YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-51~55.
Gwaggo tun da taga Khadi, tana d’an
samu a d’inki, hankalinta ya tashi,
Gwaggo ta kudiri aniyar sai ta b’ata
keken d’inkin. Beeba ko murna ganin
Addah ta, tasoma iya d’inki yanzu zata
bar kai d’inki, ana wulakanta ta, Gwaggo
ko kulum sai ta zagi Beeba, akan yanda
take, nuna zakewar ta ga Khadi. Haka
rayuwa tayi ta tafiya, Khadi na cikin
kunci da matsin Gwaggo, hak’uri takeyi
da ita, kulum sai taci kuka, yanda
Gwaggo ke zagin iyayenta.Yanzu har ta
kai, yan’unguwa sunsan, Khadi yar riko
ne a hannusu. In Gwaggo taga Malam
baya gida ta hana Khadi zuwa gun
d’inki, in makwabta sun kawo faci,
Gwaggo ta korasu, ta hana su shiga cikin
gidan. Khadi kusan sati bataje, gun
koyar d’inki ba. Malam baya samun
zaman gida, sabga sun masa yawa, gashi
yau tafiya ta kamasa zuwa Jigawa, tunda
asuba yatafi. Zaije ya sayar da Gona’nsa
dake garin, don fara sayyan auren
Khadi. Da wuri ta tashi tayi wanke-
wanke’nta gama, ko karyawa batayiba ta
d’au hijab da nikaf d’inta, ta fito cikin
sand’a, takalmanta a hannu ta rike dan
Gwaggi kartajita, cikin sand’ a ta fita, a
qofar gida ta sanya hijab dinta. Sauri-
sauri ta fara tafiya sai da tayi nisa ta
duba jakanta, taga naira d’ari ya rage
mata, Gwaggo duk ta amshe sauran
kud’in. Mai Napep ta tsara, ta masa
k’watancen gurin, Yace”tabada naira
d’ari, nan tafara “rok’ansa ragi, da kyar
ya yarda zai kaita a naira Saba’in. Ta
shiga suka d’au hanya, ko da taje sai da
mai koyamusu d’inki, ta mata fad’an
rashin zuwanta, hak’uri ta bata.nan suka
fara aiki har sai da karfe hudu suka
tashi, din yau sun samu K’wangilan
dinka uniform d’in wani school.
Dr Umar ne ke waya, yana sanar da
Mum d’insa zai da wo 9ja, girki na
musamman Ummin sa ta masa, ko da
jirginsu ta iso, driver ne da kanwarsa
Iham sukaje d’auko sa. A hanya suke
hira da ilham, yana tambayar ta,
yan’uwa da abokan arziki, har suka iso
gida, tun daga nesa nake hango securitys
a qofar gidan, tabbas ko ba’a fad’amin
ba, Umar d’an wani babban attajiri ne,
ko mai mulki, don masu karatu, bazan
iya tsara muku kyan gidan ba. Tundaga
gate masu aiki, ke masa sannu da
dawowa, har ya isa cikin wani falo, niko
Rash ganin irin kyan gidan nace”bazan
bari a bani labarin cikin gidan ba, da
hanzari na sanya kaina cikin falo,
yasalam masu karatu hmm wai in bakayi
bamu guri, karkuso kuga cikin falon,
sannu a hankali, nafara bin falon da
kalo, komai na golden da brown ne, ko
dana d’aga kaina wasu koyaye ne
tamkar zinari, sai haskawa sukeyi a
cikin falo. Gefe na samu na rab’e don
yanda sanyin A.C ke bugani, ga wani
sassayan kamshin da ke tashi, wata yar
datijuwa ce, ta fito d’auke da fara’a,
afuskan ta ta iso cikin falon, tana
cewa”ur welcome my son. Cikin
girmamawa yaje yayi hugging d’inta,
yana fad’i” i miss u too my lovely mum.
Kanshi ta shafa, tare da rike hannusa,
my Son “muje ka watsa ruwa sai kazo ka
ci abinci ka huta. Mikewa yayi ya nufi
side d’insa, komai a canza masa na
d’akin, wanka ya shiga, bayan ya fito ne
ya nufi falo, nan ya cika cikinsa da
abinci kala-kala, yana kammalawa
kenan ya nufo falo, wani daga cikin
security d’in yazo, yace”Oga kana tare
da bako Dr Abdul, ya kalesa cikin
girmamawa, Yace” barshi ya shigo ae ba
bako bane shi d’an gida ne. Dr Abdul ne
ya shigo, sai da ya gaida Ummin su Dr
Umar, tukuna suka nufi side d’in sa, hira
sukayi sosai kafin ya masa sallama, akan
zasu had’u, sai da ya rakosa, har jikin
motarsa yashiga sai da, Dr Abdul ya bar
gidan, kafin ya koma cikin gida.
Amin afuwa, har yanzu wuta bai tsaya
ba, shiyasa kuke jina shiru.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
[9:12PM, 9/14/201
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» 'YA'YA DA DUKIYA...... 51-55
'YA'YA DA DUKIYA...... 51-55
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment