New Post

Saturday, 1 April 2017

AMANA TA CE 14

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
  
14                             
Bayan sunyi sallah isha’i suka dan yi hira kasancewar lokacin damina hadiri ya hadu aka soma iska, dole yasa suka shiga dakunan su don bacci, ruwa akayi sosai washe gari da safe bayan sun karya ne, Malam yayi shirin zuwa gona nan Ammar yace zai bi shi suka tafi tare, inna da Auta sukayi aikin gd.
Haka rayuwan su ya kasance acikin kauyen cikin kwanciyan hankali, yau kwanan su 10 kafar Auta har ya warke, Ammar ma ciwonsa ya bushe har yayi bawu, nan yasoma tunanin mafita don zamansu kauyen kaduna sam baiyiba, don marasa imanin nan suna sanin yana cikin kauyen to zasu iya turowa a kashesu baki daya, malam ya samu ya masa baya ni yana so su kara gaba don in mutu nen nan suka samu lbr zasu iya turo wa a kashesu malam yace hakane jiki ba kwari ya dau ko yan kudinsa da ya tara na kayan gonan da ya sayar ya basu yace suyi guziri inna kam da taji zasu tafi har da yar kukanta don sun shaku auta ma tayi hawaye, washe gari alhamis suka fito da ga kauyen nan suka shiga motar zuwa rigiyar malam wani kauye da ke jahar bauchi, a cikin motar suka zauna shiru ba mai magana sai yan motan da suke hira duniya.
         Haka har suka iso wani kauye wai shi na bardo, nan yaga ana sauka kawai sai yace bari su sauka gurin nan suka sauka, koda suka sauka gefen rumfunan garin dake bakin hanya ne ya sayo musu fura da nono roba biyu ya ba ma zee ta amsa, tafara sha kenan sai ga hawaye, ammar na ganin haka yace Auta hakuri zakiyi shi rayuwa haka take yau dadi gobe ba dadi mukasance cikin gode ma Allah, sai ya kara wada yar mu cikinta yayi sanyi amma takasa shan nono, wai ita ce yau a titi a kuma kasuwa take cin abu, rayuw kenan Allah ya jikan su dad, ganin taki sha yasa Ammar yakasa sha shima, don baya kaunar ganin zee cikin tashin han kali, nan2 sai yashiga damuwa.
haka suka bar gurin suka dawo gindin wata bishiya suka zauna, lokacin sallah yayi ya nufi masallaci, yayi sallah dake a gefensu yake bayan ya idar ya dawo auta tayi alwala ta shinfuda dan kwalin zanin da inna ta fata ta daura, tayi sallah, haka har dare yayi koda aka watse gashi basu san kowa ba, Ammar ya duba musu gurin wani mai shayi da benci a gun nan ya hada ma auta kwaya biyu yace ta kwanta, haka ta kwanta idonta na zubar da hawaye, tabbas tasan ammar ne kadai ya rike iyayenta da gsky, Allah ya saka masa da dawai niyar da yakeyi da ita, Allah ya jikan iyayenta da nasa Ameen, Ya Allah ka bani abunda zan saka ma Ammar da shi, kuka ne yazo mata marar sauti haka tayi mai isarta daga baya tayi shiru, ammar ko kasance wan benci biyu ne a gun mai shayi ba wanda zai kwanta yasa ya dan zauna ya jingina da jikin falangen gurin shayi haka har bacci ya daukesu.
           Cikin dare misalin karfe daya da rabi, cikin bacci Ammar ya rika jin ihu daga nesa tun abun na nesa har ya matso kusa sai auta ma taji ta tashi, ihun yayi yawa gashi gudu sukeyi sai a lokacin yaji ana cewa barawo barawo, yace ma auta ta tsaya kar ta fito jikinta sai bari yakeyi nan ya fita itakuma tana lekawa, aiko yana fitowa sai ga wani tutum da gudu yabi bayan gurin shayi ya gudu, ana haka sai ga mutanen sun yi kansa suka nan suka fara dukansa suna shine barawon, auta na ganin haka tafito da gudu ta na ihu, wayyo Ammar dina ba barawo bane, wayyo dad kuzo ku kuga halin da muke ciki zasu kashe shi kansu tayi gadan2 tana so ta kutsa, da kyar ta samu tashiga dai2 wani ya kai masa duka da dorina kenan ya sauka akan Auta nan tasaki wani razanen kara.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts