YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-76~80.
Da sauri ya tareta, ta fad’a hannusa,
sunanta yakira, Khadijat! Khadijat
Khadijat… Pls ki tashi, kar ki tafi ki
barni lokacin dana ke bukatarki, kene
farin cikina. Pls Khadijat, yana jijigata,
amma sam ko motsi batayi, Dr Umar ya
fita a hayyacinsa, sai sam batu yakeyi,
Gwaggo ko wani ruwan sanyi, tasake
d’ebowa bata tsaya, wata-wata ba, ta
k’wara ma Dr Umar. Duk da na da lafiya
sai da ya razana, ajiyar zuciya ya sauke,
nan take ya dawo cikin hayyacinsa,
hannu sa ya kala, da sauri ya d’auketa,
cikin mota ya sanya ta. Da gudu yabar
unguwan. Asibitin Murtala ya wuce,
yana zuwa ya d’auketa a hannu,
Emergency yayi da ita. Kasancewar shi
duty safe ke dashi, Dr Abdul ke duty
kwana. Da sauri ya d’aga waya ya
kirashi, “Dr Abdul dan Allah kazo
Emergency, Khadija tace bata da lafiya,
kazo ka taimka min, muryansa kaman
zaiyi kuka, duk ya rud’a Dr Abdul, don
bai kuma taba jin, Dr Umar cikin
wannan, yanayin ba. Dr Abdul
yace”Friend wacece Khadija?.cikin fushi
yace”Malam in zakazo to in bazaka zo
nakira, DR James, kashe wayan yayi,
yafara kiran Dr Jame kenan, Dr Abdul ya
turo qofar ya shigo. Da sauri yayi kanta,
yana ganin Khadi ce, mamaki ya cikasa,
tambayoyi yafara yi makansa,” daman
Umar yasan Khadi ne?.
“To mai yasa yarinka min tambayoyi
akanta?.
“Ta ya’akayi tazama Khadijansa?.
Maganan Dr Umar ne ya dawo da shi,
daga dogon tunanin daya shiga.
Dr Umar Yace”kai Malam, lafiya kake
mata, irin wan kalon?. Da sauri yazo ya
kareta, cikin kishi da jin haushi, yake
maganan. Dr Abdul bai cemasa uffan ba,
cikin hanzari yasoma dubata, daman
yariga yasan matsalanta, cikin ikon
Allah, ansamu numfashin ta, ya dawo
dai-dai. Sai dai bata farka ba, sun mata
aluran baci, don ta samu hutu.
Special room aka kaita, don hutawa ita
kad’aine a d’akin. Dr Umar ya zauna, a
bakin gadon ya zuba mata ido, ko
kyaftawa ba yayi. Ji yake kaman ya
k’arba mata ciwon, Dr Abdul ne ya
shigo, yace”Ya mai jiki?. Da sauki ya
bashi amsa. “Allah ya k’ara sauki. “In ka
gama kasameni a office d’ina. Ok! Dr
Abdul ya fita, office d’insa ya koma, ya
zauna cike da tambayoyi, a fuskansa. Dr
Umar sai daya kai, kusan kamar 1hrs,
kafin ya kira nurse, yace”ta kulamasa,
da patient d’insa.
Da sallama ya shiga office d’in Dr Abdul,
bayan ya zauna ne, Dr Abdul
Yace”friend ina kasamu Khadi?. Ko
dama ka santa tun-tuni, Dr Umar yace”
kai ka santa ne?. Dr Abdul ya d’aga masa
kai alamar eh!. Ajiyan zuciya Dr Umar
yayi, nan ya kwashe labari, tunga randa
ya fara ganinta, har yanzu, dayake fama
da azaban sonta. Sai da Dr Abdul ya
jijina kai, yace”Allah mai iko, to ae itace
Khadijan, da ranan kaji ana case akanta.
Cikin mamaki Dr Umar yace” mai kace
ne ban fahimta ba. Nan Dr Abdul
yabashi labarinta, iya yanda ya sani.
Umar ya tausaya mata ba kad’an ba,
wani Sonta da Qaunarta, suka k’ara
shigansa. Cikin tsokana Dr Abdul yace”
friend amma gaskiya, ka cika kishi,
kawai don ina mata kalon sani, amma
kawani tare, dariya Dr Umar yamasa,
tare da kai masa dukan wasa.
Malam dawowansa, daga kasuwa kenan,
aka basa labarin, abunda ya faru bai iya
shiga gidan ba, ya juya zai tafi kenan,
yaga Beeba ta fito, duk ta rud’e hijab ma
bai-bai tasa. Da sauri ta bisa, Napep ya
tsara musu, suka nufi Asibitin Murtala.
Zuciyan Malam sai tafasa yakeyi, yana
tunanin wani kalan hukunci, zai yanke
ma Gwaggo. Don abuntan yayi yawa,”to
wai mai Khadi ta tsare mata a
rayuwanta ne?. Da takeson ganin
bayanta, tabbas zai Aura da Khadi, don
ta huta da bala’in Gwaggo.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
[9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» YAYA DA DUKIYA... 76-80
YAYA DA DUKIYA... 76-80
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment