New Post

Tuesday, 18 April 2017

YAYA DA DUKIYA...81-85

YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-81~85.
Malam sun isa Asibiti, direct office d’in
Dr Abdul sukaje, Don tambayansa, ko
nan aka kawo Khadija, don shi har
yanzu, bai san a ina, Dr Umar yake aiki
ba. Duk da yasan dai, shi likita ne, suna
zuwa suka tarar da Dr Abdul a office,
cikin yanayi damuwa Malam”ya
gaidashi, ya tambayes ya aiki?.
Alhamdulilah!, Malam yace”Dr dan
Allah, ko nan asibitin, aka kawo Khadi?.
Dr Abdul ya amsa masa da eh!. Barin
rakaku d’akin da take. Sai da sukayi
tafiya mai d’an nisa kad’an, kafin suka
shiga, wani Ward mai kyau, kana shiga,
falo zakagani babba, sai gurin da likitoci
ke zama, gefe kum d’akin hutun likitoci
ne. Sai d’akuna da suke jere, gwanin
birgewa, gurin tsab da shi, kamar ba’a
cikin asibiti ba. Kowani d’aki gado
d’ayane a ciki, sai yar loka da ke gefe,
Malam suka tura, qofar d’akin da
sallamansu. Dr Umar ne zaune ya zabga
tagumin gaban Khadi, sam bai masan
sun shigoba, suka sake mai-maita
sallama, amma shiru, Dr Abdul ne ya isa
gunsa da sauri ya dafasa, yace”my
friend, cikin razana ya d’ago, sai a
lokacin yaga Malam, duk kunya ta
rufesa.
Mik’ewa yayi da sauri, yana musu,
sannu da zuwa. Kalo d’aya Malam yayi
ma Khadi, yaji wani mugun tausayinta,
ya kamasa, tambayan kamsa yayi anya
bayi da laifi, shima acikin cutar da
Khadi, da Gwaggo takeyi?. Idonsa ne ya
ciko da kwala, bakin gadon yaje, ya rike
hannuta, cikin muryan damuwa,
Yace”Khadijatu kiyafr min, duk nine
silan saki, cikin wannan damuwar.
Tabbas Hauwa watarana sai tayi
nadama, mai d’umbin yawa, Allah ya
miki Albarka, ya Allah kajikan Adamu.
Duk wanda suke gurin saida jikinsu yayi
sanyi, Beeba kam kuka takeyi sosai.
Malam ya juya ya kali, Dr Umar
yace”Umaru na rasa, da wani irin,
kalma zan gode maka. Tabbas ka taimaki
Khadijatu iya taimako, Allah ya bamu,
abunda zamu saka maka dashi.Allah ya
maku Albarka
Cikin zuciyan Dr Umar yace”abida
zaumin kad’ai kubani Khadijat, don
zuciyata, takamu da azaban sonta.
Gwaggo da ke gida, sai fatan take, “Allah
yasa adawo, da gawan Khadi. Na tsani
ganinta, kamar mayya, komai zakamata
bata zuciya. Mtsss ina da daga nan,
tashiga uwa duniya, in huta da
fitinaniyan, yarinyannan.
Ko da taji Beebah tabi Malam, sun tafi
asibiti, bakaramin haushi tajiba.
Tunanin kalan, rashin mutuncin da zan
masu.
Kwanan su Khadi, biyu a Asibiti, Dr
Umar shi ke d’awainiya da su. Kulum
yana hanyan Asibiti, yana tashi daga
aiki bayan ya duba Khadi, shagon waya
ya zarce, yasaya mata, iPhone 7, wayar
ta had’u. Gida yanufa, yana zuwa, yayi
wanka, ya fito dining, Iham ce tazo
tazauna a gefensa, tana masa surutu, can
idonta ya kyalo waya maroon, tace”bros
wannan fa?. Tare da kai hannuta ta
d’auka, “bros wayan tayi kyau, bai
kaleta ba Yace”na Khadiyat ne, ihu tasa
tare da cewa”wooow wayan tayi kyau.
Barin samata number, nan harda
WhatsApp, ta bud’e mata. Sai da yagama
tukun ya amshi wayan yafita.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts