New Post

Tuesday, 18 April 2017

'YA'YA DA DUKIYA... 141-145

4:55PM, 5/25/2016] Rash Kardam :
’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-141~145.
Shirye-shirye biki akeyi ba sanya, su
Hajiya Jamila.k’irjin biki, su Farhat da
Queen Neena takanas suka koma gidan
Hajiya Suwaiba da zama, abunda aka
shirya za’ayi ran Alhamis kamu, sai
Jumma’a Walima da daddare kuma
dinner, washe gari asabar yini. Komai
ya tsaru yanda ake so, yau ne ranar da
za’a fara Kamu, da yamma ko kwaye sun
shirya, har an kaisu gun jiran isowar
Amarya ake, ba’a dade ba kuwa ta iso
cikin wata lafiyayiyar mota, tun dana
zuba ido ma Khadi kasa d’aukewa nayi,
gaskiya tayi kyau, duk yan guri sai yaba
kyanta suke, taro yayi taro, komai yatafi
yanda akeso, sai kusan shida suka gama
kamu, daga gun gidan, Hajiya Suwaiba
aka sake kaita.
Washe gari akayi walima shima tsaru
daddare kuwa sukayi shirin dinner.
Hajiya Suwaiba ta bada umurni akai
Amarya gidansu daga can za’a wuce da
ita Dinner har a kaita gidanta, wannan
umurnin Mum ne.
Masu karatu in bakwayi bamu guri,
tundaga nesa na hango motoci jere suna
d’eban mutane, sai da aka gama diban
kowa, na hango wata maroon d’in lemo
zeen ta perker, su Gwaggo da’ake leke,
baki tasaki tana kalo, don tunda take
bata tab’a, ganin irin motarba. Nan
akace afito da Amarya Inna Yalwa ce ta
rakota, ohoho sunan wani kalma waishi
sorry!! Masu karatu karkuga Khadi, in
har nace zan iya tsara muku kyan da
tayi, wayana ba zai d’auka ba. A hankali
suka isa jikin motar tashiga, ana tayar
da motan taji an rik’o hannuta, a razane
ta juya Umar ne yaaha kyau.
Koda suka isa gun dinner duk wanda ya
gansu sai ya yaba, haka taro ya kare
kowa cike da murna.
Da safe Malam ya kira Khadi, ya mata
nasiha, yan’uwan Mamanta suma nasiha
suka mata, Gwaggo da k’afarta tazo tana
kuka ta roki Khadi yafiya, Khadi tace”
ba komai ta yafe mata.
Da daddare aka d’au Amarya sai gidan
Umar niko Rash nace”fatan alkairi.
Gwamna gida mai ji da kyau ya bamasu
Malam, yace”karsu d’au tsinke acikin
nasu. Haka ayi suka koma, tsakani Beeba
da Dr Abdul ko wata soyayya ne mai
cike, da qauna sukeyi ma junasu,
Gwaggo yanzu kamar bata gidan don
Albarkacin Khadi takeci.
Kwanaki sun tafi shekaru sun sud’e,
koda naje gidan Khadi na hango ta da
yaranta, sun girma suna gudu ko ina,
Khadi yanzu ta dawo cikakoyar mace
mai aji da kamala.
Gwamna ya biya ma su Gwaggo da
Malam aiki Hajji suka tafi.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts