New Post

Saturday, 1 April 2017

AMANA TA CE 20

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
  
               20
                            
Kiiiii kake ji karar mashin ta tashi sama da ammar nan mutanen gurin duka dau salati, wasu da gudu sukayi gurin, abinci kam duk ya zube, nan mutane sukayi kansa cikin ikon Allah bai ji ciwo ba sai dai ya dan buge kafarsa gefen hanya aka maidashi mutane sai sannu suke masa Ammar na dawo hayya cinsa sai ya hango robar abinci ta fashe maganin kam bai san ida ya yarshi ba, nan take wasu zafafan hawaye suka soma gangaro masa a zuciyarsa yana gode ma Allah daya sa yana da sauran rai in da Allah yaso sai kafarsa ta cire ko hannu yana da kyau a kowani hali ka tsinci kanka to ka gode ma Allah sai ya kara maka, cikin ikon Allah mai mashin ne ma ya dan kurkurje nan ya ba ma ammar hakuri don yanzu fitowarsa bai da ko sisi ajikinsa Ammar yace ba komai haka ya mike ya na din gisawa ya sake zuwa chemist ya sayo paracetamol da da maganin mura na ishirin ya sayo ma auta shinkafa talatin ba ko ruwa nan ya laluba aljuhunsa ya ga biyar hamdala yayi ya sai mata pure water biyar da sauri yana din gishi ya nufi gunta.
yasamu duk ta dawo wani iri dagata yayi yana mata sannu abinci ya fara bata da kyar ta iya ci kafin tasha magani ya maida ta ya kwantar nan yaje yayi alwala yayi sallah bayan ya idar yayi nafila yana gaya ma Allah kukansa kafin ya dawo gurin auta ga yunwa tasoma damunsa sai da yaga bacci ya dan dauketa kafin ya sake komawa cikin kasuwa ya yi sharan yayi sa’ah mai shagon mutumin kirki ne ya basa dari buyu nan ya bashi sauran abinci ammar yayi godia yaci kafin ya sake suwa wani gu ya musu aiki nan ya.samo dari uku nufo hanya.
        Tun daga nesa ya hango auta rike da cikinta tana juyi da sauri ya karasa gunta,nan yasoma mata sannu yariketa kuka tasoma masa duk ya rude ya tambayeta mai ke da munta tace cikinta ganin yanda take juyi yasa ya dauketa da sauri ya nufi titi nan rake aka zuna musu ido dake haka ya nufi chemist da ita nan mai chemist ya soma dubata aiko yace Malam period dinta ne zaizo nan ammar ya zare ido yaya zaiyi ba pant ba gun wanka mai chemist ya bata magani tun agun tasha ya dan kwantar ta akan benci sun dan dade don ciwon ya dan ragu sai rashin karfi ajiki nan ya cemasa kudin magani 200 haka ta bashi nan suka mike zasu tafi kenan yaga shini ya bata gun da ta zauna nan ta zare ido yau yaga ta kansa ya zaiyi kenan Yasalam Auta ko tsaban kunya kasa daga idonta tayi sai hawaye nan ta fara Allah ya isa masu baba sani duk sune ummul aba isin sata cikin wan nan hali.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts