New Post

Saturday, 1 April 2017

AMANA TA CE 30

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
  
30
                            
Sai karfe 12:00 suka isa garin sun samu su inna cikin lfy bakaramin murna sukayi da ganinsu ba nan ina ta musu tuwon geronta mai kaushi miyar danyen kubiya ga man shanu sosai su kaci suna zuba santi baran Kausar ma tafi kowa santi don ta dade bata ci irin wan nan abicinba ga surki yaji suga sosai koni rash  sai da na lashe baki don yawuna yana tsilo tsabar kamshi ya ishen.
Sai da suka huta bayan sunyi sallah asazahar tukun ammar ya basu tsarabansu nan sukayita murna kafin suka fara hiran yaushe gamo nan ammar ke bama su inna lbr bayan barin su garin sun tausaya musu sosai sai yamma sukayi wanka suka fita zaga gari dandali suka nufa tun daga nesa suka hango yam matan garin sunyi wanka masu sayar da abinci na sayarwa abun dai sai kun gani.
Najaat ce da tawagar kawayenta tunda ga nesa ta hango ammar da su auta zunguro ummen da zulai kaii kalli wancan kamar wanda suka taba zuwa maciya da malam la shine dan birni kai kali wancan auta ta nuna sina kama da wan nan yar India mai gashinan ga kawarta ma kamar yar india nan suka saki baki sai kallinsu suleyi haka su auta da kausar da ammar sukayita hotuna sai magriba sukamar dandali suka dawo gd bayan sunyi sallah ne suna zaune suna hira sukaji surutun mutane da yawa kuma mata sai azo a dan lekasu a koma
can dai abun yayi yawa sai malam ya mike ya a hankali ya fake aiko lokacun su najaat suka leko karaf malam ya rike ta waye nan tafara inda2 daman tazo gaida ina ne sai taga yan birni malam da ya gane waye sai ya kyaleta yace su bar labe ba kyau nan suka shiga cike da murna suka gaida su inna sai satan kallon ammar sai da suka dade sosai kafin suka musu sallama suka nufi gd su malam ma sukayi sallama wa su auta suka shiga dayan dakin inna da kausar da Zee suka kwana daki daya da safe inna ta soya musu kosai da yar tsame ta musu kunun tsamiya haka suka karya cikin farin ciki daga nan suka fara shirin dawuwa bauchi,
Su inna sun cika mu da tsaraban kauye su daddawa ne wake gyada kuka harda zuma,
Wanka sukayi sannan ammar ya ciri 10k ya bama malam inna ko 5k godia sukayi sosai kafin suka rakosu gun motarsu suka dau hanyan bauchi.
Tun bayan da su kausar suka tafi kauye da yamma ahyan tazo cin abinci ya ga ga abinci har abinci a ido yana sawa a baki yaji ba test karshe haka ya hakura tea ya hada ya sha mum ma da tana sawa a baki ta ajiye gashi hauwa bata nan ta shiga cikin gari yau munay ce tayi abinci sai da ta sha tea kafin ta kira munay tayi mata fada akan ta dage ta koyi girki din girki shine mace kiga kausar da Zee mana yanzu ina ne zasuje baza suyi abinci wa mitum yaci har yana santi Munay sai zun bura baki takeyi ita a dole an mata fada ta tashi ta nufi daki sai kunkuni takeyi haka dai a daddafe suka kai washe gari Mum ke musu abunci ahyan ma ya masu kausar ta dawo don yafi gane cin abincinta sai ko in mum ce ta musu yana ci sosai.

Ba mu iso cikin gari ba sai kusan 1:40 dake ba mu fito da wuri ba ko da muka dawo wanka mukayi muka ci abinci kafin mukasa aka shigo da tsaraba muka nuna wa mum yau hauwa’u mai girki ta dawo dan haka daki na nufa na fara baccin gajiya.
Yau kwanan mu 3 da dawuwa daga kauye kulum gidan mu cike yake da wakar india daga gani nansan yayan su kausar ke sawa kuma shima da alama masoyin wakokin india ne kulum in ina daki yasa wataran nayi rawa wataran in zauna ina bin wakar baran wakikin Arjuly Siyn ina son wakarsa yau tun da safe munay tazo ta min warning in gyara mata daki san nan in kade mata cikin Waldrop dinta zata fita sai yamma zata dawo tun da ta fita nasa ka wando wizy da yar rigata mai dan tsayi ya kama jikina nan nashiga na gyara ma munay daki na fito zan sauka kasa dauko dauko fresh milk insha don nayi aiki sosai ina fitowa naji daga wani dakin da ke kusa da down stairs naji ansaka wakar Vear wai take Surili akhiyon wale, daman mayar wakan ce ko ada nan na fara tika rawa irin na wakar don mutum2 ake wakar amma ni daya nakeyi sai nan take na tsinci   kaina cikin ni shadi ina bin wakar ina rausayawa.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts