A’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-41~45.
Sai da guri ya lafa,Dr Abdul yace”Baba
ka same ni, a office d’ina. Biyosa yayi,
suka nufi office d’insa. Sai da Dr ya
zauna, yace”Baba ka zauna, magana
zamuyi da kai. Malam ya zauna, ya na
fiskantan Dr, gurin shiru kusan, na minti
biyu, kafin Dr ya nisa yace”Baba ina son
in tan bayeka ne game da Khadija.miye
alakarta da wannan matar? Kusan
yawanci lokuta, in kun kawo Khadija ba
ta da lafiya, matan nan sai ta mata abun
da zai kunta ta. anya kuwa mahaifiyarta
ce?. Malam ya nisa yace”gaskiya ba
mahaifiyarta bane, Khadija yar riko ne a
hannu mu, nan Malam ya kwashe
tarihin Khadi, ya basa a takai ce, ba Dr
Abdul ba, ni kaina Rash na tausaya
mata.wayar sane tayi haske alamar kira
ya yanke, d’agawa yayi, ya ga duration
wajan awa d’aya da rabi, sai alokacin ya
manta, bai kashe wayar ba. Dr Umar da
ke jin, duk abun da ya faru da Khadi,
tare da tarihin rayuwan ta, take yaji
yana son tai maka mata. Ta bashi
tausayi, da ace yana 9ja da ya san
abunyi, kwanciya yayi, a lafiyayen
gadon sa, fiskansa yana kalon silin, cike
da tunani kala-kala, har bacci ya
d’aukesa.
Dr Abdul ya nisa yace”gsky Baba ya
kamata ka d’au mataki, don yarinyan
nan, tana yawan aiki da ruwa, ga
wahala ya mata yawa. Malam
yace”nagode in Allah ya yarda, zan d’au
mataki, sallama ya masa ya koma, gunsu
Khadi da har a lokacin, kuka takeyi
sosai, ko da ya iso, ya kalleta cike da
tausayawa, yace”Khadeejatu~Kubrah!, ki
kara hak’uri akan na da, nasan ki mai
biyyace, duk da Gwaggo tana cutar da
ke, kuma kina hak’uri, ki ‘kara akan na
da, kinji ‘yar albarka, kai ta d’aga masa
alamar eh!. Sanna tace”Baba ka maida
Beeba gida, tunda Gwaggi bata son
zamanta anan. Murmushi yayi,
yace”Beeba ba inda zata koma, har sai
an sallame ki, Beeba ‘yatace nafi,
Gwaggon ku iko akanta. Nan ya ta gaya
mata kalamai masu dad’i, har ta mance
da muwarta, dariya suke yi, ita da
Beeban ta.
Gwaggo ko da ta koma gida, taringa
masifa da zage-zage, har Malam ya dawo
bata daina ba, har tana cewa”kasake ni
mana, tunda yarinyan ta lashe
kurwanka, d’aki ya shiga, ya kyaleta ta
gama sababinta.
Kwanan su Khadi biyar, a cikin Asibiti
aka sallame su, tun a hanya take far
gaban, dawowa gida, don bata san dame,
Gwaggo zata tareta ba.
Dr Umar kuwa tunda yaji labarin,Khadi
yaji yana son tai maka mata, yarinyan
ta bashi tausayi. Wayarsa ya d’auka ya
kira Dr Abdul bayan sun gaisa yace”ya
aikin dai? Daga ban garen Abdul
yace”Alhamdulilah! Aiki ba dad’i. hira
sukayi sosai, Dr Abdul yake tambayar Dr
Umar yaushe zaka kare course d’in nan?.
Ajiyar zuciya yayi, kafin yace”saura
wata shida mu gama, nima na damu in
dawo 9ja, nayi missing abubuwa da
yawa. Cikin zolaya Dr Abdul yace” harda
Baby Sakina ko?. Mtss yayi d’an tsaki
yace” ana ta kai, waya ke ta kaya.
wannan mayyar yarinya, maras kamun
kan, ina zan kaita?. Ae saninta ya fi
nawa. Yauwa ranan wacece naji ana
hayaniya akanta?. Rannan muna waya
da kai, kamar a Ward d’in mata ne, sai
da Dr Abdul ya d’anyi tunani kafin
yace”ok! Khadijat ne, nan ya kwashe,
labarinta ya basa. Dr Umar ba karamin
tausaya mata yayi ba. Ya kuma kudiri
aniyar, duk randa ya ganta cikin
damuwa sai ya tai maka mata, duk da
bai san ya kamani ta yake ba.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» 'YA'YA DA DUKIYA... 41-45
'YA'YA DA DUKIYA... 41-45
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment