YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-56~60.
Yau kwanan Dr Umar 8 da dawowa, har
ya koma bakin aikinsa, tun safe yake jin
son yawo zai zaga gari, kuma bai son
security ko d’aya yabisa, don shi daman
bai cika fita da security’s ba, don Dad ke
matsa masa baya son yana yawo haka,
ko driver yana bari yana jansa, yana
tashi a office karfe 3:30pm, gida ya nufa
yayi wanka, yau sai ya tsinci kansa da
son sanya jamfa, nan ya ciro wata
shadda dark blue amata aiki, da surkin
farin zare da blue, hularsa ma blue ce da
surkin fari, ya d’auko ta kalminsa ya
tare da agogo, tsayawa yayi a madubi,
yana kare ma kansa kalo, gaskiya ya
hadu ko ni Rash dana kalesa, sai da
kirjina ya bada dumm, Umar mutum ne
mai kyau ga kamala ga k’warjini, fari ne
tass, yana da dogon hacci tare da
karamin baki, kai in ka kallesa sai
karasa da wani yare zaka danganta shi,
India ne ko balarabe, ko Fulani. Tunda
ya sauk’o falo falo, umma ta ga d’anta,
sai murmushi take zubawa, tace”Baba
na sai ina haka?. “Wananan wankan fa?.
“Ko nayi surkace?. Don raboka da saka
manyan kaya ka dade. Cike da
murmushi ya kalli Umma, Yace”
Ummana duk wannan tambayar ni
kad’ai, bata surka Umma da saura tukun,
zan dai zaga cikin gari ne. Cike da
kulawa tace”Allah yasa futanka a
samomin surka mai hankali da tarbiya,
yar mutunci, cikin jin dad’i ya amsa da
Ameen. Tace”Son Allah tsare a dawo
lafiya, ka kuma tafi a hankali, to ya
amsa ya fita, tun a harabar gidan
ma’aikata ke masa sannu kud’i ya ciro a
aljuhunsa wanda bai san nawa bane ya
basu, ya shiga motarsa ya ja.
Khadi tafe take, tana tunani yau ta
kad’e, in cikin zuciyar ta tace” yau gashi
malam baya nan, nikam na banu,
bansan wani irin duka zata min ba. Hala
yau kamma, k’wananane ya kare, nan
tafara “Ya Allah ka yafe min, kasa na
cika da imani, wasu hawaye ke bin
fuskarta. Tafiya take sam bata san inda
take nufa ba. Tsaban zance zuci, har ta
hau kan titi, jama’ a dake hanyar sai
kalonta suke, wasu na tausaya mata,
gashi fuskanta da nikaf, jama’a na ta
mata magana sam bata sani ba, bata ma
san sunanyi ba,”wai kunu a wani gida”.
Dr Umar na tafe a cikin motarsa, ya
kuna qira’ar Ahmad Sulaiman, yana tafe
cikin nutsuwa, ya wuce ran about baban
gwari kenan ya d’auki hanya. Sam bai
hangi yarinya ba, sai da yazo kusa ya
ganta. Sai tafiya take a tsakiyar titi ga
mutane sai kalota suke horn yayeyi da
k’arfi, amma sam bata ji, gashi ya d’au
gudu sosai, wani wawan burki da yata
kane yasa dawo cikin hayyacinta, damar
motan, ta gabanta ya tazo, suman tsaye
tayi, dan tsaban razana ita bata fadi ba
ita bata motsaba.
Da sauri ya fito cikin motar, yana zuwa
kusa da ita, yaga bata motsa ba ga idonta
sun kafe, cikin dakiyar zuciya yave” ke
lafiyarki klau kuwa kika hau kan titi?.
Me kike tunani haka? Luuu yaga ta tafi
zata fad’i cikin zafin nama ya tareta, ta
sauka a jikinsa. Jijigata yayi yaga bata
motsi, cikin sauri ya fincike nikaf dinta,
sam bai ga fuskanta ba, juyaa yayi, ya
kali wanda suka taru a gun, wasu na
masa kalon mamaki, wani d’an tsoho
yagani yace”Baba pls kazo ka taimaka
min dan Allah. kamata sukayi, suka
dawo da ita gefen titi, da sauri Dr Umar
yaje da gudu ya bud’e motarsa, ya
d’auko goran ruwa, yazo ya yayya fa
mata, sai a lokacin ya kali fuskan, kasa
d’auke idonsa yayi, yana furta”Sarki ya
tabbbata ga ubangijin sammai da kassai,
lalle ubangiji yayi hallita a gurin. a
hankali tasoma bud’e idonta, tarass ta
sauke su akan, Dr Umar da ya zuba mata
na mujiya, ya kasa d’auke kansa ga
fiskanta.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» 'YA'YA DA DUKIYA..... 56-60
'YA'YA DA DUKIYA..... 56-60
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
0 comments:
Post a Comment