New Post

Saturday, 1 April 2017

AMANA TA CE 22

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
  
               22
                            
Haka suka yi ta hira kulum ammar sai yaje dako ganin ba zai fiddasu ba ya nimi gurin mai sai da kayan fruits da kayan miya suka fara sayarwa yazana yaro agun nan ya na dan samu har mutu min ya kaisa gidansa da ke bayan winti market daki biyi ne daya ciki da falo shida matarsa sai daki daya karami ba ko flasta su ammar ke ciki kulum matarsa sai tasa auta aiki gata da kazanta auta bata iya gani sai ta gyara gurin wanki yaranta tace sai tayi tun auta bata iya ba harta saba ko kadan bata fada ma ammar ba don zai iya cewa su bar gidan ita kuma bata so suyita yawo a titi wataran tayi kuka ta share hawayenta haka tayita hakuri gashi abinci dan kadan take bata kamar na dan yaro karami sai dare ammar ya somata na ma da madara haka sukayita rayuwa kwanaki sun wa watanni sun tafi har sun kai shekara a bauchi ba abunda ya canza sai baki da sukayi da ramakam akwaisa duk da ammar na iya kokarinsa akan auta duk abun da yasan zai mata kyau sai ya sai mata har yasata a wata islamiya dake bayan unguwan tana zuwa, shiko riga mai kyau bai damu da kansa ba wataran har mita take masa kayansa kala uku rak itako ya cikata da kayan ado duk iya samu kudi ma ita yake kashewa hakan yasa sa’dat shiga tashin hankali don mijinta baya kashe mata kudi haka gashi yaron hannunsa yana hidima wa kanwarsa nan take lbr wa makwabciyar ta tace ke sa’adat bazaki ganeba ne haka kurum zai na kashe mata kudi batare da yana latsata ba daki daya fa suke kwana in baki shawara yau ki fito ki lekasi kigani nan suka tafa sukayi shewa hakao akayi daddare ta fito cikin rashin sa a taga ammar a waje yake kwana auta tana ciki sai datayi haka har sau uku awajr take ganinsa sai randa akayi ruwa shine taga ya kwana a daki ko da taleka taga shi yana bakin kofa auta na karshen daki ba haka taso ba amma tsabagen makirci irin nata nan tafara habaici ma auta akan ammar na aikata masha’a da ita ranan tayi kuka amma ta danne bata fada ma ammar ba
don tasan yana da zuciya sosai haka sukayita rayiwa abunu tausayi.
Abangaren ammar kuwa kasuna tafiya dai2 har yayi customer a kwai wata hajiya datake yawan sayan kayan salad da fruit agunsa da vegetables har sun saba wataran kam yarta take turowa tasaya agunsa hakan dai yaci gaba da dana’arsa, auta ko sai rama take kulum in yasata a gaba yana tambayanta tace bakomai haka zai gaji ya kyaleta.
              * * * * *
Zaune yake a gaban kayan fruits wata bakar HONDA CRV TA cike da nuna isa da gadara take taku tun daga nesa mutane ke kallonta sabida ta tafi dasu ga ta da kyau tafiya take kamar bazata taka kasa ba kai daga ka ganta kasan naira ya zauna ma iyayenta da fatarta sannu a hankali ta tsaya tana kallon yar fruits don ita bataga wanda mum tace tazo gunsa ba har taxo zata juya ta hango wani dogon saurayi fari mai kyau tamkar sharukan kalo daya za kamasa ya tafi da tunanin mace don daga ka gansa kasan baragon namiji bane kuma mijin nuna ma sa’a ne kasa kyafta idonta tayi akansa shiko bai ma san anayi ba wai kunu a wani gida, ko tan tama babu shine Ammar din da mum take sayan kaya a gunsa, woow amma guy din ya hadu matsalar daya ne rashin naira sai da taji wani mai saida fruit na gefen ammar yana cewa hajiya kaya za a baki kafin ta dawo tunaninta a gadaran ce ta isa gun ammar tace aslm ya kk tambaya nake wai wani shi ammar fiska ba yabo ba fallasa yace eh nine ammar din lfy cikin isa tana satan kallonsa tace hajiya Maryam Alkali ne ta aiko ni wacce take sayan kaya a gunka yace ok ina jinki nan tace wai ka hada mata kaya kamar yanda take saya nan Ammar ya hada mata kaya masu kyau ta bude jaka ta dauko kudi ta basa tsabagen kallon da take masa ta yarda posd din ta garin mayar wa jaka bata sani ba sai da ta bar gurin zuciyarta cike da tunani ammar har ta tada motarta ammar yaga poss ya bita amma ina tayi nisa nan ya budr sai yaga ID Card dinta da dunanta Munayshat Alkali nan yaga complement card dinta da address dinta da da sauri ya tsari mai mashin ya bi bayanta.
1 To masu karatu danso musan wacece Munayshat? Kuma wacece Hajiya Maryam Alkali?
2 Shin munayshat son Ammar takeyi zai amsa kuwa to ya rayuwan auta zai kasance
Kubiyo Yar gidan JARAWA don jin yanda zata kaya taku a kulum mai kaunarku   Yar Mutanen Kardam.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts