AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
26
Luuu ta tafi zata fadi cikin ikon Allah ta rike karfe matakalan benin bata kai kasa ba duk jikinta sai bari yakeyi amma ta gode ma Allah da ya kareta yasa bata fadi ba kasancewan ba wanda ya gansu wani kalon warning munayshat ta mata kafin ta wuce ta sauka ta karasa table auta jikinta yayi sanyi sosai nan taji wani sabon hawaye yana shirin zubo mata kamar zata fasa sauka sai ta tuna hajiya ce ta kirata in bataje ba ta kyauta ba a hankali ta sauka ta hango su a dinin cikin nutsuwa ta karasa sai da ta gaida hajiya mamu sannan kausar da fara a ta amsa munayshat kam wani sako ta amsa mata ta gefen ido nan ta sunkuyar da kai hajiya mamu tace yata kisaki jikinki ki dauka kina gd ne ki daukeni tamkar mum dinki ga aunty ku kausar nan sai wan nan sis dinki Munayashat muna hada ido ta sakar min harara to na amsa ma hajiya na mata godiya nan mukaci abinci bayan mun gama munay ne tafara tashi ta nufi dakinta kafin hajiya nan kausar tace ya karin hakuri nace Alhamdulilah tace bakomai mun zama daya ki dauke sis dinki kai na daga mata nan tace da safe zamu fita sai ki sai abun da baki dashi to na amsa nace Aunty Kausar sai da safe tace Allah ya kaimu a hankali na haura sama gun dakina kamar munafuka ina shiga na kwanta ina tuna irin tsanana danake hango irin tsanar da munay take min a idonta nan naji wasu sabin hawaye suna zubo min kofar naji an turo da sauri na daga kaina munay na gani fuskanta ba ko alamar anuri nan gabana ya fadi, kafarta daya ta daura akan gadon daya kuma na kasa ya tsanta ta nunani da shi kee duk randa naga kin nuna shigewarki a cikin gd nan sai kin raina kanki san nan ke zakina gyara min dakina da wanki under wears dina da nawa san nan kika kuskura kika fada ma mum nasaki wayan nan aiki ko Aunty Kausar sai kin raina kanki san nan bana son kina shige ma Ammar don ba tsaranki ba( jama’a kutayani jin karfin hali anan harda kashe kamar ba tare ta gansu da Ammar ba)
Kuma bana son in ina falo kina yawan zuwa kinji ko idan kika kuskura kika tsallake doka daya to zaki gamu dani sannan kika fada ma Ammar wlh wlh wlh kinji sau uku na rantse sai na kulla miki sharrin da bazaki iya warware ba sai kowa ya tsane ki kuna jina ko cikin rawar murya mai shirin kuka na daga kai wani harara ta sake min da baki na miki magana ko da kai nan nace da baki tace to da baki zaki amsa min nan nace mata to ta rike kunne na in kunne yaji jiki ya tsira kai na girgiza mata kafin ta sakar min wani rankwashi wanda har kwakwalwan kaina sai da naji shi.
Ammar ko ya na kwance sai juyi yakeyi duk ya damu da kewar auta wanda in da sabo to ya kamata ace ya saba don baya ganin wata mace sai ita hakan yayita sakawa da kwancewa ganin ba zai fiddashi ba yasa ya dauro alwala ya soma nafila daga nan yasoma rairo karatun al-qur’ani mai girma da muryansa mai dadin sauraro dake yana da hadda akansa abun sai wanda yaji(ya Allah ka azurta mu da ilimi mai albarka da amfani amin) sai da yayi adu’o’i mai yawa kafin ya shafa sannan ya kwanta yana mai tunanin abunda ya aikata a ranan na alkairi da istigifari har bacci ya daukesa
Zee auta ko duk da AC dake dakin bai hanata zufa ba sai gumi ke keto mata tana kuka marar sauti wayyo Allah na yau nayi rashin iyayena yau gani cikin kunci kun tafi kun barni ina ma da zanbiki yau na fada rayuwan da bansan wata irin kunci zanulyi ba dad dina ka tafi kabarni wayyo Allah na ka kawo min agaji.
Saturday, 1 April 2017
Home »
» AMANA TA CE 26
AMANA TA CE 26
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment