New Post

Saturday, 1 April 2017

AMANA TA CE 29

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
  
29                            
Kausar tana shiga dakinta ta ganshi a gyare ko ina murmushi tayi Allah sarki baiwar Allah gsky auta tana da halin kwarai ko jikinta barin dubota yanzu haka halan ko abinci bata ciba dakin auta ta leka ta ganta jingine da gado ta lumshe idonta da alamar kamar bacci take amma ba baccin take ba fridge taje ta dauko mata kunun aya ta nufi kitchen ta dauko mata abinci da plate ta dawo dakin a hankali ta ke tada ta Zee ta bude idonta taga Kausar ce murmushi tayi tace Aunty Kausar kun dawo lfy ya hanya kausar tace wato ko ki fito ku gaisa da bros ko auta tace zanje in gaida shi
Kausar tace to tashi kici abinci na san yanzu haka ba abinda kika ci ba musu auta ta mike taci abinci sukayita hira harsai la’asar kausar ta nufi dakinta don ganatar da sallah la’asar auta ma sallah tayi bayan sun idar ne suka shiga kitchen sukayi abincin dare bayan sun fito ne auta ta koma daki don yanzu ta hana kanta zaman falo bata son hayaniya sam.
Ammar business ya zauna ga shago sai kara habaka yakeyi abun sai son barka burinshi kulum autarsa ya ganta cikin farin ciki san nan komai ya samu ita yake sayama wa haka account dinsa ma da sunanta ya bude duk kudin da ake basa nasa yana sawa a gun kamar kulum da ya saba zuwa sari kano yaje yayi sari nan ya ga wasu dogayen riguna masu kyau haka ya saya musu su uku Zee Auta maroon da ratsin golden colour na kausar baki na munay ash da ratsin baki sosai yayi sayya yana ta sauri ya dawo don ya gana da dan hajiya mamu wato Ahyan don shima ya nuna nasa farin cikin dawowarsa.
     * * * * *
Kaduna kuwa haka rayuwan futha da sadiya ya kasance yanzu futha ta gama diploma har tasamu Admission a degree tana gamawa zata tafi school of law haka tacigaba da gu danar da yan bincikenta don ta dau ma kanta alkawari sai ta gano wanda ya kashe ma auta iyayenta.
Sadiya ma haka abun yake karatunta take cikin kwanciyan hankali amma sai dai kulum tunaninta autar ta awani haki take ga iyayenta ku su nuna damuwarsu a kan magana gashi dukiyar sai habaka take abinda ya daure mata kai yanda taga wasu mutane tu da alamar ko bacun ransu baba isiya da Abbanta basa son gani gashi kuma mai gadin gidansu Auta da sun dawo sun dinke da iyayenta kuma wani abun daure kai yanda pinky kewasa da naira ba mai kulata sai kara daure mata gindi akeyi in yau ka ganta awan nan motar gobe da wancan kawaye kuwa sai yayan manya take harka da su abun sai hmmm don yanzu ji take da kanta tana kallon Big Girl ce ita ga naira ga hutu.
Ammar ya dawo yayi murna da ganin Ahyan sosai ya kawo tsara ba masu auta da kausar san nan yanzu an yanke shawarar zai fara fita waje nan yayi murna da godia san nan ya ce ma auta ya kamata suje kauye su gaida su Inna larai da Malam don su musu karamci da bazasu taba mantawa ba, hajiya mamu ya samu ya mata bayani tayi murna san nan ta basu goma na arziki sukai musu nan kausar tace zata bisu tunda gobe zasu dawo munay sai wani yatsina take ita ala dole tana kyamar yan kauye,
Tunda Ahyan ya dawi ko da wasa basu taba haduwa da auta ba yau kwanansa 4 ya ba masu kausar hakuri akan kayansa ran Thursday sai iso sukace ba matsala,
Ammar wanka yayi sosai haka ma auta sunyi kyau kausar ta dau Camera don tana son zuwa kauye ran asabar da safe suka dauko hanyan suwa kauyensu Malam suna masu farin ciki.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts