’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-101~105.
Cikin takaici ya fincike rigansa, kalon
tsana yake mata, da sauri Gwaggo ta sha
gabansa, yau fa sai na tona muku asiri.
Wani mugun kalon da ya aika mata,
yasa Gwaggo bashi hanya, Khadi da gudu
tabar gun. Gwaggo ta ga kayan da Dr
Umar ya kawo da rawar jiki ta d’iba tayi
cikin gida.
Beeba na ganin haka tace”Gwaggo mai
yasa keke ma Addah Khadi haka?.
Gwaggo cikin zumud’i tace”kee bari
kawai ae ido da ido na kamasu suna
iskanci, cil da cil ganin annabin
tsohuwa. Beeba tace”kai Gwaggo gaskiya
Adda Khadi bazatayi haka ba, zata taba
zubar da mutuncinta ba, kuma na yarda
da tarbiyan da Malam ya bamu. Cikin
b’acin rai Gwaggo tace”oh to! to! Wato
Malam shi ya kula da tarbiyan ku bani
ba?. Beeba shiru tayi ganin Gwaggo ta
d’au da zafi.
Malam na dawowa Gwaggo da
munafurci tazo ta fara labartawa
Malam, Malam ya kaleta sama da kasa
yace”tashi ki ban guri bana son gulma, a
yanzu a kwai wani abunda zaki fad’an
na yarda, bacin nasan irin tsanar da
kikayi ma Khadija, yarinyan mai
hankali, bataji ba bata gani ba, kna
gallaza mata, jiki ba kwari Gwaggo ta
bar d’akin.
Dr Umar ko hankalisa kwance ke
gudanar da aiki, yanzu Dad d’insa kad’ai
ake jira a kawo sadaki, sai asaka ranar
biki.
Sakeenat kuwa sam Mum d’inta, taki
goya mata baya. Hankalinta duk ya
tashi, can ta tuno wata shawara, Zuly ta
k’ira a waya. Tace” kqwara kina ina ne
yanzu?. Zuly tace”gani a hanyan zuwa
gidan ku. “Ok sai kin iso. Ta ajiye wayar
tana zaman jiran zuwan Zuly.
Ko da Zuly tazo bayan ta gaisa da
Hajiyar Sakeenat, tashiga gun Sakeenat,
bayan sun zauna Sakeena tace”kawa
nifa bazan share mari da Umar ya
minba gaskiya. Zuly tace”wani mataki
zaki d’auka?. Sakeenat tace”na bayar a
sayo min dorina hud’u masu kyau,
zamuje unguwansu ba tare da securitys
ba, in munga yarinyan ko mu aika tazo
sai mu cazata.Zuly tace”good idea, haka
zamuyi.
Key motarta ta d’auka suka fita,nan idi
security ya kawo mata sak’onta, ta karba
suka ja mota sai Dakata.
Sun dad’e a unguwan Khadi bata fito ba,
can da suka gaji yaro suka tura yaro ya
kirata, Khadi ko kamar bazata fito ba,
amma can da yaron yasake dawowa, ta
d’au hijab d’inta tace”Beeba ana kira na
a waje barin duba ga wayata nan. Khadi
na fitowa yaron yace”gasu can a wancan
motar. Khadi tana ta raba ido, don Umar
bai tab’a zuwa mata da irin motar ba.
Sakeenat ko suka rike bulala kowa ne
bibiyi a hannusu, sai da Khadi tazo kusa
suka bud’e motar atare, suka nufota da
gudu dukanta suke tak’o’ina. Khadi ihu
take amma basu kyaleta ba, Beeba taji
kamar muryan Khadi da gudu ta lek’o
ganin ana dukanta, koma gida “Gwaggo
dan Allah kizo, yaran ranan suna dukan
Adda Khadi, Gwaggo tace”ha da gaske
Beeba tace”eh!.
Duka suka fito da gudu. Dukanta ko suke
Gwaggo ta fara kukara mata, kunyi min
dai-dai. Rab Beeba ya b’aci sosai, ganin
ba mai ceton Khadi, gashi ba maza a
gun, yasa ta tuna da Dr Umar. Da sauri
ta duba call history, ta kira number,
bugu biyi yad’aga, “hello hello Ya Umar
kazo ga wasu na ta dukan Adda Khadi,
wanda suka zo ranana. Cikin figici
yace”what suwaye?. Kashe yawar yayi
ya shiga mota gudu yake kamar zai tashi
sama.
Sakeenat ko ganin sun mata lilis, ga
mutane sun soma taruwa da gudu suka
shiga mota, suka bar unguwan.
Dai-dai zasufita a layi motar Dr Umar
yadanno kai ganin motar Sakeenat yasa
yasha gabanta, ganin zai tsaresu yasa
taja motar da k’arfi sai da ta buge masa
glass d’in mota ta gudu. Da har zai bita
sai ya tuna kowani hali Khadi take
kuma?. Sai ya fasa ya kara gudu.
Beeba ko ganin sun tafi dakyar wata
makwabciyar su, ta taimaka mata suka
shiga da Khadi gida. Karkuga fiskan
Gwaggo fal farin ciki.
Dr Umar na zuwa yaga mutane, da gudu
yayi salama ya shiga gidan, Beeba ya
fara karo da ita cikin damuwa ke
tambayrta ina Khadija?. Hawaye ya
k’ara zubowa “tana d’aki a kwance.
Yana shiga yaga halin da take ransa ya
b’aci sosai. Ya kira beeba yace” ki had’a
ruwan zafi don tayi wanka, waya ya
kira ba afi minti goma ba sai ga wasu
ma’aikatan asibiti da kaya, da kanta
yamata treatment, ya mata allura nan
take bacci ya d’auketa. Yana fitowa
yace”sistet Beebah barinje gida na dawo.
Na mata allura ta samu bacci, in ta tashi
ki kaimata ruwa ta watsa zataji dadi.
Yana zuwa gida yasanar da Mum d’insa
komai, cikin bacin rai takira His
Excellency yana d’auka, tace” ranka
shidad’e! Ya aiki?. Cikin jin dad’i His
Excellency ya amsa. Nan ta sanar masa
da komai, sai da ya jin-jina al’amarin
yace”tun da Baba liman nanan zan sa a
tura 1million sai akai sadaki, 2millions
kuma a had’a kaya akai. Ina dawowa sai
aure kawai. Mumcikin farin ciki
tace”Allah ya ja kwanan mai girma
governor, godiya muke Allah ya tsare
mana kai, Ya amsa da ameen.
Malam ko da ya dawo ransa ya baci,
amma yace”duk hakan baza’a fasa
auren nan ba sai anyi, duk mai hassada
sai dai yayi ya gama. Dr Umar ko kulum
sai yayi sawu 3 a gidan kula ta
musamman ke ba Khadi.
Yau da yazo bayan sun gaisa da malam
ya saida masa “iyayensa zasu zo, za’a
kawo sadaki. Malam yace”Alhamdulilah!
Allah ya kawosu lafiya mungode.
Washe gari Baba liman yazo ya kawo
sadaki, Malam sai da ya razana, kin
karban kud’in yayi yace”gaskiya Malam
sunyi yawa a rage. Baba liman yace”sam
bazan koma da ko si-si ba, mudai fatan
mu Allah ya sanya alkairi. Baban Khadi
ganin Malam ya girmesa, kuma bazai
iya masa musu ba ya sa hannu ya
karb’a.
Yana shiga gida don ya ba ma Gwaggo
haushi yace”Hauwa kawo min taburma
nan kizo kiga ikon Allah. Da sauri
Gwaggo ta fito har tana tun-tub’e, ta
shin fid’a masa tabarma bayan ya zauna
sai taga ya zaro da min kud’i har bunch
biyar, ido Gwaggo ta zaro, “Malam ina
kasamu wanna kud’i?. Murmushi yayi
yace”Hauwa wato zakaran da Allah
yanufa da cara ko ana muzuru ana
shaho sai yayi. “Kuma d’an hakin da
karaina wataran sai ya baka mamaki.
Gwaggo tace”ni dik ban gane hausanka
ba Malam?.
Malam yace”hmm Sadakin Khadi aka
kawo har naira na gugan naira million
d’aya. Wayyo nashiga uku sadaki ina
Malam d’an yankan kai ne ba fa
zaiyuba. Nima sai ka samo ma Bedba
miji, Gwaggo ta sha kwalan Malam, ihu
take tana kuka, tana fad’in ya cuceta.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
[9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» YAYA DA DUKIYA..... 101-105
YAYA DA DUKIYA..... 101-105
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment