YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-36~40.
Sam Gwaggo bata ‘kaunar ganin Khadik,
da Beeba sun zauna gu d’aya. A kwai
wani rana, da Khadi na wasa ma Beeba,
Gwaggo na zuwa ta saka k’afarta ta
shure Khadi, ta fad’i akan hannu ta, sai
da ta gurd’e. Ranan ran Malam ba
‘karamin b’aci yayi ba, har sai da ya
mari Gwaggo. Tun daga lokacin ta ‘kara
tsanar Khadi, har zuwa girmanta, sam
bata tausaya mata, duk aikin gidan
Khadi keyi, Beeba kuwa bata son ganin
Khadi cikin damuwa, in Gwaggo ta bata
ma Khadi aiki, sai ta faki idon Gwaggo
ta zo ta tayata su gama. Haka rayuwansu
ya kasance dad’i da ba dad’i, Malam ya
sanya su a Makaranta Khadi da Beeba
suna ‘ko’kari, amma Rabee kam in ban
da niman tsokana ba abunda take. A
hakan har Khadi ta kammala Secondary
school d’inta, ta barsu Beeba yanzu ke
karatu har islamiya an yaye ta. Matsalar
ta d’aya ne sam bata kula saurayi, ko
sunzo Gwaggo koran kare take musu, wai
baa su nimi mayya ba. Tana lashe
zuciyar mutane, har ta lashe na Malam
da yarta Beeba. Hakan sam bai damun
Khadi,ita kulum da Malam addu’a su,
Allah ya shiryi Gwaggo yasa ta gane.
Wankin Gwaggo dana Ya’yanta Khadi ke
yi, in tafara sai ta gama, bata isa tace”ta
gaji ba Gwaggo zata fara mata bala’i,
wani lokacin, abimci ma hana ta take.
Back to lbr.
Khadi bata farka ba, sai kusan k’arfe sha
biyu, sai da Malam ya ga tasamu ta ci
abinci, kafin ya musu sallama, akan
zaije shi gd ya dawo, Beeba ta mishi
adawo lfy, ya fita.
Yana isa gd, Gwaggo ta taso cikin
masifa, tana tambayar sa ina ya kai
mata yarta?. Ko dun bai damu da ita ba
ne, yana son wannan mayyar ta lashe
mata kurwa, kamar yarda uwarta ta
lashe zuciyan mutane. Sai da ta gama
sababinta Malam bai bi ta kanta ba,
abincin sa ya d’auka, ya fita tare da
tabarma da pillow. Gwaggo na ganin ya
fita, gyale ta d’auko ta fara binsa a baya,
har taga ya nufi Asibitin Murtala, itama
tace”ma me Napep su bi Malam, haka ko
akayi, har ya shiga cikin asibitin, ta bisa
a baya, har ‘kofan Ward d’in da aka
kwantar da Khadi. Ta na labe taga ya
shiga d’akin bai dad’e ba ya fito, ya nufi
wani guri a cikin asibitin. ta na shiga,
gadajen ta rink’a bi, har ta iso na su
Khadi, wani mugun kalo ta sakar ma
Khadi,da ke jin gine da pillow,
tace”mayya kin lashe zuciyar mijina da
yata, to bakiyi sa’a ba, tana zuwa kusa
da ita, ta wanke ta da kyakyawan mari,
nan take yan d’akin suka yi mata caaa.
Kafin ka ce me, guri ya d’auka da
hayaniya. Dr Abdul ne ya fito daga Ward
d’in dake, kusa da na su Khadi,
hannunsa rike da waya, da alamar waya
yakeyi. A hankali ya ke tafiya, tun daga
nesa ya ke jin hayaniya, yace”Dr Umar
ina zuwa, naga kamar female ward na
lfy, bai karasa ba ya iso gun hayaniya,
yayi yawa, da kyar ya kutsa zuwa cikin
gun, sam ya manta bai kashe wayar ba.
Dr Umar shima bai kashe ba, dai-dai
lokacin Malam ya iso gurin, ganin
abunda ke faruwa ya soma jan Gwaggo
da ta rufe Khadi da duka, sai zuba
bala’in take. Dr Abdul ya iso yana “tan
bayan lfy?. Gwaggo sai wani fin cikewa
take, Malam ya d’auke ta da mari. Ta
d’ago tana kalon Malam tace”ka mare ni
a kan wannan banzan, mayyan mai
kod’ade’en fuska. Ba zan yarda ba, sai
na rama ta sake yin kan Khadi, itakam
in banda kuka ita da Beeba sun rike
juna. Dr Umar da ke jin duk abunda ya
faro, duk da baya gurin amma ransa ya
baci sosai, cikin zuciyarsa yace”duk da
bansan maike faruwa ba amma wata
irin macece haka?. Malam ya ransa ya
baci mari ya sake wanke Gwaggo da shi,
zafin yasa ta nutsu sosai, sai ta dawo ta
fara jan Beeba, ita ko gadon ta rike,
security aka kira suka fita da ita. Sai da
guri ya lafa, Dr Abdul yace”Baba ka
sameni a office d’ina ya fita, Malam ya
nufi office d’in sa.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» 'YA'YA DA DUKIYA.... 36-40
'YA'YA DA DUKIYA.... 36-40
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment