YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-91~95.
Karfe shidan yamma, jirgin su ya sauka,
acikun garin Abuja. Bata bata lokaci ba,
ta sake shiga jirgin Kano, ko da ta iso,
anyi sallah magriba, ana shirin yin
isha’i, taso yau taje taga yar gidan uban
waye, Dr Umar ke sonta, kuma da me
tafita da shi, da har zai aureta, tabbas
yarinyan sai ta raina kanta, washe gari
da had’a security dinta, wankan kece
raini tayi, ta kira kawarta, Zulaihat
tace”Zuly ki shirya kizo, zaki rakani,
wani karamin unguwa, wai shi Dakata.
Cike da tsokana Zuly tace”kawas mai
zaki dakata acan, nan Sakeenat, ta sanar
mata da komai, Zuly tace”ban minti
kad’an ina zuwa ko ku biyo ku d’auken.
Haka akayi, suka dauketa, cike da rashin
mutunci a fuskokinsu.
Khadi ko wanka tayi, sabi da tasan yau
weekend, Ya Umar d’inta zaizo, tayi
kyau kamar wata amarya. Suna tsakar
gida suna tad’i’ ita da Beebah
kasancewan, Gwaggo ta tafi gidan
kawarta, shiyasa suka sami freedom yau.
Tun daga nesa suke jin, wi wi wi wi,
kukan jiniya alamar, wani babab yazo
unguwan, har sai da aka zo qofar
gidansu, tukun kukan ya tsaya, cikin
mamaki suna jira suji maisu shigowa,
Khadi tace”Beeba kardai police ne suka
zo gidannan?. To wayayi laifi?. Tana
wannan tunani ko taga masu bakaken
kaya, suna shigowa cikin gidan, nan take
hanjin cikinta ya kad’a.
Sai da suka shigo, sun tsatsaya musu,
wasu yan mata ne biyu, su ka danno kai
cikin gidan, kalo d’aya zaka musu ka
gane, sun san bariki, idonsu abud’e
yake, ga fiskansu ta sha man bleaching.
Cikin isa da taunar chewing gum, ta iso
gaban su, sai da suka musu kalon, sama
da kasa, kafi ta juya, ta kare ma gidan
kalo. A tare suka kwashe da dariya, Zuly
tace”kai yayan talakawa, a cikin ku
waye Khadi ko Khadija, shiru ba wanda
ya bada amsa. Cikin zafin rai suka sake
magana, da kyar, Khadi tace” gani nice
Khadi. Sai da suka kaleta sama da kasa,
sai da gaban Sakeenat ya bmfad’i don
sai yanzu ta lura da Khadi, tabbas
yarinyan ta had’u, dole Dr Umar ya
makance a sonta. Daurewa tayi, ta fara
yi ma Khadi, “concrete warning, duk
randa naji ance kin kula Umar sai na
muki rashin mutunci, sai nasa an
d’aureki, tabbas duk halin naka-naka ne,
mai rashin kunya ma wataran yana da
rana. Beebah da Khadi kasa magana
sukayi, Rabee’at dake bacci a d’aki,
hayanayi ya fitar da ita, jin yanda, aketa
zaginsu, dana iyayensu ta karaso da
gudu, ta kalisu Sakeenat, ta sama da
kasa, ta nuna su da yatsa, tace”banza
mai fiskan biri, kin wani sha bleaching,
waye ke?. Da har zakina zagin iyayena,
nan Rabee’at tashiga sauke musu,
kwandon rashin kunya.
Dr Umar yayi wankan sa ya nufo, gidan
su Khadi, tun da ya shigo unguwan ya
fara ganin motoci, har ya iso qofar
gidansu Khadi, nan yaga security, gidan
gwamnati, da sauri ya fito daga mota, ya
kira wani body guard, tambayesa mai ya
faru, nan yake basa bayani, Sakeenat ne
a ciki, da sauri ya shiga gidan, dai-dai
likacin da, Sakeena ta harzuk’o zata
mari Rabee’at da sauri Khadi, ta shiga
tsakanin su, sai jikayi tasss!!, karan
saukan mari a fiskan Khadi, kafin ta
motsa, sai nasojin wasu karan tass!!
Tasss!! Tass!! Gar sau uku, Dr Umar ya
mari Sakeenat. Ya juya ya kali security
d’in, da sauri suka bar cikin gidan. Cikin
fushi ya kali Sakeenat, Yace” kee waya
baki izinin zuwa gidan nan?. Duk randa
na k’ara, ganin k’afarki sai kinji
ajikinki, ki kuma sani Khadeejat ta miki
nisa, itace uwar ‘YA’YA Na, ita nakeso,
itace rayuwa, farinciki na, in part
rayuwata bazatayi dai-dai ba in ita,
banza sakarya, ko ana soyayyan dole
ne?. Nace bana sonki bana sonki, ba
kuma zan soki ba. Cikin b’acin rai yazo,
rik’o hannu Khadi yace”My wife kiyi
hak’uri dan Allah, hannu yasa, ya share
mata hawayenta. Ya rike hannuta, ya
Sakeenat da bakin ciki ya isheta, kaman
ta shid’e a gurin. Yace”kee Sakeenat!
Kinga wannan ta fi minke komai, itace
mahad’an rayuwa ta, tafiki kamun kai,
da nutsuwa, in kin…… Da gudu ta bar
cikin gidan tana kuka, wi-wi da hawaye.
Tabbas yau taja ma kanta raini agaban,
wayanda take takasu son ranta, yau
Umar ya mata haka?. Tana fita mota
tashiga, Zuly ma ta biyota, rake suka bar
unguwan.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» YAYA DA DUKIYA... 91-95
YAYA DA DUKIYA... 91-95
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
0 comments:
Post a Comment