New Post

Saturday, 1 April 2017

AMANA TA CE 21

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
  
21                            
Ammar gaba daya ya rasa mai ma zaiyi ne sun dan dade agun mai chemist daya ga basu tafi ba ya lura da matsala dake ustaz ne yasha Sunnah ya koshi cikin kulawa yace malam lfy dai ko ammar ya dago idonsa da ya cika da kwalla ya ma rasa mai zai ce, mai chemist yace ya kamata ka kaita gd don tayi wanka ta huta ammar cikin muryan sa na rawa kamar zaiyi kuka yace mu baki ne a garin nan bamu da kowa cikin tausayawa yace ayya sai a lokacin ya lura da yanda jikin auta ya baci nan ya ce masu ammar zan muku taimako daya ga gd na banisa kazo muje gun matana ta taimaka mata da kaya ta gyara jikinta ammar yaji dadi yacd ba matsala nan ya riko hannun auta suka bi mutu min nan gd sa na bayan stadium plat ne ciki da falo sai stored sai kitchen nan ammar ya tsaya daga waje shikuma sukayi sallama suka shiga da auta nan wata mata baka mai dan kyan jiki gata da sakin fuska ta fito tana musu sannu dazuwa cikin harshen fullanci ya mata bayani nan naga fuskan Rahmat ya bayya na tausayi tace yar uwa shigo dake bayinta na falon ne nan ta hada mata ruwan wanka ta kaita bayin shiko mai chemist ya kowa waje gun ammar suka dan fara hira.
Rahmat ta ciro mata sabin pant guda 4 da Alway ko amfani da shi batayi ba ta dauko mata riga da siket daya da dogon riga dake da ka dan zata fi auta ki ba nan ta samata a wata yar jakan biki mai zip da hijab daya da sabulun wanka sinki da na wanki biyu nan ta saka mata riga da siket na eglish wears wanda tasa da hijab mai hannu blue yadin plan tuyobo bayan auta ta gama wanka nan ta bata pant tasa ta bata mai da powder tasha da lip stick kai kar kuso kuga auta nan ta yi kyau abunka da farar mace ga kyau azuciyar rahmat tana yaba kyau irin na auta abinci tabata nan taci sosai ta bata zobo yasha hadi kafin ta dauko jakan ta bata lokacin har ta dauraye mata kayanta sunsha ta nuke tasa mata a hakar tace ki duba waje kice musu kin gama nan auta ta leka tun da tafito ammar ke kallonta sai murmushi yakeyi ga idonsa ya ciko da kwalla rabonsa da yaga auta fess haka tun suna gun su inna laure a kauye yau har yar kyau tayi, auta tazo da sauri tasa hannusa ta share masa kwalla tace yaya na kabar kuka nima zaka sani kuka murmushi yayi yace babyn dad yau kinyi kyau sosai tace ta gode duk abunda sukeyi mai chemist na ganinsu duk sun bashi tausayi nan ta sai dama su sakon rahmat mai chemist yashiga gd ya fito masu abinci sai da su kaci kafin Ammar ya masa godiya auta tafito suka kara gaba. Rayuwa kenan
              * * * * * *
Sady abun duniya duk ya isheta yanzu bata isa tafita ba babanta zai dameta gashi yace matukar ta hadu da putha sai ya yanka ta kuma motar da zai bata ma ya fasa duk ita bai da meta ba sai sauyawan babanta anya yana da gsky yake haka yazama dole insan sirrin boye tana cikin wan nan tunanin pinky tazo cikin masu matsatsun kaya da kyar ta ke motsi cab su pinky an samu duniya yanda akeso rawan kai ya karu bare ga mota a hanu….lol… Hira sosai sukeyi anan sady take lbr ta ma pinky sauyin iyayensu pinky kafada tada ga alamar ko in kula cikin isa tace ni ba damuwata bane tunda zanci mai kyau insha mai kyau bani da matsala ga motar da zan shiga ko ina ba sa’ar dazata min raini kin ga ni ba damuwata bace kawai ke ma ki share kizo ayi harka dake sis sady tace ni kyale kyale baya gabana gasky nakeso tafito kuma zanyi iya kokarina pinky tace ae saikiyi ta kai nan tafice tashiga motar ta tabar gdn.
     Almarin futha kuwa jaratu tasa a gaba don ta cimma burinta shiyasa ita ko saurayi bata kulawa karatu takeyi ga yawan adu’a Allah ya bayya na Auta ya karesu a duk halin da suke.
Baba sani ko yanzu an waye daga zuwa wan na hotel din sai gdn wacce bazauran shida baba isiyaka holrwar su suke acewarsu Allah ya basu kudi dole suyi abunda ransu keso, Allah ta kyauta ya Allah kar kabamu kudin da baza mu kasheshi ta hanyar halal ba ameen.
                * * * * *

                                                          **********                                                                                              

Auta dun yitafiya kadan don su koma inda suke zaune bayan sun isa gun ammar yace zai sake komawa kasuwa ko zai sami aiki nan auta ta bata rai tace ka huta ai tau mun samu abunda zamuci kuma gobe ba zamu rasa ba don duk bakin da Allah ya tsaga ba zai hana shi abinci ba nan sukayita hirasu gwanin burgewa daga gani yau suna farinciki ammar yace to kimin afuwa nima naje cikin kasuwa a kwai bayan gidan wanka da akeyi na kudi nima in samu nayi wanka auta tace sai ka dawo Allah ya kare nan ya mike yaje ya biya naira 20 yayi wanka ya fito ya dawo gun autarsa suka cigaba da hiransu.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts