’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-116~120.
A gidan su Dr Umar kuwa, sun gama
had’a lefe nagani na fad’a, lefen nun ma
sa’a. Cikin kayan harda key d’in mota,
k’irar Honda CRV, Mum d’insa ta saka
masa, Dr Umar shima ya karo wasu kaya
aka saka, masu karatu kar kuso kuga
kayan akwatina ma Set hud’u akasa,
zannuwa kuwa ba kananu. Hmmm
kayan d’an Gwamna d’aya tilo aidole ya
zama abun kalo, Mum tace”Umar ka
sanar da Khadijat jibi za’a kai kaya.
Cikin murna ya shirya sai da ya je Store
ya mata sayya, ya nufi gidan, bai wani
b’ata likaciba ta fito. Sai da sukayi
hiransu yace mata”My Khady!”. Cikin
sanyin murya ta amsa da “na’am”.
“Khadijat! Duk wani farin ciki na kene,
ina matuk’ar qaunanki.
“Alhamdulilah! Allah ya amsa min
addu’a ta, na bani ke amatsayin mata.
“Ki sanar da mutanen gida, In Allah ya
kaimu jibi za’a kawo kayan lefe.
Cikin jin kunya ta saki murmushi, tare
da rufe fuskanta da tafin hannun ta.
Hira sukayi mai cike da so da qauna, sai
dab magriba, ya mata sallama ya tafi.
Khady na shiga gida ko da Malam ya
dawo, bayan ta masa sannu da dawowa,
ta sanar masa da sak’on Dr Umar. Cikin
farinciki ya yi musu addu’a.
Washegari Malam ya aika ma dangin
Mahaifiyar Khady, dangin Uba ya sanar
ma wayanda yakama ta su zo karban
kaya.
Malam ya sayo kayan karban bak’i,
harda yan kajin sa, guda biyar ya tura
kasuwan kauye, aka sayo masa. Ya sayo
multina da lakacera, kaya iya na talaka,
Baba Yalwa k’anwan Maman Khadi su
suka soya kaji, pepper meet sukayi, yayi
kyau ko ina sai kamshi yakeyi. Gwaggo
in banda harare-harare ba abinda
takeyi, ko hannu bata samusu a aiki ba,
karfe uku sun gama komai sun gyara ko
ina sai kamshi yakeyi. Malam yaje ya
d’an had’a kud’in da zai had’a na kasan
akwati, ganin karamci irin na Umar ya
samo dubu goma yaba ma Inna Yalwa
yace a basu. Khady ko tayi wanka cikin
kayan ta masu kyau, suka zauna a d’aki
ita da Beebah don basa son yawo.
Rabee’atu kuwa tana kusa da Gwaggo,
sai lashe baki takeyi, don tunda taga ana
soya kaji, yawunta ya kai.
Su Inna Yalwa wanka sukayi, suka saka
kayan su, mai kyau, suna zaman jiran
baki.
A gidan su Dr Umar kuwa, Mum kwanta
ta kira da matan Baba Liman, sai
Kwanwar Baban su Umar, bata tara
mutane ba, sabida tasan yanayin gidan
su Khady, kar suje su musu ba dai-dai ba.
Milasalin karfe hud’u da rabi, suka d’au
hanyan.
Misalin karge biyar, cikin unguwansu
Khady, ya d’au jiniya, motoci ne sukayi
jerin Gwano ga securitys a motoci sun
sanya sauran motan a tsakiya, suna
shigowa take suka fir-fito dan gani mai
zai faru. Motocin qofar gidan su Khady
suka tsaya.
Gwaggo dake d’aki taji jiniya mota,
tace”ko lafiya naji karan motar yan
sanda?.
Rabee tace”ai inaga wanda suka daki
Adda Khady ne suka dawo dukanta hala.
“Don ranan da irin wannan suka zo.
Gwaggi tace”Allah yasa sune, su dakata
inga ta inda za’ayi auren.
“Zo mu fita muga ya zasu kare. Suna
fitowa dai-dai lokacin yan sanda suka
shigo gidan da bindigansu, Gwaggo sai
zare ido take. ana haka suka ga wasu
Mata cikin shiga ta alfarma sun shigo.
Gwaggo tace”lafiya dai naga kuna shigo
mana gida?.
Wata mata mai yar kiba tace”nan ne
gidansu Khadijat?.
Gwaggo tace”eh! Nan ne.
“Lafiya dai?.
“Lafiya klau, kafin tayi wani magana
ansoma shigo da akwatuna.
Gwaggi tace”wanna fa?.
Matar tace”kayan Khadijat muka kawi”.
Gwaggo ta buga k’irji tare da zaro ido.
Nima Rash sai da wayata ta subuce don
na tsirata da ganin yanayin Gwaggo.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
[9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» 'YA'YA DA DUKIYA..... 116-120
'YA'YA DA DUKIYA..... 116-120
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment