New Post

Tuesday, 18 April 2017

'YA'YA DA DUKIYA.... 121-125

’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-121~125.
Gwaggo ta buga k’irji tace”nashiga uku,
anya kuwa ba Khadi mu bane.
Matar tace”nan gidan mana”. Innna
Yalwa tace”sannuku da zuwa ga gurin
zama”. Cike da fara’a suka k’ara
shigowa. Nan fa aka shigo da akwatuna,
ko da aka shin fud’a taburma, hmm
akwatuna bazai yiwu a bazasu, a tsakar
gidan ba. Inna Yalwa tace”yan’uwa yana
da kyau, kafin mu fara bud’e kaya, muyi
addu’a Allah ya sanya alkairi, ya kad’e
fitin-tinun dake ciki, ya kuma kawar da
idon mahassada da makiya, dazasu kawo
farmaki ma auren nan. Gwaggo tace”kee
Yalwa wa zaiyi hassda ko makiyi nasan
dani kikeyi, nan Gwaggo ta fara kwala,
ko ta kanta basu bi ba, sukayi addu’a
aka fara bud’e kaya. Yasalam masu
karatu karkuso kuga kayan yawanci
ready made ne, ga tsada, ko da ka zo kan
takalma duk gulma na, na kasa k’irga
yawansu, jakukuna da poss ba’a magana.
Ko da aka bud’e na d’ankunaye hmm
gwala-gwalai da fashion masu tsada, ga
manyan balguls ba a cewa komai, can
idona ya kyalo wani karamar a kwati
acikin kayan, da sauri Inna yalwa ta
d’auko, tayi-tayi ta bud’e amma ta kasa,
wannan matar ne tace”kawo ki gani,
tana tab’a qofar akwatin yafara k’ara
sauti mai dad’i gashi da k’arfi. Tana
bud’ewa yace Hello My Master, cikin
wata tausasashiyar murya na mata, kai
ka d’auka a fili mutum yayi wannan
maganan ba.
Wata mata da ke gefe, tace” a kula da
wannan a kwatin, don White Gold ne a
ciki, yana da matukar tsada sosai,
kud’insa ya kai miliyan uku a kud’in
9ja. Inna Yalwa baki har kuni godia suka
fara musu, sai suka d’auko d’an kayan
da suka had’a musu suka mik’a. Inna
Yalwa da dubu biyar a jikinta, ta k’ara
musu yadawo 15k. San suki karb’a sai da
su Inna Yalwa sukace”ko kun rainane?.
Da fara’a sukace”a’a Allah ya sanya
alkairi, wane mu da raina kyautan da
zata fito, daga gidan surkan Gwamna,
matar d’ansa d’aya tilo. Inna Yalwa
cikin rashin fahimta tace” umm Hajiya
bam gane kince Surkar Gwamna ba?.
Matar tace” eh ko bakusan cewa Umar
shine d’an Gwamna d’a d’aya tilo na
miji.
Inna Yalwa tace”sam bamu sani ba ya
ma b’oye mana ko shi waye”.
Take matar ta war-ware musu, aikafin ta
rufe baki. Gwaggo tasaka ihu ta hau
tsakiyar kayan tana watsi da su, tana
cewa” wanna fa k’arya ne d’an yankan
kai ne, Hajiya Suwaiba k’anwar Adam
Naira cike da mamaki, tace”lalle tabbas
yau naga halinki da’ake fad’a.
“Bari kiji ga kayan Lhadijat nan abu
d’aya ya bata sai mun miki rashin
mutunci, kisani duk wanda zakana masa
hassada da bak’in ciki, Allah kan masa
sakayya, mugunta da kike mata ne Allah
ta bata. Gwaggo tayi kanta zata
cakumeta wani security ya kaimata
naushi ta fad’i a kasa. Hajiya Siwaiba
tace”ae da ka barta da yau na koya mata
hankali, ni ba irin matan da suke
d’aukan wargi bane.
“Mtsss bamza sakarya marar imani.
“Khadijat takusa hutawa da muguntanki.
Gwaggo na ihu kamar mahaukaciya,
tana cewa”sai kun kawo na Beeba da
Rabee’ in ba haka ba zamana lafiya.
Gwaggo hauka tuburan Inna Yalwa ta
kali K’anwar Gwaggo tace”da fa kin
kama yar’uwanki kartayi tsirara, tsabam
bak’in ciki. Da kyar aka shigar da
Gwaggo d’aki aka kule ta.
Malam da yadawo, ko da yaji labari,
Hamdalah yayi, ya k’ara gode ma Allah,
tabbas Khadijat ta samu miji, don yana
jin labarin halin d’an Gwamna. Kayan
yasa ka aka d’eba a gidan aka kai gidan
Inna Yalwa da daddare, ba wanda
yasani, motar kuwa ya kai gun wasu
masu ajiye mota aka ajiye masa.
Yan’unguwa ko ina ka leka sai zance
akeyi, wasu ko so suke su ga Khadi matar
d’an Gwamna.
Gwaggo tana d’aki sai zage-zage take,
Beeba ko murna ba’a magana.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
[9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts