AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
16
Kuka take sosai ammar ko motsi baiyi ba nan takara jin natsara su baba sani suka jefasu cikin irin wan nan halin, wani bawan Allah ne mai tausayi ya dawo yace bai war Allah daga ina kuke, cikin kuka tace ka taimaka min dan uwana ya tashi shikadai ya rage min an kashe iyayenmu, nan kukanta ya tsananta cikin tausaya wa yace ki tsaya tai mako daya zan miki yanzu ga gidan mai gari can barin je na kirashi da gudu ya tafi ko da yaje ya jima yana buga kofar kafin aka bude, masa, mai gari ya fito suka gaisa nan yasa sai damasa cikin damuwa mai gari ya dauko garensa ko da suka zo har lokacin ammar bai farfado ba, hakan yasa suka daukesa zuwa asibitin garin nan aka bashi agajin gaggawa, bayan sun dan masa treatment ne suka shin fidesa akan yar gadon asibiti, auta ko in banda kuka ba abunda take, bayan ansa masa ruwa mai gari ya musu sallama akan da safe zaizo duba su, auta kasa bacci tayi ga haddiri ya hadu nan akara walkiya da sauri ta haye karamin gadon duk tsoro ya ci kata baran data ga wajen asibitin jeji ne, nan ta kan kame ammar sosai hawayen ta na sauka a akan kirjinshi cikin barci yaji an kan kamesa, a han kali yasoma bude ido yaga duhu da kyar ya iya daga hannunsa yaji auta ne nan kuma yayi kokarin mikewa kansa ne ya masa wani nauyi ga sara masa da yakeyi, a hankali ya shafa kan yaji bandeji ne an daure, sai a lokacin ya tuna mai ya faru hawaye ne yasoma zuba masa shima tabbas yasan suna cikin wani yanayin da Allah ne kadai zai fiddasu.
Auta jin alaman na motsa hannu yasa da sauri ta shafi fiskansa nan taji hawaye a hankali ta daga hannun ta tasoma share masa hawaye tana cewa kayi hakuri Allah zai saka mana kaji kuma Allah yana tare damu yaga halin da muke ciki ba zai bar mu haka ba, nan ya karajin jikinsa ya mutu ga auta da ta kwanta masa ajiki bai san lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ba, har azuciyansa yana son auta ko da aure zatayi ba iya bayar ta ga wani ba don bai son wani yaci Amanar da dad ya basa ko in auta tace bata sonsa to dole ya hakura don ba zai takura ta ba, gwanda ya shiga ko wani irin hali ne da ya sata a damuwa.
a hankali ya kara kan kameta a jikinsa wanda sai da itama taji wani shock ya ziyarci jikinta ajiyar zuciya tayi ahaka suka kwana yau kam bacci mai dadi tayi ajikin Ammar wanda rabonta da ta yi tun iyayenta suna da rai, sai da asuba ta mike da ta fiti kofar asibitin in da taga randar ruwa ta diba tayi alwala ta shin fida dan kwalinta tayi sallah,
bayan ta idar ne ta zo da ruwan ammar da kyar ya iya tashi sabida jikinsa yayi tsami tana zuba masa ruwan yayi alwala yana kwance yayi sallah don kansa ya masa nauyi.
Sai da gari ya waye sosai gurin karfe 9:00 mai gari yazo duba sa da yar kununsa a kwanon sha da kosai nan suka gaisa bayan sun gaisa ya ke tambayan su mai ya kawo su gari da har zasu kwana a kasuwa nan auta ta basa lbr ya tausaya musu sosai, nan ya musu sallama akan darana zai zo dubasu auta haka take kula da ammar dan kudin da malam ya basu shi suke yasan abun da ya dan musu su ci, kwanan Ammar uku a asibiti aka sallamesa jikinsa ya warke sai tabo, ko da suka fito a asibiti gdan mai gari ya nufa ya masa godiya san nan yace yana so su kara gaba don yana son cikin birni inda zai samu sana’a yayi da karfinsa, nan mai gari ya ce yanzi kana fita sai garin bauchi shine babban gari, nan yaji yana son garin don ya dade yana jin lbr garin bauchin yakubu ga Addini ka mutunta mutum ga iya karama baki, ga masa waina sai wanda kazaba, nan yayi godiya mai gari ya rakasu suka shiga motar bauchi.
Saturday, 1 April 2017
Home »
» AMANA TA CE 16
AMANA TA CE 16
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment