YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-96~100.
Tana fita suka nufi gida, da gudu ta
shige d’akinta, kuka ta rinka rusa sosai,
Hajiyarta ne ta shigo, tace”Zuly mai ya
sami k’awarki ne?. Zuly tafara bama
labarin komai. Hajiya tanisa
tace”Zulaihat ba ki ba ma kawarki,
shawara mai kyau, tunda Umar baya
sonta, sai ta hak’ura, ko ana son dolene,
kusani a ko da yaushe mace, ita ke jan
kimarta, nikam bazan goyi bayan k’arya
ba. Kunutsu kusan mekukeyi kun fa
girma fa, ae ko irin shigan da kukeyi,
wazai so ku?. Inayi fad’a Abban su
Sakeenah, yace nacika takura masu, ga
irinta nan, nima ina goyon bayan Umar,
matsawan ba canzawa kukayi ba. Kukan
Sakeenat ya karu, sai buga k’afa takeyi,
tana cewa”Hajiya ni baki sona, tunda
bakison abunda nake so, “tsawa ta daka
mata, ke bana son aakarcin banza da
wofi fa, sai da tamusu ba dad’i, tukun ta
bar d’akin.
Dr Umar kuwa lallashin Khadi yayitayi,
Gwaggo ne ta shigo da sallamarta, tun
daga waje an fata rahoto, shiyasa take
fara’a, tana ganin Umar, tace” eehehe
duniya yau taimin dad’i, in dai a kanka
ne, da Khadi naso da dukan tsiya suka
mata, ka wani shigo mana gida d’an
iska, wato karuwanka ne suka kasa
hak’uri suka biyo ka nan?. Ran Umar in
yayi dubu ya baci, don ba abuda yatsana
kaman a danganta shi da mazinaci.
Gwaggo ta zagesu tass shida Khadi, tayi
d’aki, Beebah ko sai basu hak’uri takeyi,
Khadi kam kuka takeyi, kafansa yaja jiki
ba kwari ya bar gidan.
Malam ya na dawowa ya samu labari,
yajima yana tunani daga k’arshe, yace
anya kuwa bazan dakatar, da Umar da
zuwa gidan nan ba?. Haka ya ta sake-
sake, har ya tsayar da amsa ma kansa.
Bayan kwana biyu Umar yazo, tun a
waje suka gaisa da Malam, nan ya fara
ba ma Malam hak’uri, Malam yace”ba
komai ya wuce, amma inaga ka hak’ura
da zuwa kawai, tunda daman ba wata
alaka bace a tsakanin ka da Khadeejat,
cikin firgici ya d’ago, yanaso yayi
magana ya kasa, Malam yajima yana
zargin Umar na son Khadi, amma bai
furta ba, shiyasa yayi hakan don ya
tabbatar. Don zan bada dama ga mai
sonta ya turo magabatan sa, ayi magar
Aurenta kawai. Inaga hakan shine zai
zame mata hutu, Umar duk ya rud’e,
yakasa magana jiki ba kwari, yabar
unguwan, gudu yakeyi Allah ne ya kaisa
gida lafiya, yana zuwa ya tarar da Mum
a falo, gunta ya nufa, ya kwantar da
kansa, a kan cinyanta, sai ga hawaye.
Cikin sanyin murya yace”Mum zan
rasata, Mum ki taimaka min, pls dan
Allah!. Cikin rashin fahimta Mum
tace”wacece zaka rasata?. Ajiyar zuciya
ya sauke, Yace”Mun Khadeejat ce, Mum
tace”kamar yaya zaka rasata?. Nan ya
kwashe labari, ya fad’a ma Mum komai.
Tab lallae Sakeenat bata kyauta ba,
amma ko da Dad d’inaka bai dawo ba
zamuyi waya dole asan abinyi.
A yan kwanakin nan duk Dr Umar ya
rame, hakan yasa Mum, ta sanar da Dad
d’insu, ko da sukayi magana dashi,
yace”bazai samu daman dawuwa, a
satin ba don haka zai sa mataimakinsa,
yaje da kansa, Mum tace” ni a’a ban
yarda ba, kasan Alhaji Bashir baya da
sauki, akan yara , kawai inaga zamu
nimi wani yaje, kuma kaga yanda
yakeson Sakeenat, komai zai iya yi. Dad
yace”shikenan duk yanda kukayi, Mum
ta sanar da Umar komai yayi murna,
sanna yace”shi yanaga a tura Baba
Liman, don yana da halin dattaku. Haka
ko akayi, Baba Liman yaje neman auren
Khadi ma Umar, basu wani samu
Matsala Baban Khadi ba ya amince. Nan
suka zuba kayan mun gani anaso, da
kud’in gaisuwa dubu 2k, Malam yaki
karba yace sunyi yawa, amma Baba
Liman ya dage sai da ya karba. Da
murna yashiga gida, a zuciyar shi, yana
mai cewa tabbas Khadijansa zata huta,
don da alama Umar d’an manyan
mutanene, kuma zai riketa da AMANA.
da murna ya shiga gun Gwaggo, cikin
zak’uwa takaleshi “Malam lafiya naga
sai farin ciki kakeyi?. Hmm kedai bari
kawai, ina cikin farin ciki, mik’omata su
gidan goro da catoons d’in minti yayi,
tare da d’aura mata damin kud’i akai,
ido ta zaro su waje, “Malam wayan nan
kud’in fa da kayan fa?. Cikin murmushi
yace”na Khadijat ne, kud’in aurenta.
Jakar uba! Ina bazai yuba, ina na Beeba
ko Rabee’atu?. To ba a gidan nan za’ayi
wannan abun ba, sai dai ko inda Beeba
ne. Malam yayi dariya yace”Hauwa
kenan wai meysa ba kya boye
hassadanki a fili, ae ni na d’auka Khadi
da Beeba da, Rabee’at, duk d’aya suke a
gunki?. Allah ya sauwake, nawa-nawa
ne. Kuma wannan auren bazai yuwuba,
sai dai ko in zaka kawo na Beeba sai a
had’a. Shikam dariya ta basa, don suk
tagama fita a hayyacinta, ya d’ibi kayan
ya kai d’akinsa. Khadi najinsu amma
duk ta damu da taji wa Malam zai
had’ata aure da shi?.
Malam ne ya shigo d’akinta, ya zauna a
kujera, cikin nutsuwa ya kira sunanta, ta
amsa, sai da yamata nasiha, kamar
yanda ya saba, tukun ya saida mata,
Umar ya kawo kayan ,yagani yana so,
ina fatan kin amince kina sosa?. Shiru
tayi, daga yanayinta ya gane ta amince,
albarka ya samata ya fita.
Washe gari Dr Umar yayi wanka sa, yayi
kyau sosai, sai da yabiya Sahad ya mata
shooping mai yawa, tukun ya nufo
gidan, yaro yasamu ya aika ta fito. Cikin
nutsuwa take takawa, tana sanye da
hijab ash yamata kyau, hannu tasa a
aljihu yana kare mata kalo. Da sallama
ta karaso bayan sun gaisa, yace”gimbiya
Khadeejatu, murmushi tayi yace kali
nan, tana d’ago fuska ya kashe mata ido
d’aya, tare da d’aga mata gira, duk sai
taji kunya ya kamata. Haka sukayi
hiransu a zaure, sai dab zai tafi ya d’ebo
mata, kayan saya mata, godia ta masa
har zata tafi yace”tsaya barin yi
surprising d’inki, murmushi tayi. Yace”
pls close ur eye, ba musu ta rufe, ” miko
hannuki, bata komai ba ta mika masa
tana murmushi, wani zobe ya ciro sai
kyali yakeyi, ya sanya mata a hannu,
nan take hannuta ya d’au kyalu yana
haskawa. Kiss ya kaimta a hannu, sai
sukaji, la ha ila ha illalahu, uhu jama’a
da sauri Gwaggo ta damke su duka. Ta
kwalala jama’a ku kawon d’auki na
kama yan iska yau. Ihu take kamar
mahaukaciya, Khadi ko duk jikinta sai
bari yakeyi, nan take hawaye ya fara
zuba, Umar ko don takaici kasa motsi
yayi.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» YAYA DA DUKIYA.... 91-100
YAYA DA DUKIYA.... 91-100
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment