New Post

Tuesday, 18 April 2017

'YA'YA DA DUKIYA..... 106-110

:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-106~110.
Gwaggo ta sha kwalan malam sai ihu
takeyi, ya sa hannu ya ban-bare rigansa,
yazo zai wuce ta sake shan gabansa,
“yaufa bazaka fita agidan nan ba, yau
saika kawo ma Beeba miji. Ya matsa
tabisa yazo zai shiga d’aki ta tare qofar,
sai ya tureta yazo fita ya iso zaure, tazo
da gudu ta kama rigansa saida ta yaga.
Ran Malam in yayi dubu ya b’aci bai san
lokacin da ya kikifa mata mari ba, ya
hankad’ata ta fad’i akasa. Yace”Hauwa
hassadakin bazaikai ki ko ina ba,
wannan aure matsawan in ima raye ba
fashi, sai dai ki mutu da bakin ciki. Ya
juya ya nufi d’aki ya canza kaya, yazo
ya wuceta, har ya fita ya dawo
yace”kuma wallahi in kika kuskura kika
tab’a Khadija, a bakin aurenki saki zan
miki ba dawowa, kina dukanta kin san
sauran, Yasa kai ya fita. Gwaggo abun
duniya ya isheta, tabbas Malam tun da
ya rantse sai ya aikata, jiki ba kwari ta
koma d’aki tafara kuka, cikin zuciyarta
ko cewa take”wanna mari ba zai sha
banza ba tunda yace karna daketa, to ae
dole tayi aikin gida, dan haka ba duka
akwai zagi da wahala yankuma.
Khadi tana d’aki kwace, tana group chatt
da kwayenta, wanda suka had’u a
WhatsApp ta lura suna da hankali,
shiyasa nasu yazi d’aya. A group d’in
Khaleesat Haiydar suka had’u na
Facebook dake Khadi mayar karatun
novel ne. Hiran Novel d’in KAINE SIRRI
NA littafin Aisha Muh’od, Queen Neenah
tace” Khadeejat kin karanta KAINE SIRRI
NA? khadi tace”eh ina karantawa kai,
gaskiya novel d’in ya had’u. Farhat B
Haske tace” Queen Neenah n Khadeejat
kun karanta MARTABA TA da MATAR
MUTUM na Mrs Umar Soja kuwa?.
Sukace “a’a bamu karanta ba.
“Lalle an barku a baya ni harna gama
karantawa, yanzu ina karanta YAR
WAYE NE?.na Khairat S Panisau, da
KUDAN ZUMA na Zee Hrt.
Suka had’a baki tare da cewa”Farhat
littafin ya had’u ne?.
“Eh kai ana rikici kam, ku tamabi.
Hajiya Jamila Aliyu Haiydar tana dashi
sai ta tura muku.
Queen tace”Khady bari na nemomana
zan tura miki ina samu.
Khady tace”ok amma fa nagode. Farhat
B Haske tace”gaskiya ya kamata yanda
muka saba musan juna, gashi mun shaku
sosai, ae zumuncin bai kamata ya tsaya
a chatt ba.
Queen Neena tace” ae fa gaskiya kam,
yanzu musa rana sai mu fara zuwa
gidansu Khady.
“Ko ya kuka gani yan’uwa?.
Duka suka turo da haka za’ayi. Khadi taji
dad’i amma tana tunanin yanda zasu zo
Gwaggo zata iya cin musu mutunci.
Salama sukayi akan ran Friday za’a
had’u, a gidan Hajiya Jamila Aliyu
Haiydar sai su taho.
Gwaggo tana gama sake-sakenata tafito
ta kwala ma Khady kira, “fito dan
ubanki, mai fiska kaman na biri, kin
lashe wa mijina zuciya kin rabani da
yata, gashi kin samu d’an mutane, kinsa
yayi sata sun kawo kud’in aure ko?.
“To ni kam dai ahir d’inki.
“Kurwata kur bazaki iya ci ba.
“Ko uwarki ma haka tagaji ta barni don
nafi k’arfinku.
Nan take idon Khadi yaciko da kwalla.
Gwaggo ta tattaro wanke-wanke ta tara
mata, tashiga d’aki ta d’ebo kaya harda
wankaku, duk ta had’a mata.
“Maza-maza kiyi ki gama su yanzu, ki
kuma tabbatar an girkan abicin kar yayi
dare.
“Kin san halina basai an fad’a maki ba
aha.
“Ni ce Gwaggo Munguwa No1, in kika
kuskure min a aiki sai na miki ba dad’i,
tsohuwar mayya kawai.
“Mai son raba aure, amma kuma bazaki
iya ba sai dai a fasa naki.
“Kuma ina kan bincike duk randa na
gano gidan saurayinki, sai naje na had’a
duk wata manakisa ta, an fasa auren.
Niko Rash”nace Gwaggo rashin sani yafi
dare duhu, da kimsan Umar d’an waye
da baki fara masa rashin mutunci ba,
don yafi k’arfin raini.
Khadi ta dunkufa aiki baji ba gani, duk
da ta gaji amma bata son ta nuna bare
Gwaggo ta zagi iyayenta, don yafi komai
cin mata rai.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
[9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts