New Post

Tuesday, 18 April 2017

'YA'YA DA DUKIYA 136-140

’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-136~140.
Umar kuka yake ana haka har suka iso
New Delhi, motane tazo ta d’aukesu har
asibitin da za’a mata aiki, kasancewa a
sanar musu, sun sanda suwansu, ana
shiga da ita likitoci, suka hau bata
taimak’on gagawa. Sun d’au awani suna
mata surgery, Umar ya kasa zaune ya
kasa tsaye, duka sun dun kufa sai addu’a
sukeyi. cikin ikon Allah likitan ya fito
cike da fara’a, hannu ya mika ma
Gwamna, yace’ In Allah ya yarda musa
tsamani komai normal”
Hamdalah suka rayi, suna gun akazo aka
wuce da ita zuwa d’akin da zasu ajeyeta.
Khadi bata far-fad’o ba sai kusan
3:00am na dare, doctors aka kira duka
dubata, Umat ko sai addu’a ke mata.
Haka suka kasance cikin jinyan Khadi
yau kusan watandu d’aya kuma yau ne
za’a ware mata, bandage, doctor
yace”suyi fatan Allah yasa aikin yayi
nan aka shiga da ita, wani room don
since mata, su Umar sai addu’a yakeyi.
Awa d’aya ya d’aukesu, likita ya fito nan
ya saida musu komai normal, zasu iya
shiga su ganta, Umar da gudu yayi
d’akin yana zuwa ya ganta kwance, suna
had’a ido murmushi ya sakarmata, zuwa
yayi ya rungumeta, ana haka su Malam
suka shigo, sai da Dad yayi gyaran
murya, tukun ya san sun shigo, cikin jin
kunya ya koma gefe, sannu suka ringa
mata.
Tun daga wanna ranan Umar shike mata
dressing d’in ciwonta, ya bata abinci
abaki, ya mata alwala, da daddare kuwa
kafin ta kwanta zai d’auko story book
yana karanta mata, da joke masu dad’i
tana dariya, har tayi baci, inyaga tayi
nisa da bacci yazo ya ru gume matarsa
haka rayuwansu, ya kasance gwanin
dad’i. Ganin Khadi ta warke suka fara
ahirin dawo 9ja don ayi biki kowa ma
ya huta.
Gwaggo kam taci a zaba, in har kasanta
ada kaganta yanzu bazaka ganeta ba,
tayi baki sosai, gashi har hak’urinta sun
zube, tsaban duka da wahala, sai daga
baya ne, Beeba ta sanar ma Dr Abdul
gaskiya, shima ya fad’a ma Baban Umar,
sai da sukayi bincike suka tabbatar da
gaskiyan al’amarin kafin aka saketa,
randa tashiga unguwansu, matasa suka
tashi zasu mata duka da kyar aka
kwaceta, Gwaggo tayi nadama ba kad’an
ba. Kulum cikin saloli take, tana addu’an
Allah ya tashi kafad’un Khadi.
Yau jirgin su Khadi ya sauka 9ja, Umar
ko sai wani rawan kai yakeyi, ko
kunyasu Dad baiji, sai yawani rok’o
hannuta, sai da Mum ta zo ta rik’e
hannu yarta, Mum tace”Malam za’aban
aron yata, zan tafi da ita kafin biki.
Yace”bakomai ae Khadi takune.
Suna isa gida ta kira Hajiya Suwaiba da
Ameena tace”ga yata nan kuje a gyara
min ita, banson Umar ma ya ganta sai
biki.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts