YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-31~35.
Malam ya sayi maganin dubu buyu da
d’ari biyar ya nufo k’ofan Emergency ya
mika ma nurse “Malam ya tambayi
office d’in Dr Abdul nurse ce ta gwada
masa, godiya ya mata nufi office d’in, da
Sallaman sa ya tura k’ofar aka bashi
izinin shigowa, Dr ya nuna masa gun
zama Malam ya zauna. Sai da Dr ya
gama yan rubuce-rubucen sa tukun ya
d’ago da fuskansa tare da zare yar faran
glass d’in da ke manne a kyakyawan
fuskansa. Malam ya msa sannu da
aiki,Cikin girmamawa ya amsa, kali
Malam yace”Baba jikin Khadeeja yayi
tsanani sosai, mai yasa kuke barinta
tana aiki da ruwan sanyi?, kuma tana
zama a inda ke da sanyi, mai ya kawo
hakan bacin na sha fad’a muku illar
hakan amma kun kasa koyayewa. Malam
da jikinsa yayi sanyi yace”Dr in Allah ya
yarda wanan karon zamu kiyaye fatan
mu kawai yanzu ta samu lfy. Dr Abdul
ya kallesa sosai tabbas ya gano damuwa
a cikin idonsa ga alamar magana a
bakinsa, amma tunda bai fad’a ba “ni
dai zanyi iya kokarina ganin na taimaka
mata, ya Allah kabata lfy ameen. Ya kalli
Malam yace”shikenan zaka iya tafiya
amma akula mata da shan magani. Kai
Malam ya d’aga masa alamar eh!. ‘Dakin
da aka kwantar ta ya yashiga Beeba ya
gani a bakin gadon ta zuba mata ido ga
alamar tayi kuka sosai. Da Sallama ya
shigo Beeba ta masa sannu ya amsa tare
da zama a d’aya daga cikin plastic chairs
d’in dake d’akin. Yace”Beeba ya jikin
Addah ki?. tace” da sauki amma har
yanzu bata tashi ba, bacci take ya kalli
Khadi yace”Allah ya baki lfy, cikin
zuciyar shi kuwa cewa yake” ya zama
dole in d’auki mata ki akan Gwaggo
bazai yiwu Khadi taci gaba da wahala
haka ba. Ya mike ya nufi k’ofar Asibiti
ya sayo musu abinci ya dawo ya kawo
musu nan Beeba ta karya, shima sama-
sama yaci abincin.
Gwaggo ne tafito daga bayi ta na
zuwa d’aki taga ba Beeba ta duba d’akin
su Khadi taga bata nan d’akin Malam ma
baya nan, Rabi ta tambaya tace”kee ina
Beebalo?. Rabi ta kalli ina tace” ba sun
fita da Malam ba naga ya riko Adda
Khadi, tsaki tayi ta leko titi basa nan,
nan takama bala’i yau zaizo ya sameta
akan me zai fita mata da yarta don wata
marar galihu, ita yarta na galihu, cikin
gida ta koma sai surutu take ita d’aya.
WACECE KHADIJA?.
khadijatu~Kubrah shine asalin sunan
Khadi ya d’aya tilo ga Malam Adam.
Malam Adam haifafen garin kano cikin
unguwan Dakata gurin fire service.
Yayan Malam Ahmad ne Ubansu d’aya
ne. Tun Malam Ahmad na karami Allah
yayi rasuwa Mahaifiyar sa, ya koma
hannun Maman Adam wato Kakan Khadi
kenan, ta yi musu rikon tsakani da Allah
har suka girma. Adam shiya fara yin
Aure kasan cewan shine babba sun
shekara da yawa da matar sa Balkisu
Allah bai basu haihuwa ba, sai daga
baya ta samu ciki ya zo mata da laulayi
haka tayi ta fama har tazo haihuwa, ta
kwana biyi tana na kuda, kafin rannan
ukun har ana shirin shiga da ita
operation ta haihu ko juyawa batayi ba
Allah ya karbi abunsa. Malam Adam yayi
kukan rashin matarsa mai hankali da
kirki, watan ta shida da rasuwa Baba
Ahmad yayi Aure, ya auri matar sa
Hauwa amma auren dangi sukayi yar
kwan war Maman sa ne,(danganta karsu
ta gun uwa kenan da haiwa). Hauwa
macece mai masifa tun tana budurwa ta
ki jinin Balkisu Maman Khadi ganin
yanda Ahmad ke zama a d’akinta hakan
yana bata haushi sosai.
Cikin ikon Allah Khadi ta samu kulawa
in ka ganta bazaka ce bata sha nono ba
madara take sha bul-bul da ita ga ta da
gashi ga kyau sosai, gwanin burgewa.
Hauwa shekaranta 3 da Aure ta haifi
yarta Beeba kar kuso kuga murna gunta,
ta d’au son duniya ta d’aura ma Beeba,
ta taso cikin kulawa ga hankali, in ka
ganta sak Malam Ahmad kamar kakinta
yayi, yarinya mai hankali da nutsuwa,
jinin su ya had’u da Khadi tun Beeba na
karama Khadi ke mata wasa komai ta
samu zata kawo mata, amma in Gwaggo
ta gani ta kwace ta yar ta daki Khadi,
ana cikin haka wata ranan talata Malam
Adam ya tashi da ciwon Ajali kwanasa
biyar Allah ya karbi abunsa tun daga
wannan rana Khadi ta dawo hannun
Malam Ahmad da zama, nan Gwaggo ta
samu daman galla za mata, sam bata
kaunar ganin Khadi da Beeba sun zauna
gu d’aya.
ﺭﺍﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
[
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» 'YA'YA DA DUKIYA..... 31-35
'YA'YA DA DUKIYA..... 31-35
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment