New Post

Tuesday, 18 April 2017

'YA'YA DA DUKIYA.....66-70

YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-66~70.
Gwaggo cikin hayaniya da masifa,
Tace”mai yasa baka tura, Beebah ko
Rabee’atu, sai Khadi, to sai dai na k’ona
kayan. Malam kasa magana yayi, tsaban
takaicin dake damunsa, wannan wace
irin fitinaniyar macece?. Gwaggo ta d’ibi
kayan, tayi hanyan kitchen dasu, Malam
na ganin haka ya bita, kafin ya isa, har
ta fara sawa a wuta, kwacewa yayi tare
da zaro na wutan, wani gyalens mai
kyau, da sauri ya taka, da takalmin sa,
wutar ta mutu. Wani gumun kalo ya
mata, duk iskancinta sai da ta shiga
taitayinta, ta fito a kitchen, koda tazo
dai-dai gun Khadi shureta tayi da kafa,
sai da Khadi ta fad’i, ta Beeba ne ta
d’aga ta, rana mata sannu, Malam
yace”Hauwa mai yasa baki da tausayi
ne?. Kina tuna kema zaki mutu kuwa?.
Ki sani fa duk inda, iyayen Khadeeja
sukaje, kema zakije, kuma Allah baya
kyaleki bane, kuma nima ba wai fa
tsoronki nake ji ba, ina d’aga miki k’afa
ne. Hauwa kisani ‘YA’YA DA DABBA, DA
DUKIYA, BA’A K’ETAR SU, bakisan wacce
irin baiwa Allah yayi ma Khadija ba,
bakisana wani irin taimako, zata miki a
rayuwan ki nan gaba. Gwaggo ta kali
Malam cikin kalon da ban d’au maganar
ka da muhimmanci ba, tace” ehehehe
Khadi ne zata taimaken, ahir ahir, Allah
ya tsare gatari da saran k’ota, ni da
Khadi badai muzauna inwa d’aya ba.
Malam ya kaleta yace”Hauwa da badun
Allah bayason saki ba, to da yau tabbas
sai kin bar gidana, kuma kinci
albarkacin Khadi da ‘YA’AYAN da kika
haifa. Koda Malam ya ambaci saki, sai
da k’irjin Gwaggo bada sautin damm!
damm!.. Amma cikin k’arfin hali, dake
shaid’an ya mata kururuwa, tace”sai me
in ka sakeni?.daman wani abu nake
samu a gidanka, in banda gayyan tsiya.
Malam ya d’aga hannu yace”Ya Allah
kana jina, kana ganin abunda ke faruwa,
Ya Allah ka azurta Khadi da abunda zata
taimaki Hauwa’u. Yana dasa aya,
Gwaggo tace” ba amin ba har abada, sai
dai ku da wannan mayyan, talashe
zuciyarku.
Fuuuu Gwaggo takama hannu Rabee,
tajuya ta kali Beebah, kee da ta lashe
maki zuciya, saikiyi ta makale mata,
suka shiga d’aki.
Malam ya kama hannu Khadi, da Beeba
ya kaisu d’akunsa, albarka ya samusu,
ya musu nasiha, tare da k’ara bama
Khadi hak’uri. Tace” Baba ba komai, ae
Gwaggo uwatace, ita na bud’i ido na
gani, ita na santa, kuma ina mata fatan
Allah yasa ta gane Ameen ya amsa.
Dr Umar kuwa, yana komawa gida, ya
tarar da Mum d’insa, suna hira da Ilham,
shima zama yayi, tare dacewa washh,
Mum tace” daga ina haka Son?. Gyara
zama yayi, ya kali Mum yace”daga
gidansu Khadeejat nake. Kafin Mum tayi
magana Ilham tace”bros nikam ina son
gani Aunty Khadejat d’inana. Kulum sai
labarinta mukeji, fuskansa cike da
murmushi, yace”zaki ganta har sai kin
gaji da ganinta ma. Mum tace”
Alhamdulilah! Allah ya nunan ranan da
Babana ya samu wacce yake so, sai fatan
Allah ya kaumu lokacin biki, cike da
zumu d’i ya amsa da Ameen. Dr Umar
yace” Mum baki ga yarinyan bane, gata
da hankali, kuma inkinji rayuwanta
abun tausayi, nan ya basu labarin
had’uwansu, da irin wahalan, su Mum
da ilham sun tausaya mata. Ilham tayi
karaf tace” bros to ina wacce katab’a
ban lbr ta, itama wacce Khaji a agun Dr
Abdul?. Ummm itakam har yanzu ba
labarinta. Mikewa zai haura sama,
yakali Mum yace”yau she Dad zai dawo
daga Dubai d’in?. Umma tace” umm sai
next week. Ok! Allah ya kaimu.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts