AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
17
Mota su ka shiga, a hankali suke tafiya, haka kurum ya tsinci kansa da farin ciki, tun a hanya yaji yana son garin ya burge shi.
Auta ma haka abun yake tana gefen Ammar ta dan jingina kanta a kafadarsa, haka kurum take jin sanyi a zuciyar ta, nan ta fara tuna irin rayuwan da sukayi abaya lokacin iyayenta suna raye, ku ina zataje a mota suke tafiya mota mai AC ba hayaniya, amma yau gata a motar kasuwa, Allah sarki yarinyan da taso cikin gata da kulawa ya daya tilo yau gata a cikin gararin rayuwa Allah ya kawo masu sauki Ameen.
Karfe goma da minti sha uku, suka iso cikin garin bauchi, driver ya sauke su a waje tashar mota na winti market, nan suka sauka, kowa ya kama gabansa, Ammar ya riko hannun Auta suka bar gurin, titi suka tsallaka suka zo ta gefen stadium akwai dan guri nan suka zauna, kallo daya zakayi ka ga kamanin su auta yanda ya canza sunyi baki ga rama da sukayi sosai.
Sun dade a gurin sosai, amma sun rasa inda zasuyi can yace bari yaje ya nimo musu abinci, tace to gefen gun masu sai da jarida da gyaran mashin ya ga mai sai da shinkafa da wake nan ya saya musu roba biyu da pure water kwaya 2 ya kawo musu, haka suka ci sukayi godiya ga Allah ya mayar wa masu shinkafa ya karbi canji ya dawo, haka suka zauna sai da aka kira sallah, nan ya sake saya mata ruwa tayi alwala shi kuma ya tafi masallacin da ke gefe yayi sallah, bayan ya dawo suka zauna hira ya rinka mata yana bata dariya don ya debe mata kewa sabida yaga damuwa a idonta sosai, haka suka yini har dare agun suka kwanta.
Da gari ya waye sallah yayi yace ta zauna a gun kartaje ko ina zaije ne man abunyi ko da dako yasamu don su rinka samun abunda za suci da in da zasu zauna, haka ko akayi ya shiga cikin kasuwar winti, haka yayi yawo sosai amam shiru ba lbr aiki sai azahar ya dawo yaje ya sayo musu shinkafa sukaci, bayan sunci tace Yaya na anyi nasara kuwa cikin mutuwar jiki yace ina Allah baisa an dace ba, idonta yaciko da kwalla tana shirin yin kuka ya girgiza mata kai alamar aa, yace ko kin manta Allah yana tare da mu bazai barmu haka ba, kuma duk bakin da Allah ya tsaga bazai hana shi abinci da zaici ba.
haka suka sake kai dare nan suka sake kwana.
Washe gari ma haka yafita yayi yawo har ya gaji gashi yan kudinsa sun soma karewa saura dari biyar, yau sai bayan la’asar ya dawo dake ya ba ma Auta naira dari don tasayi abunda zataci ko da yadawo yasamu tana bacci akan yar fallen zanin da ta shimfida tausayinta ya kama shi, Allah sarki auta yau itace tamkar wata tsintaciyar mage gwamma shima namiji ne, idonsa ne ya ciko da kwalla a zuciyarsa yake adu’ah Allah ya kawo musu dauki baisan hawaye yana sauka da ga idonsa ba saiji yayi auta na share masa hawaye itama idonta yaciko da kwalla, tace Yaya na sai dayaji sanyi har cikin ransa, mai yasa ka kuka ban son ganin hawayen ka, in kai kayi hawaye wazai rarrashe ni, kaine mai sani farin ciki, Allah gatana kaine gata na, yaya na waya taba ka karkasa kanka cikin damuwa Allah zai kawo mana mafita yana tare damu kaji, kaman karamin yaro ya daga mata kai, tace kayi min murmushi, ammar baisan lokacin daya murmusa ba, itama murmushin tayi ta rike hannunsa tace Ya Allah kaja kwanan yaya na kabani abunda zan saka masa dashi.
Saturday, 1 April 2017
Home »
» AMANA TA CE 17
AMANA TA CE 17
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment