New Post

Saturday, 1 April 2017

AMANA TA CE 38

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam

38                            
Ahyan bakaramin damuwa ya shigaba, yau yasan mum dinsa tayi fishi dashi bai kuma kyauta ba, dole yaje ya bata hakuri, da kyar ya iya shan tea ya sha magani ya koma ya huta.

         Yana isa asibiti ya gaida su H mamu, san’nan yanufi gun Dr yake tambayart cikin Zee tace d sauki, dakin ya dawo ya zauna a gefe, ya zuba ma auta ido ko kyaftawa baya yi,wayar H Mamu yayi ringin tana dagawa taga munay ce, da kamar bazata daga ba, amma sai ta dauka daga daya bangare akace, “hello mum ya kk? Mum duk abunda bros ya miki ya kamata kiyi hakuri ki tausaya masa, kizo ki ga jikinsa, a kan wan”nan yar da ba’a san asalinta ba, sai wai2 amma ki kyale dan ki wanda kikeso” wani tsawa ta daka mata nikaina sai dana tsorata, wato munay kema bayansa zakibi ko? Kuma kar in kuskura inji kin kara zaginta ni baruwana da shi, har sai ya gyara halinsa tukun mtss ta kashe, ammar har rashi saida yaji taisayinta don tacika uwa ta gari ba mai son kanta ba, sai yau yaji kara sonta a matsayin uwa, “Allah ya biyaki mum”, kausar ma jikinta duk yayi sanyi ammar yayi karfin hali yace mum kije ki dubasa da jiki, duk abunda zaiyi bazaki taba kankare alakar kuba, “hannuka baya ruba ka yanke ka yar” dan kine dan haka adu’ah shine mafita, taji dadi amma bata nuna ba sai kawar da kan ta tayi kamar bata jishiba.
Zee ce ta fara motsi kada2 sai tasaki wani kara take sukayi kanta dukansu, ihu take tana kiran sunan Allah, sai kuma ta soma cewa Ammar…. ammar….. Ammar kazo ka kwace ni zai kashe wayyo Allah na, wayyo mum kun tafi kun barni, ammar da sauri ya je ya kira Mrs Abdul da sauri sukazo allura ta mata take bacci ya sake daukarta, Mrs Abdul tace karku damu zata farka cikin hankalinta, ajiyar hrt ammar yayi godia ma Allah dr tafita ta basu gu.
        Sai can dare ta farka, taga mum nan ta soma tuna mai ya faru kuka tayi sosai, mum na lalashinta, tea ta hada mata tasha ta kai mata ruwan wanka tayi taji dadin jikinta kafin tayi sallah.
        Ahyan kuwa an sallamesa cike da tsoro da zullumi ya shiga gd, da farko kam yaki shiga sai da munay tashiga ta duba masa ko mum na’nan, taga batanan tukun ya shiga gidan.
         Kausar jin munay na gd yasa tadawo kuma hauwa mai aiki ta dawo yau, tukun ta koma gd, ya rage h mamu ke ajikinta, gsky ta gwada musu kulawa.
Sai can yamma ammar yazo yana gun cuku-cuku neman shagon da zai dan sari kaya yazuba aciki, ya fara business da yan kudin da ya tara na albashin da yake samu.
Sai da ya gaida h mamu tukun ya yima auta ya jiki? ta amsa da sauki, sun dan taba hira kafin yace ma mum yana so zai roki gafaranta don ya mata laifi sai da ya bata hakuri kafin yasanar mata da hukunci da ya yanke, da farki taso taki akan sai dai ahyan ya bargidan, ammar ya nuna mata ilan hakan san’nan ta amince, sun na cikin hira Mrs Abdul tazo ta basu sallama, kaya suka tattara san’nan ya tsara musu napep suka je gudan sai da h mamu ta gyara ma auta daki duk da a gyare yake kafin ta musu salama akan gobe zata dawo.
         Ko da ta koma gd tasamu ahyan ko kalon inda yake batayi ba, da gudu yazo ya rike kafarta yana bata hakuri tureshi tayi ta wuce idonta cike da kwalla, “a zuciyarta tausaya masa amma sai ta gwada masa kurensa”.
Washe gari sukaje da kausar suka duba auta tare da kayayaki bayan sun dade suka musu sallama suka dawo, washe gari ammar ya tattara yan kudin h mamu da ya sani da wasu ta kardunta ya kaimata yabata hakuri sam bata so ya bar yi mata business ba don yaron yana da “AMANA” amma ba yanda ta iya haka ta hakura nan ta dibi kudi mai yawa tabasa yayi godiya ya fito kenan suka tsaya da mai gadi sunyi hira sosai sai kusan 9:00 ya nufo gida ya sai musu nama da yan kayan motsabaki abakin titi mai mashin ya ajiye shi ya ajiye shi yazo shiga lugun gd da suka koma wasu yan’isa suka tsaresa harda wukakensu suka nuna kudi suke nema baiyi musu ba ya basu kudin da aka bashi, har sunce ya tafi dayan yace kai tsaya ban…..
Taku mai kaunar ku a kulum 
Rash Kardam 

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts