New Post

Tuesday, 18 April 2017

'YA'YA DA DUKIYA.... 111-115

YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-111~115
Aiki sosai tayi, Gwaggo tana fita
makwabta, Beeba ta fito tafara tayata
aiki, Khadi tace”Beeba da kin bari nayi,
yanzu in Gwaggo tazo ta samemu, ni
zata zaga uwa ta uba. Beeba tace”karki
damu Adda yanzu zamu gama aikin,
Rabee’a ta fito sai mika takeyi, alamar
daga bacci ta tashi, kitchen ta wuce ta
duna tukunya, taga an kusa gama abinci,
kwano ta d’auko ta d’iba. Beeba
tace”Rabee wani irin iskanci kikeyi ne,
kina kalo muna aiki amma kizo ki d’ibi
abinci?. Baki ta murgud’amusu, Khadi
tace”kyaketa Beeba, kinsan Gwaggo na
dawowa saita huce a kaina. Aiki sukayi
cikin ikon Allah dake, duna da zafin
nama basu dad’e ba suka gama. Khadi ta
raba musu abin ci suka ci, Gwaggi na
dawoa tayi mamakin yanda Khadi ta
gama aiki da wuri, d’aki tashiga kwano
ta fito da shi, ta turo ma Khadi ga
wannan masaran kina gama cin abimci
ki surfa min shi, don yau surfen hannu
nake so bana inji ba. Cikin girmamawa
tace”to Gwaggo”.
A gajiye tayi surfe ta gama ta wanke ta
shanya shi.
Yau takama jumma’a yau ne su Hajiya
jamila da Queen Neenah zasu zo, yan
kud’in da ke Hannuta ta had’a ta siyo
kaya ita da Beeba sukayi girki. Ware
dubu biyu zata basu kud’in Napep, ta
gyara ko ina sukayi wanka ita da
Beebah, sunyi kyau sosai. Gwaggo na
ganin Khadi ta fito tace”mayya inda
kinga fiskanki da bazaki na yawo cikin
mutane ba. Rabee ta mata kalon sama da
kasa, sa’a d’aya Gwaggo bata sasu aiki
ba. Sai kusan karfe biyar, su Farhat suka
kira waya, Khadi ta d’auka da
“sallamanta kun isone?.
Farhat tace”eh! Gamu a dai-dai gun fire
servise”.
“Ok gani zuwa”.
Ita da Beeba suka fita, suna zuwa
kuwata gansu, da murna suka tari juna,
farhat tace”ikon Allah yau Allah yayi
zamu gana.
“Eh wallahi sannu ku da zuwa.
Su hajiya Jamila tace”wanna itace Beeba
ko?.
Khadi ta amsa da”eh! Itace, har kin
ganeta.
Suna hira suka shigo da sallama.
Gwaggo ta musu kalon sama da kasa,
Khadi ko sai addu’a takeyi, d’akin suka
kai su. “Gwaggo ta kwala ma Khadi kira”
ta amsa da “na’am gani zuwa”.
“Kee dan uwarki ina kika samu wayan
nan?. Ko maitan ki ya dawo har gida
kike lashe mutane?.
“Kiyi hak’uri Gwaggo kawaye nane fa”.
“Eyeh har wani daman kawaye kika
samu”.
“To yau zaku ci ubanku daga ke har
kawaye”.
“Dan Allah Gwaggo kiyi hak’uri ki bari
in sun tafi kimin duk abunda kikeso”.
“Kee ko uwarki bazata ban doka nabiba,
bare kee yar karamar kwaro”.
“Assalamu’alaikum Malam yayi sallama”.
“Khadi ta amsa”
Yana daga qofar d’akinsa
yace”Khadejatu! ”
Ta amsa da “na’am Baba”.
“Maza kizo nan”
Gwaggo cikin takaici ta ja tsuka. Sam
bata so haka ba, taso saita wulakanta
Khadi Malam ya dawo.
Da sauri Khadi ta nufi gun Malam, da
sallama tashiga d’akin, tsugunawa tayi
tace”sannu da dawowa Baba”
Cikin fara’a ya amsa da”yauwa d’iyata,
naji dad’in ganin ki, a cikin wannan
yanayi”
“Ya jinin yau fatan lafiya ko?.
“Eh! Lafiya lau, ga kwayena ma sun zi
gaida mu yau”.
“Ah madalla mun gode, in zasu tafi ki
fad’amin”.
“To baba”
Da Murna tayi d’akin ta nan tayi sannu
nasu Hajiya Jamila, Beeba ko har tayi
serving d’insu.
“Tace muje ku gaida Baba na” dukansu
suka mike har qofar d’akin Malam
sukaje suka gaida shi, ya sanya musu
Albarka. Gwaggo ma tafito daga d’aki
duka k’ara gaidata. A dakile ta amsa,
suka koma d’akin Khadi, hira sosai
sikayi, kafin suka mike zasu tafi don
magriba yayi. Ta d’ibi kayan kwaliya, da
sabulai, acikin wanda Dr Umar ya kawo
mata, da turaruka tasamusu a laida. Sun
fito Malam ya kirata yace”ga wanna
kibasu su hau adai-daita. Ta karba ta
“sukuma sukayi godiya”.
Har bakin titi suka rako su ta mika musu
tare da musu alkawarin zata zo ita da
Beeba.
Bayan kwana biyu Khadi na zaman
hak’uri, kulum da kalan horon, da
Gwaggo ke mata. Ana haka kwanwar
Gwaggo da yaranta suka zo mata kwana
biyu, kulum cikin kunci da matsi take,
itaji sanyi to tana tare da Malam ko
Beeba ko Dr Umar.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
[9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts