New Post

Tuesday, 18 April 2017

'YA'YA DA DUKIYA.... 11-15

[9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-11~15.
Cikin ta kaici yazo ya tallabi Khadi ya
d’agata sai a lokacin ya kalli d’an abinci
da gwaggo ta bata.
Taburma ya d’auko a d’akinsa ya sh’in
fid’a mata, ya zaunar da ita.
Kular abincinsa ya kawo mata
tare da juye ruwa mai zafi ya had’a
mata Lipton ya bata da kyar ta iya sha.
Abicinsa ya kara mata, sai da ya
tabbatar ta kosh’i kafin ya ci sh’ima.
Khadi ta mik’e jiki ba kwari ta
nufi rijiya ta d’ebo ruwa ta nufi bayi,
wanka tayi ta fito, ta sha fa mai kayanta
masu d’an kyau ta saka ta dawo waje
gun Malam don gudun bala’in Gwaggo.
Malam yace”Mama nah bazan
fasa miki nasiha ba, inaso ko kasance
mai yawan hak’uri kinga halin Gwaggon
ku kullum Addu’a nake mata Allah yasa
ta gane gsky.
Khadiya duk halin da kika samu kanki,
ki kasance mai hak’uri zakici riban
rayuwanki. Kai ta d’aga masa alamae
Eh!.
Heeba ce ta sh’igo da Sallaman ta,
cikin fara’a ta k’araso gun su, sannu da
gida ta musu kafin tace”Addah ina ta
sauri inzo in tayaki aiki, da aka tash’i a
makaranta, ban samu abun hawa ba,
Gash’i har kin gama.
Khadi tayi murmushi tace”ba
komai k’anwata, ya makaranta?.
Alhamdulilah! Ki d’auko abinciki kici to
Adda.
Malam yana jin dad’in yanda
yaransa suka had’a kai, baran Beeba da
sam bata gado halin uwarta ba, heeba ya
rinya ce mai hankali kamar Khadi.
Sabanin Rabi da ke ji da taken rash’in
kunya, halinta sak na uwarta hatta kama
da Gwaggo take kama.
Gwaggo tafito tsawa ta daka
ma Beeba kee mai kikeyi a gunsu, kin
dawo ko sanar ni bazakiyi ba, ni bana
son kina taraya da mai fiska kaman na
muciya.
Oh! Ni Rash nace”wannan
Gwaggon wata irin macece ta fiye son
kanta, anya ma idonta na gani kuwa?.
Duk irin kyan Khadi tana zaginta.
Ko beeba ma bazata gwada mata kyau
ba don ta d’aran mata nesa ba kusa ba.
Taku a kullum mai k’aumarku .
ﺭﺍﺷﻴﺪ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺔﺩﻡ

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts