New Post

Tuesday, 18 April 2017

'YA'YA DA DUKIYA..... 61-65

YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-61~65.
Sai da ta dad’e kafin, ta d’an tashi,
sannu suke mata, bata iya amsawa ba,
sai da ta huta sosai, Dr Umar ya kaleta,
cike da tausaya, Yace”yan’mata mai yake
damunki haka?. Da har kike irin
wannan tunanin?. Kasacewa komai tayi,
sai da yamata fad’a sosai, Yace” ki tashi
mukauki gida, sai a lokacin ta zaro ido,
kai ta girgiza musu alamar a’a, bayanda
basuyi ba, amma fir taki, daga k’arshe
Dr Umar ya tsara mata Napep, nan ta
bada kwatance gidansu, sai da tashiga
Napep sun d’au hanyan, Dr Umar ma
motarsa yashiga, har yayi hanyan gida,
komai tuna ya juya kan motarsa zuwa
Dakata, gudu yakeyi sosai, cikin sa’a ya
hango Napep d’insu, a baya ya rinka
binsu har suka kai k’ofar gida. Mai
Napep ya tafi, ta tsaya a k’ofar gida,
tana tunani shiga, gashi yamma tayi
sosai, ga yunwan da takeji, da kyar ta
iya shiga gidan. Ganin ta nufi cikin
gidan ya fito daga motarsa yazo dai-dai
zauren.
Assalamu’alaikum ta fad’a cike da tsoro,
kara shiga ciki tayi ganin Gwaggo bata
kusa, da sauri Gwaggo ta fito,”kee
karuwa yar’iska ina kika fito?. Cikin
fargaba da zaro ido, Khadi tace” wallahi
Gwaggo gun d’inki naje. “Karya kike dan
ubakiki, dukanta Gwaggo tayitayi kamar
ta samu jaka.
Dr Umar tun daga, nesa ke jin murtan ta
tana ihu, sai leke yaykeyi, zuciyarsa na
tafarfasa, ganin Gwaggo ta d’auko
muciya, Beeba da ke gefe sai kuka
takeyi, tana bama Gwaggo hak’uri, Dr
Umar dake cikin zaure, ganin Gwaggo,
ta d’aga muciya zata kwada mata, bai
san lokacin da ya shiga gidan ba, rike
muciyar. Gwaggo cikin fushi, d’ago tana
masa kalon raini, daga kai waye ne?.
K’ok’arin fincike muciyar takeyi, Malam
da ya dawo daga tafiya, yaji da sauri ya
k’araso cikin gidan, ganin abunda ke
faruwa yace”Hauwa mai kikeyi haka?.
Nan fa tafara ba Malam labarin karya da
gaskiya, ta d’aura dacewa”Khadi karuwa
ce yar’iska, da sauri Malam ya dafe
kansa, don harcikin zuciyan sa, yaji
kalman ta dake shi. Cikin kunan rai, Dr
Umar yace”wannan sharri ne wlh, nan
ya kwashe abunda ya faru ya fad’a
musu. Gwaggo nan ta tire, “sam ni
banyarda ba, shine ya d’auketa suke
iskanci tare, Malam ya mata kwalon uku
saura kwata, hak’uri ya fara ba Dr
Umar, tare da masa godia. Dr Umar yayi
musu salma ya nufi gida, cike da
jimamin rayuwan Khadi.
Tun daga wannan ranan, Dr Umar
yasamu gurin zuwa, gidan gun Malam
susha hira sosai, wani lokaci Malam ya
turo Khadi su gaisa, sam bainuna musu
ko shi waye ba, kuma bai taba sayan
wani abu ya basu ba. A hankali
shak’uwa ta shiga tsakaninta da Dr
Umar.
Kamar kulum Dr Umar, yayi wanka
cikin manyan kaya, yayi kyau sosai, sai
da ya biya ta, Sahad store yayi sayya,
kaya ya had’a ma Khadi, less da atamfa
da shadda d’inkaku, da su takalma da
jaka.
A hankali yake tafiya, har ya shigo
unguwan, cikin sa’a ya samu Malam na
gida, sai da suka gaisa, ya bud’e boot din
motarsa, buhun shinkafa biyu, na tuwo
dana dafawa, sai taliya carton biyar da
makaroni, harda su maggi star. Malam
dake gefe, ya tsaya yana kalon ikon
Allah. Sai da aka gama shigarwa,
Yace”Umar mai yasa kayi irin wannan
d’awainiyar, kai ya sunkuyar, Malam ae
ba komai, kai mahaifi ne ae. Godiya yayi
masa sosai, dai-dai lokacin, Khadi tafito
Gwaggo ta aike ta, tazo wuce musu, ta
gaida Dr Umar ya amsa cikin kulawa
zata wuce, Yace”tsaya ki amshi sak’onki,
don ina sauri yau, wasu manyan ledoji
ya miko mata, Malam Yace” Umar
d’awainiyan yayi yawa, bakomai Baba
sauri nake, sai na dawo, godiya yayi
masa Dr Umar yaja motarsa ya bar
gidan, Khadi ne tafara shiga cikin gidan
da laida, Malam na biye da ita. Gwaggo
tana ganin laida a hannu Khadi, da sauri
taso zata amsa, ganin Malam tace”yau
samuwa mukayi haka?. Malam yace”eh!
Wallahi wanda ya taimaka ma Khadi ne
yayi mana alkairi, Gwaggo ta dafe k’irji
lokacin ta zazzage kayan ciki, nan fa ta
tsorata, “ae wallahi abunda bazai
yuwuba kenan, wannan k’arya ne.
Malam daman funa furci ka kula shine
ka tsiri kai Khadi koyar d’inki, don kana
son ta had’u, da wanda ya kawo kayan,
mai yasa baka tura Beebah ko Raee’atu
ba?. Sai Khadi, nan tafara tonan silili ma
Khadi, cikin takaici Malam ke kalonta.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts