New Post

Saturday, 1 April 2017

AMANA TA CE 43

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
43
                            
  Munay da Kausar kulum suna hanyan Asibiti a d’an kw’anak’in da sukayi suna zuwa Asibiti Munay tana sh’ish’ige ma Auta ta kuma bata hak’uri akan abunda ya faru baya.
Kw’anan Ammar biyu a Asibiti aka sallame sa, tunda suka dawo Auwal ke dawainiya da su, sam bai nuna gazawarsa.
Yau Ahyan zai dawo H Mamu ta kira Kausar tace”ina son kiyi girki ma yayanki yau zai dawo, ta da’uko wasu k’aya masu ky’au tace kisa wannan zakije ki da’uko sa daga Airport. Cike da ladabi ta amsa tace”nagode Mum Allah ya k’ara bud’i yasa afi haka. Ameen!
Sai da ta gama girki kafin tayi wanka tasa goduwar rigace bakaramin ky’au ya mata ba. Key d’in motarta ta d’auko ta nufi d’akin Mum da sallamarta ta tura k’ofar ta shiga, tace “Mum nagama girkin na jera su a inda ya dace, kuma bros ya kirani yace nan da 40minutes jirginsu zai sauk’a, ina son inje da wuri k’ar yayita jirana.H Mamu tace”to sai kin dawo Allah ya kare, banda tuk’in gan-ganci. Ta amsa mata da to ta fito cikin nutsuwa take tafiya harta isa ABUBAKAR TAFAWA/BALEWA AIRPORT. Bata dad’e da zuwa aka sanar nan da 5minutes Jirgin UK zai sa’uka. Jirgin na sa’uka fasinja suka suma fitowa mik’ewa nayi naje gurin, sai da mutane suka fir-fito can na hango Yaya Ahyan cikin wata bakar Suite yayi masifar ky’au ya kara haske da k’iba,sai ya dawo min tamkar wani bako ciiin zuciyata nake cewa”gsky Yaya Ahyan na karshe ne duk macen da ta same shi taji dad’i,” Ya Ahyan yana matuk’ar burgeni amma kash zai yi wuya na saye zuciyarsa. Ahyan kuwa tunda yake sau’kowa ya ky’alla idonsa a kan kausar sai da ya kusa suman tsaye, d’an shek’ara biyu zuwa uk’u da yayi baya gari, Kausar ta k’ara cika da ky’au tamkar ba ita bace. Hmmm yace”Kausar ina matuk’ar sonki tun kina yar yarinya amma nasan Mum da wuya ta bani ke. Dai-dai lokacin ya iso kusa da ita. Sam bata san ya iso ba saida ya hura mata iska a idonta wani sas-sanyan ajiyar zuciya ta saki, sai alokacin ta farga ya iso kusata ita, watsowa yayi dab da ita har tana jiyo fitar numfash’insh’i, ga shi duk ya cikata da kamsh’in turarensa Ayhan yace”Kausar mai kike tunani haka?. In ka ji yanda ya ke maganar tamkar rad’a zai mata a’cikin kunnenta.
Cikin jin kunya tace maba babu ok! Trolley da ke hannu sa ta karb’a suka sh’iga mota, tun a hanya Ahyan ke satar kalonta har suka iso gida. Munay tana jin tsatuwar mota ta fito da gudu tana oyoyo my bros, tana i’sowa sukayi sharking din hannu, suka nufi cikin gd.sai da Ahyan ya huta Kausar ce tayi serving d’insa bayan yaci abinci ne ya shiga gaida Mum.
Bayan sun gaita H Mamu take tambayarsa Yaya karatu? Alhamdulilah! Yanzu kam mun kammala result yayi ky’au duka suka amsa da Alhamdulilah! Allah ya sanya Al’k’airi Ameen.
Mum tace”Ahyan kaje ka huta zuwa dare ina son ganin ka zamuyi magana, ya amsa da to ya tashi ya nufi d’akinsa da Kausar ta gyara masa sh’i.
Ammar kam jiki Alhamdulilah ya war-ware har ya fara fita, abunka da mai zafin nama. Yana zaune wayars tayi kara Hajiya Mamu yagani cikin girmamawa ya d’aga wayar bayan sun gaisa Hajiya tace”Ammar ya karfin jikinka?, yace da sauki, tace Alhamdulilah! Yau in ka taso daga kasuwa ina son ganinka da magriba, to Mum zan’zo in Allah ya kaimu, yauwa nagode sai’anjima.
Ammar na sallah magriba ya zo gun Hajiya sai da ya gaisa da mai gadi kafin ya sh’iga ciki.
Munay ya fara gani a falo yaukam cikin nutsuwa ta gai dashi ya amsa ta je je kitchen ta kawo masa drink da abinci, tace”barin k’ira maka Mum din, bata jira amsan sh’i ba ta nufi sama, tana zuwa ta sanar da Mum Ammar ya zo H Mamu tace”ki kaisa falon baki can zamuyi magana, sannan ki bi kice ma Yayanku ya same ni acan to ta amsa. Sai da ta fad’a ma Ahyan tukun ta sanar da sak’on Mun wa Ammar, dake ba bak’oba ne falon ya sh’iga ya zauna, sai ga Ahyan ma ya sh’igo hannu ya mika masa suka gaisa, Mum ne tash’igo itama da sallama suka amsa ta nimi gu ta zauna, nasiha ta musu sosai mai sh’iga jiki, sunansu tak’ira d’aya bayan d’aya suka amsa ta d’anyi sh’iru kafin tace”na yanke hukunci had’aku aure da k’anne ku. Cikin razana suka d’ago a tare suna kallonta, sake mai-maita abunda ta fad’a tayi, Ahyan ta kanka zan fara, kasani tun lokacin da yar’uwa ta take raye muka yi al’k’awarin zamu had’a ya’yanmu Aure, ina son in cika wannan burinmu, kuma bin umarni na sh’i zai sa na yafe maka abunda kayi min, don haka na yanke hukunci had’aka aure da yar’uwan ka Kausar har na sanar da yan Sokoto. Ba shawara nake baka ba umarni na baka, ta kai dubanta ga Ammar ta kira sunansa, ya amsa jiki ba kw’ari,tace”Ammar kaima ina ga zaka auri Zainab don tafi sabawa da kai ta sh’ak’u da kai sosai, Ammar a cikin zuciyansa yafurta Alhamdulilah!.a fili kuma sunkuyar da kansa yayi yace to Mum Allah yasa hakan shine mafi al’kairi!, Ta amsa da ameen. Tace”don haka kuje ku fara sh’iri wata sati ne d’aurin Aure da tarewa. Sannan bace sai kunyi kayan karya ba a’a mu al’kairin abu mukeso suka amsa da to sh’ikenan ku tash’i kuje Allah ya muku albarka ameen. Amm Ammar ina so ka zo min da Auta da kayanta zata dawo gdn nan harsai anyi biki sai ka d’auketa to ya amsa suka fita.
Ammar na isa gida wata zuciya tace karkayi sauri sanarda Auta kai zata Aura halama bata sonka kawai ka gwadata ka gani.
Da sallama ya sh’iga gidan amam ya d’aure fuska Auta da fara ta masa sannu da zuwa, ganin yanayin sa ya sa tace”Yaya na mai ya sameka? Kona maka laifi ne? Kai ya gir-giza mata alamar a’a to mai yasame ka? Dan Allah ka sanar min.
Cikin al’hini ya soma yimata bayani kam hahiya zata hadasu Aure kuma wata sati duk Auta ta k’agu taji da waye yace ni da Kausar da ke da Ahyan what?? Tace “ina sam bazaiyuba ni wlh bana sonsh’i. Ina da wanda nake so, cikin damuwa Ammar yace” wa kike so?.shiru tayi tana kallonsa don bata san lokacin da ta furta maganan ba, Ammar yayita bata kalamai akan ta d’au k’addara da abunda Allah ya zab’a mata, Auta kam kuka ta somayi mara sauti, daren ranan bata rintsa ba.
Da safe kuwa idonta duk ya kumbura Ammar na ganin ta sai duk ta bashi tausayi kamar zai fad’a mata ko zata samu sauki, don yana hango tsagw’aron Sinsa acikin kw’ayar idinta amma ya share.
Yace”Auta ki sh’irya zuwa dare ina dawo zan kaiki, cikin fush’i tace”ni ba inda zanje kai naga alamr ma baka damuba daman baka damu dani ba, kuka ta saki mai tsuma zuciya har k’asan zuciyansa yake jun kukanta, fita kawai yayi a d’akin don bazai iya saura-ronta ba. Yinin ranan bata ci abimci mai ky’au ba sai da azahar ta samu bacci ya d’auketa ko da ta tash’i bayan la’asar idonta ya washe wanka tayi takiyin kw’aliya tace”ni ba ida zani daman son da Ammar ke min bana gsky bane, hmm ko ajikinsa bai damuba mts ni haushin Kausar din ma na fara ji. Ni rash nace”kw’aji min Autan nan harta na da bakun iya fush’i Ammar kuma fa da ya ganta da saurayi yayi yaya?.
Da yamma da Ammar ya dawo sunsha rikici don FIR tace ita ba inda zata je, sai data ga ya bata rai kafin ta fito tana kuka ta dan debi kayanta kad’an suka tafi.
A gd basu same su ba don sun fita sayayya tana zuwa dakinta ta wuce, sai magriba suka dawo ganin karsu fahimci halin da take ciki yaa ta d’an biye damuwarta ta sake kad’an, sukayi hira har zuwa 8:40 Mum ta haura sama Munay ma haka Kausar da Auta kad’ai a falo.
Ammar ya sh’igo zai musu sallama ya wuce yatarab ba Mum ya musu sai da safe ya fita.
Biyo sa tayi da ta sha gabansa kasancewar ida suke ba haske kafin ka isa harabar gdn ne, kuma tasoma masa tace”ni wlh bana son auren inada wanda nake so kuma shiya yace yana sona ai, ganin Ammar yayi sh’iru baice mata komai ba tasa ta fada jikinsa ta sake kuka nan take Ammar taji lbr yasoma sauyawa, kara rungume Auta yayi yace”Zainab sai da taji sunan har cikin kw”anyanta, bata iya amsawa ba sai binsa da tayi da ido yace wa kike so?, jin tambayar tayi tazomata a BAZATA, shiru tayi ta kafe sa da ido ganin yanayin da take kuma ya fahimci sh’itake so, sai yamata dabara sunanta yasake kira akaro na biyu kasa amsawa tayi yace”Zainab kina Sona?.da sauri ta daga kai alamar eh! Lallausar murmushi ya saki ya kara rungumeta fuskansa ya duko zuwa dai-dai kunne ta yace Zainab nine mijin da zaki aura, nayi hakane don in ga kina qauna ko ba ky’a qauna ta. Dukan wasa ta kai masa a kirji yace”wash ashh kika dake sai na rama zata gudu ya cabkota ya kara mannata da jukinsa tana kiciniyar kw’acewa ta kasa sai da ya bata lafiyayan kiss tukun ya saketa don kar ya wuce gona da iri.
Da gudu tayi cikin gd tana yar dariya.

H Mamu ta sanar da kausar ita ma ba a samu matsala da ita ba. Don haka suka ci gaba da sh’iri.
Ammar akw’ati Uku da kit ya yi ma auta bai wani yi kayan karya ba turmi ish’irin ya mata sai English wears da ya samata. Ban garen Ahyan shima turmi talatin yayi da akw’ati hud’u da kit komai sai son barka a talakance ba karya aciki.
H Mamu ta had’a yan Amareta tana ta tsumasu su Munay sai shirin biki akeyi.
Ammar gida ya kama musu plat su kadai ba mai tsadan daga hankaliba 80k ya samu.
Ya sh’irya shida Auwal sukaje k’auyen su Malam ya sanar musu da Inna laure yace”Malam ina son kazama waliyin Auren mu, yaji dad’i sosai basu bar kauyen ba sai tare da su Malam gd da suke ya kaisu d’aki Auta.
Amare liyafa suka sh’irya sai angwaye da suka sh’irya Dinner.
Yau take laraba duk gidan acike yake da yan biki yan sokoto sun zo, Amare ko Mum ta hana su fita anata gyara su Ammar da Ahyan sun had’a kai tare suke komai da Auwal Munay ko da Auwal tunda aka fara hidimar biki naga abunsu sai a slow.
Yau Al’hamis takama yau za’ayi liyafa Mum ne ta kawo musu wani sari mai ky’au sosai, masu kw’aliya suka gyara Amare lokacin da suka fito gun liyafar dake acikin gd za’ayi hmmm masu karatu lokacin da suka fito karkuso ku gansu ohoho abun bacewa komai don sun sha ky’au kamar ba gibe, liyafa akayi na gani na fada malama Khadija da Malam Juwairiya suka gabatar da nasiha game da rayuwan aure.
Bayan an tash’i a gunne suka nufo gida suna d’aki munay ke zi-zita irin ky’an da sukayi tace”Allah yasa wankar Dinner tafi na yau murmushi sukayi dukansu gabaki d’aya.
Ran jumma’ah tun da safe suke aiki dafa abinci yan d’aurin Aure sai da suka kammala komai H Mamu tazo tasa Amare sukayi wanka cikin atafa sun sha turare had’in yar mai duguri, bayan Sallah Jumma’ah aka saida Aure Ahyan da Kausar, Ammar da Zainab daga guri yan d’aurin aure suka wuce zaranda holel don gudanar da walima.
Da dad’dare Amare sunsha ky’au cikin gown kowacce kala d’aya da angonta Ammar yasha shadda fari da ratsin marun yayinda Auta tasha gown fari da ratsin maroon colour aciki ta sha make-up sosai tayi ky’au.
Ahyan kuma daga nesa na hango shi da farin shadda yasha aiki da zare blue colour, Kausar ma gown ta sha fari da ratsin blue colour bakaramin ky’au tayi ba.
Mutar d’aukan ya biki ne ta tsaya duk suka debi wayanda suka dace, Munay da Auwal ya d’auketa a motarsa yayinda aka tafi da Kausar da Ahyan a motar abokinsa, sai da aka gama kw’ashe su kafi naga wata k’atuwar Jeep baka mai bak’ak’en glass perker ba a dad’e ba naga wata mata tafito da Auta tun daga nesa take zuba ky’ali. Ammar kam sake baki yakeyi yana kallonta baita ba d’aukar ky’an Auta ya kai haka ba, bud’e murfin motar aka sata aciki, sai da ta zauna tukum taji k’amshin da tasaba ji, da sauri ta kalli gefenta Ammar ta gani yana mata murmushi. Lokacin aka jasu a motar hannusa ya sanya cikin nata yafara murzawa dake cikin motar ba haske matsowa yayi kusa da ita ya janyo ta jikinsa ya sanya haske wayarsa yana haska fuskanta sai da yagama kalon fuskanta ya gan-garo zuwa bakinta da ya sha jan baki a gankali ya soma. Oh!! Na gaji masu karatu sai zuwa page d’in gaba zaku jini.
Taku a kulum mai k’aunar ku 
  
Rash Kardam

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts