulatani dogo mai karan hacci kyakyawane wanda za'a  kwatanta a gurin kyau  amma ya d'an girma amma kuma girman ta had'u da wahala fuskan sa ta cika da k'asun ba da alamar dai yana cikin wahala cikin sauri Hajiya ta mik'e a razane Sarkin Fulani da k'afarsa ke ciwo bai san lokacin da ya mik'e ba murtsuk'e idonsa yasoma yi don yaga ko mafarki ne yakeyi amma ina ba mafarki bane wannan zahiri ne tabbas wanna ko ba makawa babu tam-tama.........

              *®NWA*

                   *DEDICATED TO*
           *AISHAT MUHAMMAD*
     *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 221-222

[6:58PM, 7/18/2016] Kardawiya��: ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-221~222.*

Hajiya kuma ganin Aishat na kuka ga hoto a hannuta yasa ta k'arso da sauri don ganin hoto  hannuta wannan Awarwaron gwal d'in tafara karo dashi tabbas ko a mafarki bazata manta da wannan a warwaron ba, tana duba ga hoto hannu Aishat damm! Gaban k'irjinta ya bada sauti take numfashinta yasoma d'aukewa hannun take nuna hoton dashi tana fad'in La....mi.....d bata k'arasa ba ta yanki jiki ta fad'i kasa sumamiya dai-dai da shigowar Hasna d'akin ta saki razananne k'ara tayi kanta. Hasna ta fara jijiga Hajiya amma ina ta sume Aishat ma da sauri ta sauko tazo ta k'ank'ame Hajiya tana kuka, Haiydar da ke falo jin k'aran Hasnat yasa ya hauro sama da gudu ya nazuwa yaga Hajiya a k'asa duk ya rud'e sai da ya jijigata da sauri ya mik'e yayi cikin bayin d'akin ya d'ibo ruwa yana zuwa ya watsa mata, ya k'ara watsa mata take ta saki sassanyan ajiyar zuciya gefen idonta hawaye ne ke zuba. Ta ja jikinta ta jin gina da jikin gado Haiydar da su Aishat sai sannu suke mata Haiydar ne ya bata ruwa mai sanyi tasha ta sauk'e ajiyar zuciya ta ce"Aishat ina son ki fad'amin gaskiya dan Allah ina kika samu wannan awarwaron da hoton d'an uwana k'anina Lamid'o wanda shekara da shekaru ya rasu?". Haiydar da Hasna sun zuba ma Hajiya da Aishat ido suna masu mamaki da rud'u a cikin al'amarin Aishat jiki a sanyaye ta ce"Hajiya wannan hoton Mama na ne da Baba na sai d'ayan kuma Mama na ta ce Baba na ya ce mata Kakan ni na ne suke d'ayan". Cikin hanzari Hajiya ta mik'a hannu zuwa inda hoton ya ke ta d'auko tabbas ko makawa babu Lamid'o ne d'aya hoton kuma ita ce a ciki tana budurwa sai Lamid'o yana k'arami ya dai girma ba sosai ba sai Iyayensu dukkansu sanye suke da alkyabba wanda taji ado da k'ayatarwa cikin rashin fahimta ta ce"Aishat ban fahimce ki ba kina so ki ce min Lamid'o shine Mahaifin kuma kenan bai mutuba?". A fili ta ce"Aliyu to kodai in mutum ya mutu yana dawowa ne?". Aliyu ya kalli Hajiya tabbas bata hankalinta don a rud'e take. Aliyu cikin sassanyar murya ya ce"ai duk wanda ya mutu baya dawowa sai dai in daman bai mutum ba". A hankali ta sauk'e ajiyar zuciya ta ce"Aishat ina so ki bani labarin ki iya yanda Mahaifiyarki ta sanar dake". Ba tare da b'ata lokaci ba Aishat ta basu labari ta harzuwan Mamanta garin Bauchi, idon Hajiya cike da kwalla ta ce"tabbas ke 'Yar Lamid'o ne ga saida nan wannan awarwaron da kuma cewa Mahaifiyarki ta je Gombe ta nimi 'Yan uwansa da hoton nan ya isa sai da bare wasu sassan jikinki duk irin na Mahaifinki ne shiyasa ko da yaushe nake jinki a jikina tamkar 'Yar dana Haifa, a sai da 'Yata nake tare nan Hajiya ta fashe da kuka wanda itama Aishat kukan farin ciki takeyi Hajiya ce ta mata alamar tazo kusa da ita tana zuwa suka rungumi juna suna kuka zuwa wani lokaci suka tsagaita Hajiya ta kali Aishat ta ce"ke ba 'Yar shege bane da ake fad'a miki haka ke 'Yar gatace kuma 'Yar dangi kafin muje gimbe ya kamata ki san ko ke wacece kuma waye shi Muhammad Lamid'o". Haiydar ko yafi kowa farin ciki da bayyanan iyayen Aishat asai 'Yar uwansa ce kanwan sa tabbas sai yanzu yake jin kunyan zagin shegen da yamata tabbas yasan dole yanzu Hajiya ta k'ara hura masa wuta a kan Aishat don yasan yanda Hajiya take tsananin son d'an uwata Lamid'o bare ace yarsa dole ya k'ara kwantar da kai. Hajiya ta ce"Kamar yanda ki ka gani a hoton nan Mahaifin mu Sarkin Fulani ya kasance shahararen mai kud'i a cikin garin Gombe tun asalin Kakan mu shine sarkin Gombe kinga kenan wannan Sarautan tana k'ofar gidan mu ne lokacin da Kakan mu ya rasu sai ya zamana Mahaifin mu Sarkin Fulani bazaiyu a bashi Sarauta ba, sai aka d'auka aka bama Wazirinsa kinga daganan Sarauta ta bar gidan mu kenan ko da Mahaifin mu ya girma ba halin k'arban Sarauta sai aka bashi Sarkin Fulanin Gombe wanda alokacin matan sa biyu ne sai nice 'Yarsa ta farko kuma bai kara haihuwa daga kaina ba sai bayan shekara biyar aka Haifi Muhammad wanda ake kira da Lamid'o kasancewan shine d'a namiji d'aya ma Sarkin Fulani ya d'auki son duniya ya d'aura masa wanda hakan ya ke kona ran Kishiyar Hajiyan mu tun yana k'arami take kai masa hari da niyar kasheshi Allah bai bata sa'a ba har yasoma tashi, ana haka akayi aurena da Baban su Aliyu muna zama a cikin garin Gombe lokacin a gun yake aiki kafin mu dawo Bauchi da zama kasancewar shi d'an k'aramar hukuman Katagun ne da ke Bauchi, bazan manta da ranar da Abban mu ya dawo daga saudi ba rannan nazo gida masa murna da dangi duk mun had'u a gida".

              *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
           *AISHAT MUHAMMAD*
       *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                  *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 217-220

[7/17/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-217~218.*

Dr ya ce"ya kamata a canza mata kayan jikinta sun b'aci". Haiydar ya amsa da "to". Ya kalisu Hajiya ya ce"barinje gida na d'auko mata wasu kayan". Hajiya ta kalli agogo wayan ta karfe biyu da rabi ta ce"to kaje Allah ya kareka". Ya amsa da "Ameen". Ya fita gudu yaringa shararawa har ya iso gida horn ya ringa yi Falmi cikin bacci taji horn d'in kafin da sauri ta leka taga Haiydar ne ke shigowa cikin sauri ta shafa turaren nan ta kuma shiga bayi ta kuskure bakinta da ruwan maganin ta nufi k'ofar falo. Cikin rashin sa'a kafin ta riskeshi har ya shiga d'akin Aishat ya d'ibi mata kaya kala biyu marasa nauyi ya fito kenan sukayi two eyes(ido biyu) da Falmi hannuta a kan k'ugunta cikin isa da gadara ta ce"kai daga ina kake a cikin wannan dare?". Haiydar duk sai ya ji komai ya kwance masa ya tsinci kansa da ba zai iya yi mata musu ko gardama bare yaki bin umurnin ta, sai da ya yayi jim kafin ya ce"daga Asibiti nake". Cikin hanzari ta ce"waye a Asibiti?" Haiydar ya kalleta ya ce"Aishat ce". Dammmm! k'irjin falmi ya bada sauti bata san lokacin da ta sanya hannu a k'irjinta ta dafe ba ta ce"mai ka ce?". Haiydar yasake mai-maita abunda ya fad'a nan take zuciyar Falmi yafara azal-zala ta ciji bakinta hannuta ta had'a ta buga tare da fara safa-da-marwa tana zagaya guri idonta ya kad'a yayi jajazur ta d'ago ta ce"yanzu a wani hali take?". Haiydar ya ce" jikin da sauki sosai". Ran Falmi in yayi dubu ya b'aci ta kalli Haiydar ta ce"maza kaje ka ajiye kayan nan ka wuce d'akinka". Da sauri ya amsa mata da "to". Amma wani bangare na zuciyarshi bataji dad'in haka ba yana so yaje amma ba halin yi mata musu. Haka Falmi ta tasashi gaba sai da yaje d'akinsa ya kwanta ta nufi d'akinta.
Acan Asibiti kuwa shiru-shiru hajiya suka ga bai dawo ba hankalinsu ya tashi sosai, da sassafe hasnat tazo musu da kayan tea da ruwan zafi har wajan bakwai Haiydar bai zoba, hakan yasa Abban da kansa ya ce"Hasna muje gidan Aliyu muga ko lafiya". Hasnat da sauri ta amsa suka nufi gidan a motan Abba suna zuwa mai gadi ya wan gale musu gate(gareji) suka shiga, Mai gadi yana ganin Abba ne ya gaidasu cikin mutunci da girmamawa, Hasnat ta bud'e falo taga bakowa ganin haka tayi magana ma Abba ya shigo kasancewar tsakanin Main falonsu da side d'in kowaccen su da taraza Abba na zama Hasna ta nufi k'ofar d'akin Haiydar ta kwan-kwasa kamar a kunne Falmi sai gata ta fito tana karairaya ganin Hasna ta ja tsaki ta ce"ke lafiya zaki zo kina tashin mutane da safen nan?". Hasna ta kalleta a wulakance ta ce" gun d'an uwana nazo ni da Mahaifinsa ke son ganinsa". Falmi tayi dariya kice min ke da tsoho kuka zo". Ran Hasna ya baci ta juya ta koma falo Falmi ta biyo bayanta ta ce"aa Tsoho ne haka a gidan mu". Abba yana jin ana bada labarin rashin kunyan Falmi bai tab'a gani ba sai yau ransa ya b'aci sai karairaya take tana fad'an banzan magana Haana cikin fushi ta kaiwa bakin duka wanda saida jini ya zuba, Abba kasa cewa komai yayi ila fitowa daga gidan Hasna ta kalleta ta ce" ki iya da bakin ki don bazaki tab'amin iyaye na kyaleki ba banza shasha". Fuuuu Hasna ta bi bayan Abba sai a lokacin suka ga motan Haiydar kenan yana gida. Ran Abba ya gama b'aci amma ya daure ya boye ya ce"Hasna muje gida ki d'auko ma Aishat wasu kaya acikin kayanki". Haka ko akayi suka dawo Asibiti da kayan Hasnat. Satin Aishat d'aya a Asibiti aka sallameta jiki yayi sauki, wanda duk kwanakin nan Haiydar bai tab'a tako k'afarsa ba abun yayi ma umma ciwo amma taki nunawa a b'an garen Aishat ma haka.
Falmi ko ta samu yanda takeso don juya Haiydar takeyi son ranta shiko duk da wani b'an gare na zuciyarsa baya kin dad'in abunda yakeyi amma ba yanda ya iya.

          *®NWA*.

                *DEDICATED TO*
          *AISHAT MUHAMMAD*
     *(MAMAN ABDIL SHAKUR)*

                *RASH KARDAM��*
[7/17/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-219~220.*

Hajiya tasa ka Hasna taje ta d'iba ma Aishat duk wasu abunda zata buk'ata ta koma gidan su da zama kulum tana cikin sanyaya mata zuciya akan halin Haiydar.
Falmi ko ta samu yanda takeso don juya Haiydar takeyi son ranta shiko duk da wani b'an gare na zuciyarsa baya jin dad'in abunda yakeyi amma ba yanda ya iya sai dai abun na damunsa a cikin zuciyarsa kulum yana cikin tagumi da damuwa.********************
   8months latter.
Cikin wa'yan nan watannin abubuwa da dama sun faru harda fara jaraban Aishat sunyi WAEC yanzu suna NECO har sun kusa gamawa, yanzu driver Hajiya ta samar mata shi ya ke kai ta ko ina, Hajiya kuma ta dage da addu'a akan halin da Haiydar ke ciki tanayi kullum bata daina ba.
Rayuwan Falmi da Haiydar ko abin tausayi don tana gasa masa aya a hannu bana wasa ba duk ya rame yayi baki kamar ba ASP A.K BABA ba. Kuma duk da tsareshi da Falmi keyi bata bashi hakkinsa wataran sai ya mata kuka kafin tasa ya ajiye mata kud'i tukun ta kulashi, a hakama sai ya sha masifa kafin ya samu.
Tabbas Allah baya bacci kuma shine maji rokon bawansa don shi ya ce mu rokesa zai amsa mana sai dai ya jinkirta don ya ga imanin bawansa. Haka abun ya faru a gun Hajiya don yau Haiydar yana office yaji kaman an tsikaresa take ya tuna abunda ya faru da irin rashin zuwa gun iyayensa har kuka sai da yayi, cikin hanzari ya mik'e ya nufi gida wanka yayi yasaka kaya mai kyau ya fesa turare yayi kyau amma ya rame yayi duhu amma kyansa nanan hancinsa ne yakara fitowa. Ya fito falo sai zuba k'amshi yakeyi dai-dai lokacin Falmi ta fito ganin wanka da yayi ranta ya b'aci da sauri ta nufosa sam yau ta manta bata shafa turare bare ta kuskure bakinta da magani ta ce"kai Haiydar ina zakaje harda yin wanka haka? Ko kamanta kana k'ark'ashin izini nane?".  Bai tanka mata ba don zuciyarshi na azal-zala ganin zai fita tazo tasha gaban sa daman yana cike da ita yanda da safe tayi ta masa tsawa kamar shi d'anta ne, kwalan rigan sa ta sha cikin hanzari ya bata kyawawan mari ya fara ball(kwallo) da ita saida ya jibgeta son ransa ya fita,  motarsa ya shiga sai gidan Hajiya masu gadi na ganinsa sai da sukayi mamaki da sauri ya ajiye motarsa ya nufi cikin gidan da sallamansa ya shiga, Aishat ya fara hangota tana jikin Hajiya Hasnat ma ta hango shi kasa d'auke idonsa yayi akan Aishat Hajiya na ganin sa tayi hamdalah amma ta d'aure fuska dole ta gwada masa kurensa duk da ba da sonsa bane. Hajita ta ce"Hasna Aisha maza tashi ku shiga d'aki da sauri suka mik'e Aishat duk da taji dad'in ganinsa amma zuciyarta na suya da abunda ya mata da sauri tayi d'akinsu da gudu ta fad'a kan gado ta fara kuka mik'ewa tayi ta d'au hoton Abban ta da Ummanta da na iyayen Abban ta tare da awarwaron zinari mai tsada da kyalli nan tasa a gaba tana kalon su tana kuka. Hajiya ta ce"lafiya dai ko? Amma b'atan kai kayi yau ko?" Ya russuna ya gaida ta ta amsa cikin sakin fuska san nan ta ce"yauwa da man kai nake jira tunda yau Allah ya kawo ka inaso ka ba ma 'Yata takardan sakinta don bazata koma gidan ka ba wannan shine hukunci dana yanke kuma umurni nake baka ba wai shawara ba". Haiydar ya durk'usa akan k'afarsa ya soma kuka yana bata hakuri. Hajiya ganin ita tsaya kallonsa zai sa ta kayara ta mik'e ta bashi guri d'akinta tashiga taga Hasna ita kad'ai ta ce" Hasna ina Aishat d'in?" Hasna ta ce" tana d'akin mu ina ga". Hajiya ta mik'e ta nufi d'akin su sam Aishat tayi nisa cikin tunanin iyayenta bata san da shigowar Hajiya ba. Hajiya kuma ganin Aishat na kuka ga hoto a hannuta yasa ta k'arso da sauri don ganin hoto  hannuta wannan Awarwaron gwal d'in tafara karo dashi tabbas ko a mafarki bazata manta da wannan a warwaron ba, tana duba ga hoto hannu Aishat damm! Gaban k'irjinta ya bada sauti take numfashinta yasoma d'aukewa hannun take nuna hoton dashi tana fad'in La....mi.....d bata k'arasa ba ta yanki jiki ta fad'i kasa sumamiya dai-dai da shigowar Hasna d'akin ta saki razananne k'ara tayi kanta.

Ni Rash  danake gefe na ce" to mai ke shirin faruwa kar dai ace......... Bari dai zamuji koma miye.

               *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHAT MUHAMMAD*
       *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*


                *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 214-216

[8:05PM, 7/16/2016 ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-214~216.*

Dai-dai lokacin sauran police d'in suka iso, bai bi ta kansu ba da gudu yayi mota da ita ya sanya ta a mota ya juyo ya ce"ku tabbatar da kunbi mutanenan kuma kun kamosu zan turo wasu motocin su biku". Bai jira amsansu ba ya juya ya shiga mota ya figeta da gudu ya nufi cikin gari. Gudu yakeyi sam ba nutsuwa a jikinsa wani wawan duka ya kaima sitiyari motar tare da furzar da wani isaka mai zafi zuciyarsa na masa rad'ad'i wai ace abunda yagama tanadi wani ya rigasa wasu zafafan hawayene suka zubo masa wata b'an gare na zuciyarsa ya ce"haba Haiydar duk da abin da ciwo kardai kace zaka guje ma Aishat don son da ka ke mata na gaskiya ne bawai jikinta kake so ba. A fili ya furta" Aishat a kowani hali ki ke ina k'aunarki ke ce SIRRI NA bazan gujeki ba". Wasu hawaye ne suka sake zubo masa, wayarsa ce tayi k'ara sunan Hajiya ya gano ya d'aga cikin muryan kuka ya ce"Hajiya an sameta amma sun mata fyad'e gata ko motsi batayi". Hannu a ka Hajiya ta d'aura ta saki salati ta ce"yanzu kuna ina ne Aliyu?".  Ya ce"gani a hanya da ita zan wuce T.H". Hajiya ta ce"okay gamu zuwa da Abban ka yanzu shima ya dawo". Kashe wayar yayi ya k'ara gudu wanda kiris ya rage motar ta kwace a hannusa Allah ne ya kare. Bai dad'e ba ya isa Asibiti take a ka shiga da ita Emergency Haiydar ya gagara tsaye ya gagara zaune sai safa-da-marwa ya keyi a k'ofar idonsa na zubar da hawaye, Hajiya ne da Abba suka iso kalonsu kawai yayi ya fashe da kuka mai cin rai, Hajiya ma hawaye tafara don abun ya mata ciwo bana wasa ba.
Falmi ko gidansu ta nufa ita da Mum d'inta suka tafi gun boka ita duk a zatonta an gama da Indo dan haka ta ce"boka kaban maginda sai abunda na fad'a ma Haiydar zai yi ba kuma zai ki bin umarni na ba". Bokan ya bushe da wata mahaukaciyar dariya ya ce"anyi angama yarinya kinzo inda za'a share miki kukan ki hahahah". Kwarya ya d'aga sama saiga wasu magun-guna sun zuba a ciki nan ya mik'a mata ya ce"ga wannan turaren ki tabbatar kulum kinshafa a jikinki, sannan wannan maganin ki kuskure bakinki da shi kulum". Falmi cikin zud'i ta ce"anyi an gama boka". Bokan ya kara wata dariya kafin ya ce"maganin mu da doka kisani duk randa kika tsallake d'aya aciki asiri zai karye kuma zai miki wulakanci mummuna". Ta ce"zan kiyaye boka". Kud'i ta zuba masa suka tafi.
A can asibiti kuwa Dr ya bata taimakon gaggawa saida numfashinta ya dai-daita kafin suka duba kasanta asai ba fyad'e a ka mata ba kukkurjewa tayi acinya wanda ya janyo mata zuban jini. To ni Rash abun ya d'auremin kai bare masu karatu, amma bari mu wai-wayi baya, in baku manta ba na ce muku"ciwon da Aishat taji ya haddasa mata zuban jini sosai wanda haryasa idonta yin wani iri". Bayan da 'Yan iskan nan suka cigaba da tafiya da ita jininta ya zuba ga razana da tayi hakan ya sanya ta yanki jiki ta fad'i tayi dogon suma idanunta sun kafe, 'Yan iskan nan da suka ga haka sun d'auka mutuwa tayi, shiyasa Ogansu ya ce"kawai su yarda ita anan tunda ta mutu ba amfanin su fita da gawa karma a kamasu". Tundaga bakin hanyar da zai shigarda mutum dajin da aka sameta suke janta a kasa wanda yasa skirt d'inta kwayewa jikinta ya jijiciwo kunji dalilin zuban jinin bari mu koma labari. Ko da Dr ya gama dubata ya gito cikin hanzari Haiydar da Hajiya sukayi gunya a tare suka jefo masa tambaya "Dr ya jikinta?" Dr ya ce"da sauki Alhamdulilah kuma ba fyad'e aka mata ba kurjewa tayi, ga jini ya zuba da yawa  don haka muna buk'atar jini cikin sauri Haiydar ya ce" Dr muje a d'ibi nawa a samata". Cikin ikon Allah jininsu yayi dai-dai aka samata Dr ya ce"ya kamata a canza mata kayan jikinta sun b'aci". Haiydar ya amsa da "to". Ya kalisu Hajiya ya ce"barinje gida na d'auko mata wasu kayan". Hajiya ta kalli agogo wayanta karfe biyu da rabi ta ce"to kaje Allah ya kareka". Ya amsa da "Ameen". Ya fita gudu yaringa shararawa har ya iso gida horn ya ringa yi Falmi cikin bacci taji horn d'in kafin da sauri ta leka taga Haiydar ne ke shigowa cikin sauri ta shafa turaren nan ta kuma shiga bayi ta kuskure bakinta da ruwan maganin ta nufi k'ofar falo.

            *®NWA*

                 *DEDICATED TO*
         *AISHAT MUHAMMAD*
    *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

   
               *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 210-213

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-210~213.*

Fad'uwa Haiydar yayi a kan gwiwarsa kamar mai (nil down) yana k'araji yana ihu ga hijab d'in Aishat a hannusa ya na kuka wi-wi kamar yaro. Da gudu ya tashi yayi gabar yana kiran Aishat! Da gudu ya dawo yayi yamma yana kiran Aishat!! Ya sake dawowa yayi Arewa yana kiran Aishat!!! Yazo ya sake yin kudu yana kiran sunanta, ya dawo kaman zarare. Ya dad'e a haka ya kasa tab'uka komai sai kuka tamkar mace kamar ba jarumin d'an sanda ba mai hazak'a da kwazo wayarsa ne tayi k'ara yana kuka ya ciro daga aljihunsa ya ga sunan Hajiya kafin ya d'auka harta tsinke.
B'an garen Hajiya ko ta ce"yau lafiya banga Aliyu ya d'au wayata ba?".  Kamar ta ajiye wayan sai wani zuciya ya ce"kawai ki sake kira kiji lafiyarsa dana d'iyarki". Cikin hanzari ta danna kira. Haiydar jin waya na ringing ga jikinsa sai b'ari yakeyi (daman wannan yanayinsa ne in ransa ya b'aci jikinsa b'ari zainayi). Da kyar ya iya danna gun amsa kira yasa a kunnensa kuka yakeyi yana kiran Aishat! Ciki razana Hajiya ta ce"Aliyu lafiya mai yasamu Aishat?". Bai iya amsa mata tambaya ba sai ce mata" Hanyan gida b'ata Aishat". Sam kwakwalwarsa ta kasa tuno masa ma ya zai had'a kalman a dai-dai ya fad'a Hajiya cikin kid'ima tun da taji yananyi Haiydar tasan abun ba k'arami bane, ta d'auko hijab d'inta ko Abban su Haiydar dake hanyan dawowa yau bata sanar masa ba ta fito a gi-gice, bata tsaya kiran driver ba(mai tuk'a mota) kasancewar daman ta iya mota da sauri ta figi mota tun daga nesa take horn ma mai gadi, shi kansa mai gadi sai da ya rud'e da horn d'in da takeyi ai ya na wangale gate(gareji) da mugun gudu ta fita. Gudu take shararawa cikin min tunan da baifi hud'u ba ta soma hango Haiydar ga kuma motar Aishat! Gudu ta k'ara tana isowa ta gansa a durk'ushe a kan gwiwansa zuwa tayi da sauri ta rugumesa tana jijiga sa ta ce"Aliyu lafiya? Ina Aishat d'in?".  Jinsa a jikin Hajiya ya saki sassayan ajiyar zuciya sai a lokacin nutsuwa ta zomasa, cikin kuka ya sanar da Hajiya abinda ya tarar Hajiya ta ce"innalilahi wa inna ilaihi raji'u ai ba zama zakayi kana kuka ba, kaman ba jarumin police ba?" Abunda ya da ce zamuyi yanzu tashi kabi sawun motar sannan ka kira duk wata ma'aikatar police da ke kusa a sane dasu don a baza matakan tsaro. Haiydar ya shiga motarsa zuciyansa na suya gun aikinsu ya kira yasanar musu ya ce"susanar da sauran ma'aikatar hukumar 'Yan Sanda a bazama wasu su biyo sa, hayar da mota tayi yafara bi har ya fitar dashi bakim ti-ti, daga nan kuma hanya ta kasu kashi uku ya tsaya yana tunani sai ga wasu motocin police('Yan sanda) sun iso mota uku nan suka kasu kashi uku d'aya yabi Haiydar biyu suka bi sauran hanyoyin. Abu wasa-wasa suna neman Aishat ba labarinta  gashi har anyi sallah isha'i.
Aishat tare da 'Yan iska tafiya sukeyi sai shiga cikin daji sukeyi yayinda jinin jikinta sai zuba yakeyi kasancewar ta mai yawan cin abinci mai kyau tanada wadattace jini amma sanadin zuban da yayi da yawa ya haddasa mata jin jiri, idanunta suna wani iri, hakan baisa Ogan 'Yan iskan nan yayi niyan saurara mata ba sai aika mata da mayen kalo yakeyi.
Su Haiydar ko sunyi nima harsun gaji amma shi baijin gajiya a tare da shi zuciyarsa suya yake masa yama rasa wani irin kalan hukunci zai yanke ma wanda ya d'au Aishat d'insa tabbas ba zai iya saurara masa ba baran yanda yanzu yake jin tsananin k'aunar Aishat na yawo a jinin jikinsa da jijiyoyinsa tafiya suke ga dare yayi ko da ya kali agogon da ke hannusa 11:49 wani kwana ya gani wanda ya lula cikin deji kuma hanyar k'aramace mota bazata sake acikin hanyan ba wasu suna cewa kar abi hanyan halane ko sunbi ta gun gashi yayi daji ko  da Haiydar batunsu ransa da ya b'aci ya finciki motar ya shiga cikin dajin, sauran suna ganin ya shiga suka bisa a baya sai yayi tafiya sosai sai yaga wani abu a gefe kamar mutum ne ko tudu, da sauri ya tsaya ya fito da wani touch light d'insu mai haske yana haskawa ya hango Aishat kwance bata motsi da gudu yayi gunta yana haskawa yaga jini na fitowa daga k'asan skirt d'in makarantarta wani razazane k'ara ya saki ya soma jijigata ganin bata motsaba, dai-dai lokacin sauran police d'in suka iso, bai bi ta kansu ba da gudu yayi mota da ita ya sanya ta a mota ya juyo ya ce"ku tabbatar da kunbi mutanenan kuma kun kamosu zan turo wasu motocin su biku". Bai jira amsansu ba ya juya ya shiga mota ya figeta da gudu ya nufi cikin gari.

               *®NWA*

                *DEDICATED TO*
         *AISHAT MUHAMMAD*
     *(MAMA ABDUL SHAKUR)*

              *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE.. 207-209

[7/16/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-207~209.*

Ogan gani tana da taurin kai kuma zata b'ata musu lokaci yazo dai-dai ita cikin muryan 'Yan iska ya ce"tun da ki kayi taurin kaikuma ki ka b'ata mana lokaci kafin mu aiwatar da aikin da'aka samu sai nida Yarana mun biya buk'ata dake, bakinsa ya lashe tare da kawo hannusa ya shafi k'irjinta ya saki mayen murmushi haka suka jata zuwa motarsu suka tayar su ka bar gurin. Gudu suke sharara wa Aishat ko sai hawaye takeyi tanaso ta basu hak'uri amma ina ba hali bakinta yana rufe gam da salatab Ogansu ko tasata yayi a gaba yana kalonta don ya rinyar ta matuk'ar masa kyau ji yake koma dai ya fasa aiwatar da abunda aka sasune kawai ya b'oyeta ya mayar da ita Matar sa kuma inda zai na hutawansa. Fatan bakinsa ya lashe tare da yin wani murmushin mugunta.
Falmi ko tana cikin wasu kawayenta wanda kalo d'aya zaka musu ka gane tattatun 'Yan bariki ne masu ji da bariki, wata kawar Falmi ta kaleta ta ce"Falmi gaskiya baki da kyau yanzu abunda ki ka sa ayi kenan niko kishiyarki kyau ta ke min". Wani mugun harara Falmi ta sakar mata ta ce"yanzu zamu b'ata da ke don duk wanda zai bi bayan Indi ko ya sota to tabbas makiyina ne ina adawa da shi". Gwantsi da ke gefe jin kalaman Falmi ta shek'e da dariya ta ce"har uwar Haiydar d'in kenan kina adawa da ita". Falmi ta ja tsaki"mtsss ita a su wa yanzu next harina ita ce daga nan ina fita gidan mu zaje gun Mummy na ne, dole mu koma gun Malamin nan inaga asirin nan ya karye ne". Gwantsi ta ce"ni ko in da ni ne ke Falmi bazan tayar da hankalina ba tunda gaki kintara kud'i kin dawo babbar mace, gaki da naira kuma ai Haiydar yana sonki da yawa tunda ke kikace da hannusa ke baki kud'in nan". Falmi ta ce"ke fa zabaki gane bane Haiydar nawa ne ni kadai da kinga abunda Indo ta min jiya sai kin bani goyan baya dari-bisa-dari". Wata Mama Zeey da ta ke gefe ta ce" ina bayanki karki ragar musu ko d'aya ai kishiya ba abin so bace kishiya! Kishiya!! Kishiya!!! ina bayanki a gama da ita kawai ki huta". Haka suka ci gaba da hiransu kowace da gur-guwan shawaran da take bata a gun.
Haiydar yana office duk ya ji hankalinsa ya tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye zuciyarshi ba abunda take tunaso masa sai Aishat, haka kurun ya tsinci kansa da son ganin Aishat a wannan lokacin cikin hanzari ya tattara komai daman time d'in tashi ya kusa. Da sauri ya fito ya nufi motarsa ya shiga cikin sauri ya ke tuk'in sai da ya kusa shiga unguwamsu gabansa ya soma fad'uwa sai gumi ke ketomasa, k'ara gudun motarsa yayi ga gumi sai k'ara keto masa yakeyi duk da sanyin A.C da ke motar amma bai hana sa yin gumi ba. Tun daga nesa ya ke hango wani mota sak irin na Aishat amma sai wata zuciya ta ce masa" mai zai kawo Aishat nan kawai dai kalar motar ce d'aya, ko da ya iso gun k'ofofin motar a bud'e ya ke, ganin school bag d'in Aishat bai san lokacin da yatak wawan burki ba ya fito daga motarsa. Da gudu yayi gum motar baiga kowa ba sai ya lek'a ciki ba ta nan ga hijab d'in mak'arabtarta a gun da hularta, sai takalminta kafa d'aya ko da ya kali kasa nan yaga jinin da ya d'id'iga a hankali ya soma bin jinin har ya kaisa gun da 'Yan iskannan suka aje motarsu, nan ma yaga alamar kafa inda kayi kokawa da kuma alamar ta k'arfi aka d'auketa, ga tayar motarsu da yayi ribas da kuma yanda ya tashi. Haiydar baisan lokacin da yasaki k'ara ba ya na kiran"Aishat! Aishat!! Aishat! Kina inane?  Mai ya same ki? Wa ya tab'a min ke?". Fad'uwa yayi a kan gwiwarsa kamar mai (nil down) yana k'araji yana ihu ga hijab d'in Aishat a hannusa ya na kuka wi-wi kamar yaro. Da gudu ya tashi yayi gabar yana kiran Aishat! Da gudu ya dawo yayi yamma yana kiran Aishat!! Ya sake dawowa yayi Arewa yana kiran Aishat!!! Yazo ya sake yin kudu yana kiran sunanta, ya dawo kaman zarare.

Masu karatu sai kun gansa abun gwanin ban tausayi ni kaina Rash bansan lokacin da hawaye yasoma gan-garo min ba.


            *®NWA*

                 *DEDICATED TO*
           *AISHAT MUHAMMAD*
      *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

               *RASH KARDAM��*

BABBAN KUSKURE... 200-206

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-200~203.*

Aishat da take ciki d'aki jin an kwan-kwasa k'ofa take cikinta ya bada sautin kululuuu! Wani fitsari ne ya taho mata bashiri ta sa hannu tana matse k'asan k'afarta duk a tunaninta Falmi ne, bata san lokacin da yanka bayi da mugun gudu ta kulle bayi sai ga fisari na gan-garowa ta k'asan k'afarta. Sai rarraba ido takeyi jin an kara buga k'ofar ae sai ga fitsari na zuba take idanunta suka soma ciko da kwalla addu'a ta fara karantowa duk wanda yaxo bakinta kawai yi takeyi.
Falmi  ko duk wani tugu da zata had'a ta had'a, bata soma shirin dawowa gida ba sai k'arfe tara da mintuna.
Haiydar jin shiru yayi yawa ba a bud'e ba da har zai tafi sai ya fasa, sunan Aishat ya kira sai da yayi baki uku. Aishat daga bayi taji muryan Haiydar da kamar bazata fito ba, amma sai ta daure tana d'an sand'a ta fito falo muryan shi taji, sai da ta tattara nutsuwarta ta amsa ta ce"gani ina zuwa". Bayi ta koma ta d'auraye jikinta ta fito zani ta d'aura kafin ta bud'e k'ofar. Haiydar ya ce"beauty ina kika shiga?". Sai da ta d'anyi jim kafin ta ce"na d'an shiga wanka ne shiyasa". Haiydar yayi murmushinsa mai k'ayatarwa ya ce"beauty shine bazaki kirani inzo na miki ba, bai kamata kina wahala da kanki alhalin gani a cikin gidan miye amfanina? Kin san bana so ki wahala da yawa". Haiydar ya karashe maganan tare da d'aga ma Aishat gira tare da kashe mata ido d'aya. Aishat ta kauda kanta gefe ta ce"bana bukatar hakan kuma da wake min wanka? Ko kaine kake min? Don haka bana bukatar hakan". Zai sake magana ta ce"wai lafiya kuwa? Ni fa zan rufe k'ofa don ina da abunyi". Haiydar ya san halinta da sauri ya mik'a mata ledar bata bari yayi magana ba ta ce"thanks you". (Nagode maka). K'ofar ta mayar ta rufe tare da sakin sassayan ajiyar zuciya ledar ta ajiye taje tayi wanka kafin tazo ta bud'e ledar sai da taci abinci dake ciki tayi hamdalah ta tattara kayan zata fitar waje nan fa ta tuna da abunda ya faru kamar zata koma ta ce"ai Haiydar yana gida ba zai bari ta bugen ba". A hankali ta bud'e k'ofar d'akin da sand'a ta ke tafiya, sai da tazo dai-dai falo ta d'an leka taga ba koma sai da ta leka hanyar d'akin Falmi taga ba kowa kafin ta fito sad'af-sad'af take tafiya har ta kai komai kitchen (madafi) tukun ta dawo nan ma sai da ta leka har tazo tsakiyar falo taji ance kee ba karanin razana tayi ba take kayan cikinta suka soma bada sauti shooky.

                 *®NWA*

               *DEDICATED TO*
         *AISHAT MUHAMMAD*
    *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

              *RASH KARDAM��*
[7/14/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-204~206.*

Kee taji ance bak'aramin razana tayi ba sai da kayan cikinta suka fara shooky. Duk ta gama d'auka Falmi ce harta had'a hannayenta biyu alamar zata bada hak'uri, a hankali ta juyo sai ganin Haiydar ne ke waya da alamar ransa na b'ace gashi kuma ya ganta ta rasa ya zatayi sai kawai ta wayance taci gaba da sand'ar sai ta d'an jiyo kamar mai wasa abinko sai ya mata kyau. Haiydar kasa d'auke idonsa yayi daga gareta harta shiga side d'inta. Aishat tana shiga ta sauk'e ajiyar zuciya bayi taje tayi brush tazo ta kashe wuta tayi addu'a ta kwanta.
Haiydr kasa tashi yayi a falon yana jiran yaga dawowar Falmi ransa ya gama b'aci sosai. Falmi ne tashigo da sallamarta ganin Haiydar ta b'ata rai itama tare da k'arasowa cikin falon, Haiydar cikin b'acin rai ya ce" kee daga ina kike?". Falmi bata tanka masa ba sai wani harare-harare takeyo, Haiydar ya ce"Falmi kinason ki b'atamin gidana don Aishat duk abunda taga kinayi shi zata koya wanda ni kuma bana so ko kad'an ta koyi munanan d'abi'unki". Wani harara Falmi ta b'alla masa tare da jan tsaki tayi d'akinta, da sauri ya bita ama kash! Ta sanya ma d'akin key(mabud'i). Ransa  ya gama b'aci bai san lokacin da ya fara safa-da-marwa a falo tare da dunkule hannusa ya bugi iska, da kyar yasamu ya koma d'aki ya kwanta zuciyarsa na masa suya.
Da safe da wuri Haiydàr ya fita Aishat ma ta shirya school bus yazo d'aukarta, ko da taje school da suka zauna da su Sanah ta basu labari abunda ya faru dariya sukayi sosai kafin suka bata shawarwari. Sai da aka tashi ta bi gidan Hajiya sai da tayi la'asar kafin ta d'au motar ta nufi gida daman a gidan ta bar motar. Tafe take tana tuk'i cikin nutsuwa tun daga unguwansu Haiydar taga kanar wata mota kirar jeep bak'a da glass bak'ak'e tana binta, sam bata kawo komai ba tayi ta tafiyanta sai da tazo hanyar shiga unguwansu bayan Airport taga wannan motar tazo da gudu tasha gabanta, gashi gurin bakowa shiru gurin wasu bak'ak'en mutane ne suka fito daga bak'ar  jeep d'in nan tare da zuwa dai-dai jikin motarta suka bud'e, cike da tsoro ta ce"lafiya mai na muku? Dan Allah kuyi hak'uri in motar kukeso in fita na baku amma kar kuyi min komai". Wani daga cikinsu ya wanka mata lafiyayen mari ya ce"zaki rufa min baki ko-ko sai kinji maza?". Take jikinta ya soma b'ari idonta sai ruwan hawaye ke zuba, d'aya daga cikin mutanen ya ce"yah! Oga zamu gama da ita a nanne?". Wani murmushi Ogan yayi ya ce" no zamu tafi da ita don naga ta min zata yi test(d'an-d'ano)dole sai na huta da ita kafin mu gama da ita. Aishat najin haka ta fara zatayi ihu d'ayan ya zaga ta bayanta ya mata kyakkyawan riko wani yazo manna mata salatab a baki, k'okarin janta suka somayi amma tana turjewa abunka da fatar mace mai samu hutu, garin janta taji ciwo a hannu sai ga jini yana zuba har saida ya d'idd'iga a gun. Ogan gani tana da taurin kai kuma zata b'ata musu lokaci yazo dai-dai ita cikin muryan 'Yan iska ya ce"tun da ki kayi taurin kaikuma ki ka b'ata mana lokaci kafin mu aiwatar da aikin da'aka samu sai nida Yarana mun biya buk'ata dake, bakinsa ya lashe tare da kawo hannusa ya shafi k'irjinta ya saki mayen murmushi haka suka jata zuwa motarsu suka tayar su ka bar gurin.

Ni Rash bansan lokaci da nasaki k'ara ina binsu ina kiran Haiydar amma ina sunyi nisa ba taimakon da zan iya bata a lokacin sai addu'a.

               *®NWA*

                *DEDICATED TO*
        *AISHAT MUHAMMAD*
   *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

 
               *RASH LUV��*

BABBAN KUSKURE... 197-199

[7/12/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-197~199.*

Ta juya idonta ta ce" na manta ban miki godiya da karamcin da kika min, gaskiya kin can-canci in gode miki, kin had'a ni aure da gwarzon Mijiki Haiydar kuma kin iya had'i sosai, don ni kaina na san, nasamu mijin nuna wa sa'a gashi kyakyawa, jarumi a kowanne fage nagode". Hannu Aishat tasaka akan bakinta tare da yin kiss ta hura ma Falmi, ta saki wani murmushin mugunta, don yanda taga Falmi ta dawo, juyawa tayi ta nufi d'akinta tana rangwad'a. Falmi batan lokacin da ta d'aura hannu aka ta fara ihu tana cewa"lalle yau nasan na *TAFKA BABBAN KUSKURE* wato d'an hakin da na raina...... Na raina Indo sai ita ce zata gasa min aya a hannu". Falmi ta fara Safa-da-marwa a falon bakinta ta ciza tare da dunkule hannu, tana tunanin mafita yanzu wani mataki zata d'auka gashi taga Aishat da zafin ta take can komai ta tuna tasaki lallausa murmushi ta nufi dakinta wanka tashiga don tasamo ma kanta matakin da zata d'auka.
Aishat ko tana barin falo da gudu tayi d'akinta key(mabud'i) tasa ma d'akin ta rufe tare da jin gina a jikin k'ofar dakin tana maida numfashi. Wani sassanyan ajiyar zuciya ta saki a fili ta furta" lalle na iya cika baki duk wannan kurarin kamar zan iya dukan Falmi ai ko yau da ta shakeni sai dai wata Aishat bani ba". Jin kamar motsi yasa ta zabura jikinta sai b'ari yake ta ce"wayyo yau na janyo ma kaina tabbas yau inta rikeni nikam sunana gawa". Wani dabara ne ya fad'o mata doguwar kujeran hutuwa dake cikin d'akinta ta janyo zuwa bakin k'ofar ta tokare k'ofar dashi, wai ko da Falmi ta biyo ta bazata iya b'alle k'ofar ba. Sai zufa takeyi ga tsoro da take ji duk a razane take sai zare idanu takeyi tamkar wacce tayi ma sarki lafi.
Haiydar ko d'aki ya koma yana tunanin irin rayuwan da zaiyi da matansa biyu, gashi yanzu ba abunda yake da k'auna da muradi kamar Aishat amma sam bai ganin fuska ajiyar zuciya ya sauke a fili ya furta"Allah ka sanya Aishat sona". Mik'ewa yayi tare da d'aukar key(mabud'i) d'in motarsa ya fita waje don ya samu abunda zai ci.
Falmi ko tana fitowa cikin hanzari tasoma shiri make-up (kwaliya) tayi ta d'auko kaya tasaka tare da d'iban kud'i tana wani murmushin mugunta ta fita.  Wayarta ta d'auka ta kira wata magana sukeyi kasa-kasa wanda nikai na Rash duk son d'ibo rahoto na bansamu damar naji mai take ce wa ba, dole na hak'ura injira ta gama na bita naga mai take shiri aikatawa.
Haiydar yana fita gurin cin abinci yanufa ya sayo guda uku, gida ya dawo ko da yazo falo yaga ba kowa, d'akin Falmi ya nufa yaga batanan da alamar ta fita ledar da yaso nata ya ajiye mata. Ya nufi b'an garen Aishat ko da ya tura k'ofar yaji a kulle sai ya kwan-kwasa k'ofar.
Aishat da take ciki jin an kwan-kwasa k'ofa take cikinta ya bada sautin kululuuu! Wani fitsari ne ya taho mata bashiri ta sa hannu tana matse k'asan k'afarta duk a tunaninta Falmi ne, bata san lokacin da yanka bayi da mugun gudu ta kulle bayi sai ga fisari na gan-garowa ta k'asan k'afarta.

Niko Rash mai zanyi in banda dariya nace"haba Indo karki bada ni mana duk kurarinki nan ace kina wannan tsoro haka?".

Masu karatu kuyi hak'uri da d'an wannan yau banda charged ne sai gobe zakujini in sun bar wuta.
Luv u all my fanz����.

                  *®NWA*

  
                  *DEDICATED TO*
           *AISHAT MUHAMMAD*
      *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                   *RASH KARDAM��*

Popular Posts

 
]]>All content on thisblog are copyright protected and cannot be reproduced on other websites without permission.