New Post

Saturday, 1 April 2017

AMANA TA CE 44-45

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam

44                        
    Wayar sa ya haska ta da ita tayi ky’au kamar ba Auta da ya sani ba, a hankali ya soma bin fuskan da kalo har yazo dan k’aramin bakin ta da yasha janbaki maroon, idonta ya haska yaga ta lumshe su wani kyau na musamman ta kara masa a hakan, take yaji wani farin ciki ya lulubesa yau Autarsa ta dawo mallakinsa YAR’AMANA sa, a zuciyara yace”ina ma da su dad suna yare suga wannan rana nasan zasu fi kowa farinciki. Ya Allah kajikansu kamusu Rahma Ameen.
Kashe wayar yayi ya kara matso da fuskansa har Auta na jiyo numfash’insa, nan take yasoma jin wani abu na tsirga masa, bakinsa yasa cikin nata yafara mata wasu salon, dai-dai lokacin suka iso, a hankali ya matsa gefe jiki ba kw’ari.
Duk yan dinner sun shuga su Ammar kadai ake jira, sai da su Ammar suka d’au lokaci kafin suka fito Ahyan na rike da hannu Kausar gsky sunyi ky’au. Ammar yace”amana afuwa mun bata muku lokaci. Murmush’i Ahyan yayi yace “mush’iga kawai don lokaci na kara tafiya. Ahayan da Kausar sune a gaba sai Ammar da Zainab, tunda suka saka kafa acikin hall d’in na saki baki ina k’alon Amaren nan, gsky Allah yayi halita a gun baran na bayannan wato Ammar da Auta. Amrah ce ta zungureni kai Rash wannan wani irin kalo ne kamar zaki cimyesu, hmmm nace”My Amrah ke dai bari kawai Amaren ne sun tafi dani sun had’u sosai gsky sun dace da junansu.
High table din nake bi da kallo gefen Ammar Auwal ne da Munay sai kujeran kusa da su Jidda da Ghali(Haughal) na gani, ko da na kali gefen Kausar Raheenat da MY na gano sai wata kawar kausar da saurayinta.
Kid’a ne ke tashi a gun ko ina ka duba jama’a ne suke zaune kowa da masoyinsa ga Mrs Umar ma da Sojanta sai luv suke sha. ‘Daya daga cikin abokan Angwaye ya bud’e taro da addu’a, kafin aka soma gudanar ta dinner sai da suka danci abun motsa baki, aka umurci Amarya Kausar da Angonta suka fara sauka kid’a aka sake musu nan fa yan liki suka taso bayan sun taka ne, aka umurci Zainab da Ammar su fito, tunda aka kira sunasu Auta ta lafe ajikin Ammar bata son sauk’a, Ammar ya janyota jikinsa kai ka dauka wani zai kw’aceta ita ko ta lafe ajikinsa, cikim nutsuwa suke sauk’owa abun gwanin burgewa ohoho masu karatu naso ace kunje gun dinner nan don duk lbr da zan baku na Ammar da Auta zai d’auke mu lokaci mai tsawo.
Waka aka sake musu kan kace me yan likin Ammar da Auta sum taso suka fara musu har suka zo tsakiyar hall din, a hankali Ammar ke ta kawa amma Auta taki rawa ganin haka yasa ya kara matsowa kusa da ita ya mata cakulkuli aiko ta kw’ato jikinsa nan yafara ju-juya ta, in ka gansu kw’a d’auka salon soyyansu suke zubawa.
Haka tarin dinner ta kare cike da farin ciki suka dawo gida, kyar Ammar ya bar Zee tash’iga gd.
Taku a kullum mai k’aunar ku
  
Rash Kardam 



AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam

               45         
Hajiya Mamu taso akai amare yau Amma dare yayi, haka ta hakura.
Da safe bayan sun karya ta zo d’akin Amaren da kayan fruit ta basu da wani abu kowacce cikin kofi d’aya, ni Rash nace “ko miye wannan oho!?.
Haka suka yini Mum sai d’irka musu abubuwa takeyi tun daya yamma ta hada su a daki d’aya ta soma musu nasiha gami da basu sirrikan saye zuciyar miji.
Da dad’dare aka zo d’aukan Amare sunsha kuka kam da ky’ar aka fita dasu, kowacce akayi kaita gidanta.
Abokan Ahyan ne suka raka sh’i saida suka dan tsokani Amarya, da yan barkw’acin su kafin suka masu sallama da fatan samun zuri’a na gari suka tafi, nima fatan alkairi namusu nafito tare da jan musu gate d’in gdn. Na nufi gidansu Auta don inga wainar da ake toyawa ta.
Ina isa na tarar da Auwal ne da Saeed suka rakash’i, nasiha sosai suka musu da yan shawarwari kafin suka musu sallama suka fito, Ammar ya musu rakiya bai wani dad’e ba ya dawo gefen Auta ya Auna tare da furta Alhamdulila!. Agogon dake hannusa ya cire yace Zainab kije kiyi alwala muyi nafila mu gode ma Allah da wannan babban ni’ima daya mana. Mikewa tayi ta nufi toilet ta d’aro alwala bata dad’e da fitowa ba shima ya fito suka suka tada kabbara. Raka’a 2sukayi kafin ya dafa kanta yasoma karanto addu’ar da in mutum yayi Amarya ko sabon abu zaiyi kafin yafara amfani da abun. Ga addu’ar kamar haka”Allahummah inni as’aluka khairi ha wa khaira ma jabaltaha alai, wa ‘a’ uzubika min sharri ha wa sharri majabalta ha alai”. Ma’anarsa sh’ine Ya Allah ina rokonka Alkairinta da d’abi’anta akansa, kuma ina neman tsari da sharrinta da sharrin da ka d’abi’antar ta akansa.( yan’uwa yana da kyau mu runka yawaita yin wannan addu’a yayin da mukayi sabon abu, Addu’ar tana da matuakan amfani, Allah yasa mudace Ameen).
Sai da ya gama karantawa tana amsawa da Ameen har ya kai karshe, kitchen yaje ya d’auko musu plate ya saka musu kazan da fresh milk mai sanyi yasa musu a kofi, Auta ta kasa sakin jikinta da sh’i, naman ya d’auko yazo dai-dai bakin ta ta kawar da fuska tana yar murmushi kasa-kasa, cikin zolaya ya dawo ta gefen da ta mayar fa fuskanta cike da tsokana yace” Amarya yau kunyata kike ji?. Uhmm ta fada tare da sake mayar da guskanta ta d’aya barin mikewa yayi cikin shauk’in so da kauna yace”baringa ta ina zamu fara, ita ko sai zi-zilewa takeyi.
  
Rash Kardam 

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts