AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
31
A hankali ya ke saukowa sanye da 3quater da yar riga mai gajeren hannu, ya jimma a tsaye yana kallonta wannan wacece da bai taba ganinta ba ko ita ce Zee din da mum ke fada gsky yarinyan ta hadu ba laifi wani juyinda tayi a rawan sai da yasa Ahyan hadiye yawu don wannan tana daya daga cikin irun matan da ya ke so ta hada koma2 gyara tsayuwa yayi yana kallinta don baison ta bar rawan,
Sam ita bata san da mutum ba tsakaninta da Allah take tika rawa,
Dai2 nan Ammar ya shiga kallon ta yakeyi cike da so da kauna dake yasan ita mayyar wakokin india ne ganin auta cikin farin ciki yasa shima ya tsinci kansa cikin farin ciki sai a lokacin ya lura da ahyan da yayi tsaye yana kallonta nan take ransa ya baci kishin sa ya motsa bai san lokacin da yaje ya mata wata damka ba kee baki da han kaline bakisan akwai wanda bai kamata su kalleki haka ba tsaya wa nayi ina masa kallon tuhuma sai a lokacin naga ahyan ya karasa saukowa sai min wani kalo yake wanda ni kaina sai da na tsargu,
Munay ce ta shigo ko sallama babu ganin irin hallin da muke ciki yasa ta nufo ni da sauri kee baki da han kali ne zaki fito cikin irin wan nan shigan duk ta rude kai ka rantse a kwai mijinta a ciki na fito da wan nan shigan nan take jikina ya hau rawa da gudu na haura sama ammar kam dakinsa ya koma ransa duk a jagule ahyan kuma bayana yabi da kallo yaga duk yanda illahirin jikina yake motsawa tabbas dole yasan abinyi akan wan nan yarinyan.
Wacece Hajiya Mamu?,..
Asalin sunanta Maryam Alkali haifafiyar garin katsina ce aure ne ya kawota bauchi,
Hajiya mamu ta taso cikin kulawa da tattalin iyayenta Alhaji Alkali mutum ne mai karamci da sanin ya kamata yana da mata daya mai sunan Xahra mace ne mai mutumci da kamala shekaransu 2 da aure basu sami haihuwa ba sai da suka shiga shekara na 3 Allah ya basu haihuwar diyarsu ta farko maryam inda suke kiranta da Mamu sai bayanda suka sanu shekara 4 Allah ya sake basu haihuwar fatima haka suka taso cikin kulawa da kaunar juna inda mamu tayi aure ta auri wani shararen dan kasuwa bayan tayi aure da wata 3 Allah ya bata cikin ahyan haka sukayita tattalin cikin har tazo ta haifeshi yaci sunan Ahyan ma’ana Gift of Allah
Bayan shekara 2 akayi bikin fatima itama bayan aurenta da sheka 4 ne ta haifi Kausar kenan kausar yar kanwan hajiya mamu ne tunda fatima ta haifi kausar ta kamu da lalurin rashin lfy bata dade tana jinya ba Allah ya karbi abunsa nan H Mamu ta karbi kausar ta dawi hannunta sai da kausar ta kusa 4 years hajiya mamu ta haifi munay haka taci gaba da kula da yaranta tana basu tarbiya mai kyau mijinta yana kasuwancinsa ka Allah ya sanya musu Albarka dukiya sai haba ka yakeyi kwanaki sunja lokaci ya tafi har ahyan yagama secondary nan Abbansa ya fara shirye2 na fitansa karatu waje yayi hatsari ya rasu tabbas sunji mutuwar nan ba kadan ba bayan yanyi arba in ne hajiya mamu tayi ciki ciku yatafi karatu kasar waje nan ita kuma tani mi aiki tana zuwa sam taki aure don tana kula da yaranta Kausar dake tana kama da mamarta in ka ganta baakace ba hajiya mamu bane ta haifeta ba don suna kama munay da dad dinsu tayi kama sam ita halinta ya fita daban bata son kowa a kusa da ita ga jinkai ga nuna isa kamar yar President.. Lol…
Yawancin kawayenta yaran manya ne bata harka da yaran masu kananan karfi acewarta za a raina ta don kalin kanta take kamar yar gidan dan gwate ….lol…
Saturday, 1 April 2017
Home »
» AMANA TA CE 31
AMANA TA CE 31
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment