New Post

Tuesday, 18 April 2017

YAYA DA DUKIYA....86-90

’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-86~90.
Sai da yayi musu, sayya mai yawa, ya
nufi Asibiti. Ko da ya shiga, sai da ya
biya office dinsa, ya ajiye wasu files,
kafin ya nufi ,d’akin da su, Khadi suke.
Da sallama ya shiga, suka amsa masa.
Beebah ne “ta gaida shi, cikin
girmamawa ya amsa, “ya tambayeta ya
mai jiki?. “Ba shi amsa da sauki
Alhamdulilah!. Fita tayi ta basu guri, ya
kali Khadi da ke kwance, “ta gaida shi,
cikin muryan, marasa lafiya, “ya amsa
mata, tare da tambayan ya jikinta?. ta
bashi amsa da sauki. Ido ya zuba mata,
har saida tasoma jin kunya, ajiyar
zuciya ya sauke, ya kara lumshe idonsa,
a hankali ya bud’esu, cikin wani salo, da
karya murya, ya kira sunan Khadeejat!!!.
Duk da rashin lafiyan da take fama
dashi, sai da taji, jikinta yamata, wani
iri,”Na’am ta amsa masa cikin siririyan
muryanta. Ya kaleta, yace”Khadeejat!.
Na kasa hak’uri akanki, Khadeejat!. Ki
taimaki zuciyata, da take fama da
azaban sonki, My Khady tun randa, na
fara d’aura idona a kanki, nakamu da
qaunar ki, ki taimaka in samu gurbi, a
cikin zuciyarki. Duk maganan, da yakeyi
Khadi, bata ce komai ba. Sai lumshe
idonta datayi, kamar mai jin bacci, cikin
kasa-kasa da murya, harda d’an
sauk’owa daga kujera, Yace”pls
Khadeejat ki taimaki rayuwata. Tabbas
nasan ina aure ki, a matsayin mata,
kuma uwar ‘YA’YA NA, nasan zasuyi
alfahari dake, a matsayi uwa ta gari.
Khadeejat!. Ki sani duk wani abunda
akeso, mace ta gari ta had’a, kin had’a.
Khadeey na!! I’m deeply in ur love,pla
don’t let me go!! You d joy of my lyf, pls
n pls Khadeey!!, ki samamin matsuguni,
a zuciyarki, ko k’ad’an ne.
Ganin shiru batace komai ba,
Yace”Khadeetaul~Kubrah, in kin amince
pls ko murmushi, kimin in samu sanyi, a
zuciyata. Ganin shiru yasa yanayinsa ya
canza, duk da idonta na rufe, tana iya
ganinsa, amma shi bai lura, da hakan ba.
“Wani lallausan murmushi ta saki, tare
da rufe fuskanta. Ganin haka, ya sauke
ajiyar zuciya, yayi godiya ma Allah. Juya
masa baya tayi, duk yanzu kunyansa, ta
soma ji, ya dad’e yana mata hira, ganin
tana jin kunyarsa, ya ajiye mata waya
tare da mikewa, Yace”yau k’anwata
kunya na takeji, amma badamuwa,
wataran zanyi maganin kunyan nan.
“Ga wannan d’an ajima zamuyi waya,
ya fita abunsa, a waje yayi sallama da
Beebah. Ko da tashi go d’aki, lokacin
Khadi ta mike, sai murmushi take
zubawa, Beebah tace”Addah lafiya
naganki cikin wannan fara’a?, cikin
zumud’i ta labarta ma Beebah, itama
tayi murna sosai,nan suka bud’e, kayan
da yakawo musu, yasha addu’a kam,
suna bud’e na waya, kalo ya koma
kansa, sun yaba da kyan, wayan sosai.
Sai can dare taji wayar na k’ara, ko da
tad’aga wayar kasa d’aukan kiran, duk
sun rasa ma ya’akeyi, Beebata tayi nata
basiran ama ina! Har wayan ta yanke,
sai can dai Khadi tace”tsaya inaga
wannan, ruwan ganyen ne amsa kira, do
d’azu jan ya katse ne. Tana jan ruwan
ganyen, ta tafara jin magana.
Assalamu’alaikum! Wa’alaikumusalamu!
Ta amsa, sai tayi shiru, ”
Khadeejat ya jikin?. “Da sauki
Alhamdulilah!. Hira ya rinka janta dashi,
har sai da yaji, kamar bacci na son
d’aukanta, ya kyaleta.
Kwanan Khadi 7 aka sallameta, tayi fress
kamar batayi rashin lafiya ba, suna
dawo gida, suka samu Gwaggo bata nan,
suka shiga, harda Dr Umar ganin irin
yanayi, d’akin da Khadi take kwana,
ransa ba dad’i ya kira waya, ba’a fi
minti talatin ba, sai ga mota da sabuwar
Katifa, irin manyan nan, da filo da
bargo, aka gyara d’akin fess, ya musu
sallama ya tafi, ko da Malam ya dawo
yayi godiya, ana haka sai ga Gwaggo.
Yau kam ta cika kamar zatayi hakuka,
don ba haka taso ba, taso a fitar da
kayan amma Malam ya hana. Rayuwa
sai tafiya yakeyi, soyayya tsakanin Khadi
da Dr Umar sai abunda ya karu, kulum
suna gaisawa da Ilham, harta sata a
group d’in novel ta yi kawaye yanzu.
Duk inda kake da jama’a, baka rasa yan
gulma, acikin mukaraban, Dr Umar
ansamu wanda ya sanar da Sakeenat, Dr
Umar yana neman wata yarinya, yanzu
haka ana kan shirin magana Aure, nan
take hankalinta ya tashi, bashi ta biyo
jirgi yau ta tazo 9ja.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts