YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-46~50
Suna isowa gida, Beeba ta ba wa mai
Napep kud’insa, ta d’auko su bargo, da
pillow, suka nufi k’ofar shiga gidan.
Khadi ta tsaya, Beebah ta juyo ta kali
Khadi, Tace”lafiya naga kin tsaya?. Nan
take idon Khadi ya kawo ruwan hawaye,
tafara magana, cikin muryan
kuka,”Beebah ina tsoron shiga cikin
gida, don Gwaggo zata iya dukana, kinga
Baba baya nan, Beeba ta kalleta cike da
tausayawa, Tace”Addah muyi addu’a in
Allah ya yarda bazata yi mana komai ba.
Kalamai masu dad’i, da ‘kwantar da
hankali, tayita fad’a ma Khadi, kafin ta
yarda sukayi addu’a, tare da shiga gidan.
Assalamu’alaikum! Gwaggo dake d’aki,
tanata sababi, taji kamar muryan Beeba
da sauri ta fito, har tana tuntube, tana
fitowa taga su Khadi, wani uwar ashar ta
narka mata, da kalon yau zaki sani.
‘Daki ta koma, ta d’auko wata
zu’ke’kiyar bulalan ta, Gwaggo tace” yau
sai na rama, marin da kikasa Malam
yamin, kuma wahala yanzu kika fara,
Mayya kawai, sam tsabar bala’i, bata
lura da qofar window, dake bud’e ba,
jikake Garamm Gwaggo ta gwaru da
window, sai da ta fadi a kasa. Nan take,
ta saki ‘kara, oh ni Rash nace”su Gwaggo
ko d’an dauriya babu. Ihu take kamar
qaramar yarinya, Khadi da gudu, ta iso
gunta fiskanta, d’auke da hawaye, sannu
take ma Gwaggo, cikin tausayawa.
Gwaggo da ‘kyar, ta iya yin shiru, tana
d’agowa kuwa, bakin ya kumbura
sundum, ko danaga bakin, bansan
likacin da nasaki dariya ba. Gwaggo
d’aki tayi, ko magana bata iyayi, sabida
bakinta, paracetamol ta sha, don ta ji
sanyi ajikinta. Khadi kam d’aki ta shiga,
ta takure gu d’aya. Tana cike da tunani,
mai tasa Gwaggo ta tsane ta haka?. To
mai iyayenta sukayi ma Gwaggo ta ke
tsanar su haka, har ya shafeta?. Duk
wayannan tambayan bata da amsansu,
haka ta hak’ura, dan bata da amsan
tambayanta.
Gwaggo tunda baki ya d’anyi sau’ki, ta
soma gana ma Khadi azaba, na yau
daban, na gobe daban, wani saran da ta
samu, in Malam nanan, bata cika gallaza
mata ba, amma in Malam ya fita, Khadi
sai ta gwammace kid’a da karatu. Khadi
ta yanke shawaran samun Malam,
Tace”Baba ina son, in fara zuwa gurin,
koyan d’inki, yafi zaman da nakeyi.
Malam ba k’aramin dad’i yaji ba, kuma
hakan zai ragemata, yawan damuwa,
sati guda ya nima mata, tafara zuwa,
amma sai dai yana nesa da unguwansu.
Gwaggo tayi bala’i ba ‘kadan ba, gani
bata da mafita yasa ta hak’ura, tafara
tunanin, sabon hanyan da zata, gallaza
ma Khadi.
Kwanaki sun tafi,Yau saura sati d’aya,
Dr Umar ya kammala course d’insa, suna
yawan waya da Dr Abdul.
Khadi tana zuwa gurin k’oyan d’inkinta,
gata da hazaka da basira, yanzu har ta
fara had’a kayan yara, zata yanka da
kanta ta had’a. Ganin haka yasa Malam
ya sayo mata, keken d’inkin hanu,
dontana, yan facin da sanda na mutane,
tana samun biyar goma. Masu karatu
karkuso kuga Gwaggo ranan, kamar
zatayi hauka, dan bak’in ciki da takaici,
Khadi kam kule kanta, tayi a d’aki, don
Gwaggo tace yau ko ita ko Khadi.
Fanz kumin hak’uri, na rashin jina,
k’wana biyu, bama samun wuta ne.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» 'YA'YA DA DUKIYA....... 46-50
'YA'YA DA DUKIYA....... 46-50
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment