: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
47
Alhaji Ammar Sa’ad Saraki ya dawo hamshakin d’an kasuwa mai cike da naira ya sanu ciki da wajen kasannan, yana da company a yawancin State d’in dake 9ja.
Jerin gwanon motoci na hango sunyi com boys abun gwanin burgewa number motar kuwa duk iri d’aya ne ansa A S Saraki1 har zuwa 10 ya nufi gdn sa, ko da ya shiga matarsa ceta taso cikin shiga ta alfarma ta yi welcoming d’insa, sai da ya huta yaci abinci ya kaleta yace Madam kinyi ky’au kuma kulum kara ky’au kikeyi, cikin salon da ta saba rikita sh’i ta juya ido tace”kaima haka sh’iyasa kulum nake k’ara sonka. A natse ya kalleta yace”Zainab ku shirya ke da yara tunda suna hutu nagama yi mana booking din jirgi ran friday zamu kaduna. Da sauri tazo ta run gumesa ko mai ta tuna sai tafara zubar da hawaye janyota yayi jikinsa yasoma lalash’inta yace”nasan me kike ma kuka ki share hawayenki yanzu ne lokacin da zamu dau fansa.
A yanzu dum wani moving din Baba Sani ina da lbr akansa kuma Baba Isya ya rasu a razane ta d’ago amma tuna abunda sukayi ma iyayenta cikim kasa-kasa da murya tace”to yau ina Baba Isiya yake gash’i ya tara da su Dad, rayuwa ke nan duniya ba gurin matabbata ba ne.
Tun ran Alhamis suka je gidan H Mamu suka mata sallama tare da musu fatan nasara daga gidan kuma suka nufi gidansu Malam suma Addu’a suka musu.
Ran friday tun karfe 1:00pm aka kaisu Airport basu dad’e ba jirginsu ya d’aga sai KD, 1hrs ya kaisu cikin garin KD, wani katafaren gd da Ammar ya gina acikin garin kaduna suka sauk’a, garin duk ya fawo ma Auta wani iri basu fita ko ina ba sai washe gari suka sh’irya cikin sh’iga ta alfarma da yan yarasu uku Zarah ce baba sai mai bi mata Kairat sai Al-hasan mai sunan Dad suna kiransa da junior, yaran ky’awawa da su gwanin burgewa. Motocin Ammar ne suka jero zuwa k’ofar gdn. Ammar rik’e da hannu junior sai Auta rik’e da hannu Kairat suka sh’iga mota suka nufi Hayin Rigasa.
Taku a kulum mai k’aunar ku
Rash Kardam
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
48
Motoci ne a jere suka sh’iga layin duk jama’ar dake unguwan sai lek’e sukeyi don basu taba ganin motoci sun jero irin haka ba, wasu kamma cewa suke yau gwamna ya zo umguwansu, dai-dai k’ofar gidan su Auta motar ta perker body gurad d’insa ne suka fito sai da suka rarrabu a gun kafin aka bude ma Ammar k’ofar motan ya fito, zagawa yayi ya bud’e ma Zee sai yara suka fito daga motarsu, duk yan gurin ba wanda ya shaidasu sai dai sunga ansa AS Saraki a jikin motar kuma suna jin lbrsa. Baba sani dake sh’irin fitowa yaga mota a k’ofar gd sa tabbas yana jin lbr AS Saraki k’odai mafarki yakeyi ne kam ya san ba abunda zai kawosa gidan.
Ammar ya mika masa hannu suka gaisa yace ka sai dani kuwa Baba Sani da yayi mutuwar tsaye yace”Eh! A S Saraki da nake jin lbrsa ne ko? Ammar yayi murmushin kasaita yace”kw’arai kuwa nine, mush’iga daga ciki falo su Auta aka sh’iga da su sai da aka kawo musu kayan shaye-shaye sam Baba Sani bai ganesu ba, sabida shekaru sun tafi da yawa ga naira ya zauna musu, Ammar ganin bai ganesa ba yace wata kasuwanci ne nake so muyi da kai, na samu lbrka gurin wani yaron ka mai suna Gumus, ya yaba da kai sh’iyasa naji ka kwantamin a rai da mu had’a business, sun d’anyi hira kafin yamasa sallama ya rako su har bakin mota saida suka sh’iga ya kima gd cike da murna tabbas tsun-tsu daga sama gashashe, nikam Rash nace”wato mai hali baya fasa halinsa a ko ina yake”. Sun d’ansoma tafiya kenan sai ga motar Futha ya danno kai dake glass gin ta fari ne Ammar yasa aka dakatar da ita sam Auta bata lura da itaba sai da yace mata”Sweet kali can aiko ta kalo futa zata fita da gudu ya riketa yace zaki wargaza mana plan d’in mu Short note yayi ya bama body gurad d’inda ya bata, ko da ta karanta ta bud’e murfin mota da sauri ta fito Ammar ya rage glass d’in motar sa tabbas sune ba gizo suke mata ba. Ammar yace kin gane a kw’ai Adress din mu so kizo ki same mu anan plan d’in mu zai iya wargajewa ok! Motar ta takoma cike da murna tana gode ma Allah da ya bayya na mata su Zee dinta
Da yamma Barrister Futha ta nufi gd su Ammar ko da taje sunyi murna ita da Zee sannan suka bama juna lbr bayan rabo Futha cikin mamaki tace”no wonder biri yayi kama da mutum dom na dad’e ina zarginsa kam nan ta ce bari na sanar da Sadiya don baza a rasa wani evidence a gunta ba, ringing biyi yayi ta d’auka sun gaisa futha ta bata lbr komai cikin murna tace”Futha suna ina nan ta bata Address d’in gidan bata dad’e bakuwa ta iso sun gaisa itama aka bata lbr taci kuka jin Babanta ke da hannu kuma ta d’au alwansh’i basu goyon baya don a kamash’i, Futha tace”yau weekend ne bazaiyu ayi karansa ba amma zuwa Monday sai ayi yanzu dai Ammar duk abun zai zama a hannuka ne duk yanda za’ayi kar kabari ya bar gari ko ya ganeka ok! Haka suka watse.
Yau monday duk wani ma’aikaci ya fita aiki, yau ne su Ammar suka kai karan Baba Sani, police har gd sa suka je aka kamasa C.I.D aka kaisa, ba irin wahalar da ba’a masa ba ama fir yak’i fad’ar gsky harranan sh’iga kotu, kowa ya hallara a koto, mai gabatar da kara ya tashi ya koro bayani ba alkali, barrister Futha ta fito ta gaida alkali kafin ta soma yan tambayoyi ma Baba Sani amma fir yak’i yarda da sh’i yayi, rashin wata kw’akw’aran shaida aka d’aga karan har sai 5/3/2016 haka aka watse amma kotu ta hana belin Baba Sani har sai ansamu gsky.
Taku a kullum mai k’aunar ku
Rash Kardam
0 comments:
Post a Comment