AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
13
Duk wani abun da zasu min na kanyi, hakuri in jure don ba dansu nake zama ba,
haka rayua tayi ta tafiya har na gama HND a gidan dad na karanta fanni business, yayin da Zee Auta ta gama secondary school dinta ita da Sadiya da futha, ranan murna ba a magana don sai da dad ya shirya mana kayatacen liyafa, bayan mun gama mun dawo zaman gida sai Auta da ke zuwa islamiyya, ni kuma duk wa aiki ina yi duk da cewan sun hana ni yi amma nakan sa kaina wani lokacin.
samun shigan da nayi a gdn shi ya daga wa maikatan gdn han kali har suke ga su da suka dade ba a musu abunda ake min, tun daga ranan suka fara kule2 na hanyar da zan bar gdn.
Baba sani da kawu isiya burinsu yanzu shine tayaya dukiyar dad zai dawo hannun su don kulum samun cigaba ya keyi, kuma ba abunda suka tsana irin yawan sadaka da kyautata wa mutane, acewar su baisan zafin dukiyar sa ba, sun sha zuwa su samesa gameda ya daina yawan rabar da dukiyan sa, yaki, ya ce in dai akan wan nan ne kar su sake tun karansa, tun daga lokacin suka fara kule2 na makircin kawar da Dad.
Basu tashi razana ba sai ran da dad yace musu zan fara aiki, a gurin kuma yanzu zai bani manager a company nin, ko kuma duk wani shiga da fuce kudi yazama ta hannu nane, ko wani kayan da za’a saya duk zai dawo hannu na,
ran da dad ya sanar min bakaramin murna nayi ba har kuka nayi, asai akwai irin su dad a duniya, asai bazan yi maraicin iyayeba, dad yayi ta lalla shina,.
Han kalin su baba sani ya tashi matuka, nan suka fara shawar su jefa dad acikin ruwa nan baba isiya yace tayaya zamu jefasa, haka sukayita shawar wari, har baba sani yace mufara masa baraza ya daura mu a kan dukiyar sa, ko ya bamu in yaki sai muje gd mukashe shi da iyalansa da dan koran da ya daura akan dukiyar, nan sukace gakan za’ayi, tun daga wan nan rana suka soma kiran dad suna masa bara zana, akan dad ya basu dukiyar sa yaki, don har nima a sha yimin barazana akan na bar gdn dad amma naki don da Allah na dogara nan da dad zai rasu ya kiramu ya bani AMANA zee san nan yasanar mana ana masa baraza, amma yaki fadan ko suwaye, bayan da ya fita ne na kirashi a waya na tambayesa da farko ya ki fada min sai da na sanar masa cewa nima ana min baraza na, na basa lbr kafin ya ban lbr komai yace da kar in sanar da xee hankalinta zai ta shi, da daddare suka zo don kashe mu gaba daya cikin ikon Allah ya kubutar da ni da Auta kuma a lokacin taga wayan da suka kashe mata iyaye, dali2 da yasa yanzu na sanar mata kenan wannan shine lbr mu, Malam da inna laure suka dago fiskansu cike da kwalla ga tausayi auta ma kukan take ni kuma hawaye ne, wani na bin wani.
Malam yace Allah ya jikan iyayenku, san nan a duniyar nan har ana samun marasa imani irin wayan nan mutane sun ci AMANA ga bata ZUMUNCI da sukayi ba ko tausayi a ransu sai son duniya, kuyi hakuri da rashi, da sannu Allah zai toni asirin su ya kuma saka muku, Allah ya jikan su muka amsa da Ameen.
Yan uwa amin afuwa na rashin jina kwana 2 waya tace ba charged, kuma ban samu zama ba.
Luv u all my fanz
Saturday, 1 April 2017
Home »
» AMANA TA CE 13
AMANA TA CE 13
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment