New Post

Tuesday, 18 April 2017

'YA'YA DA DUKIYA.... 16-20

YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-16~20.
Jiki ba kwari Beeba ta nufi d’akin, don
sam ita bata son irin yadda mahaifiyarta
ke nuna tsana ma Khadi. Gash’i ko
kad’an Khadi bata nuna damuwarta
kuma hakan ba sh’i zai hanata biyayya
ba.Allah yasa Gwaggo ta gane. Ya sh’irya
mana ita Ameen.
‘Dakin su tash’iga Gwaggo ta
balbaleta da masifa, Gwaggo tace”Beeba
bana son ganin ki da wancan mai
fuskan mujiyan, kema kuma sai niman
kai kike da su. Ni har Malam da ke biye
mata ba kyalesh’i zanyi ba, ko kad’an
bana k’aunar in bud’e ido imganta a
gidan nan.
Beeba tace”haba Gwaggo ba kyau
fad’an haka fa, kuma ae Addah tana iya
k’ok’arinta gurin kyautata miki. Ita ne
kulum cikin aiki bata hutawa ko ni bana
miki aikin da take, nikam ina son Addah
na tana da halaye mai… Bakinta Gwaggo
ta make tare da wata harara tace”kee a
kul d’inki kar na kara jin cewa kina
had’a kanki da wannan yarinya, Ko
kema ta shanye miki Zuciyan ne?, kama
yanda ta shanye na Malam baya ganin
laifita baya son amata fad’a.
Beeba tace”ko d’aya Gwaggo gsky
kenan Khadi tana da halaye mai kyau.
Mts Gwaggo ta ja tsaki ga abinki can
maza ki ci don zaki gidan Innan ku, zaki
anso min aika a gunta. Beeba ta d’auko
abinci zatafita gunsu Malam Gwaggo ta
dakatar da ita, ba yanda ta iya dole yasa
taci a d’aki badan taso ba, don ta fi jin
dad’in kasancewa da yar’uwanta.
Gwaggo tace”Beeba yi sauri ki
sh’irya kije min gidan Inna ku. To ta
amsa ta kammala cin abinci tayi wanka
ta d’auko kayanta masu kyau ta sanya
su, ra fes da ita. Gwaggo “nagama sh’irin
ke nake jira kizo fad’an sakon, don inje
kar dare ta min a hanya.
Sai da Gwaggo ta d’auko sakon da
zata kai ma Inna kafin ta bata kud’in
mash’in tace”kice ta had’a miki duka
aikan harda kayan da na saya d’in, to ta
amsa ta fito sai da tayi sallama wasu
Malam kafin ta tafi.
Taku a kullum mai k’aunarku
ﺭﺍﺷﻴﺪ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts