New Post

Saturday, 1 April 2017

AMANA TA CE 34

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
  
34                            
Da sauri ya shiga gidan, yayi hanyar stairs a hankali ya ke tafiyar, sai da ya taba kofar dakinta yaji a bude, kafin ya nufi nasa ruwa ya watsa, ya sanya kanan kaya maras nauyi, ya nufi fita daga dakinsa kenan, wayar sa tayi kuka, badan ya soba ya juyo ya dauki wayar, sunan Jenifa ya gani a scream din wayar, da sauri ya daga daga daya bangaren akace hello my luv, ya kk? Ya 9ja? yau she zaka dawo ne?nayi missing dinka da yawa, nan ta fara masa salonta na janye hankali, “take ya manta da abunda yayi niyya” suka shiga hirarsu ta masoya, bai ankara ba, sai jin ana kiran sallah mangariba, sai lokacin ya tuna kudirinsa, da sairi ya ce mike yana fadin oh!!! Shirt, ya tsa ya ciza, kafin ya kashe wayar, ko sallama baiyi ma jenifa ba,
Yana fitowa daga dakinsa ya ga munay tana haurowa, sam baiso ta dawo, batare da ya cimma burinsa ba, sannu da gida ta masa, ta wuce dakinta, haka ya hakura yakoma daki, yana jin haushi kansa da ya biye ma jinifa, (ni kuma Rash nace bawan Allah ko ka manta duk wanda ya rike Adu’ah Allah, ba zai kyale mun gu ya cuce saba, sai bisa jarabta ko kaddara).
Ammar ko duk hankalinsa bai kwanta masa, da ahyan sam, ana sallah magriba ya dawo gida, sai da yazo ya samu auta tana sallah, bayan ta idar ya tabayi lfy ta, ya ajiye mata abunda ya sayo, kafin ya koma dakinsa, auta da wuri ta rufe kofar ta, sanin halin munay, kartazo ta cimata mutunci, aiko munay tana zuwa ta kwan2sa kofar dakin taji akule ba haka taso ba.
ba yanda ta iya taje ta kwanta.
gari na wayewa, bayan auta tayi sallah, ta yi karatunta sannan ta mike taje ta hada tea ta dawo tana breakfast, sai ga munay tazo, fuskan nan ko alamar murmushi babu, nan take gaban auta ya fadi, kanta ta sunkuyar kasa, tana zuwa, ta zauna a yar kujeran da ke daki, ta daura daya kan daya, tana kada kafa.
Kee waya baki damar da har zakina kulle daki?, ko kin manta da doka na ne?, auta ta kada kai alamar àa, to maza ki bar cin abincin nan, kije ki hadan breakfast, cikin sanyi jiki, tace mai zan hada miki?, wani mugun kallon da tamata yasa ta yi shiru, idonta duk ya kawo kwalla, munay na fita ta nufi kitchen, haka soya mata Chief da indomee sai tea da yaji kayan kamshi, ta kawo mata daki, ta ajiye zata fita munay tace inagama ki dawo kizo kittara kwanukan kai ta kada mata, ta fita da sauri, sabida kukan da ke shirin zuwa mata.
“Allah sarki rayuwa nikuma haka Allah ya tsara min, Ya Allah ka bani ikon hakuri”, kuka tayi sosai kafin ta share hawayenta, ta nufi dakin munay ta debi kwanukan kenan, munay tace dan ajima kimin girki da dan yawa, don ina ‘suspect” din a kwai bakin da zanyi in sunzo, san nan ki tabbatar yayi dadi, in ba hakaba, kin san saura ta fita, adakin ta je ta jiye, falo ta gyara, bayan ta gama ta nufi dakin ammar ta gaidashi, ciki2 ya amsa nan ta bashi hakurin abunda ya faru, sam ba zai iya fushi da autarsa ba, dole ya huce suka danyi hira, kafin ta dawo cikin gd.
Ahyan kuwa tun daren jiya, ya gama kwanton baunan sa, Allah bai bashi sa’a ba yayi ta zarya amma ta rufe daki, dole ya hakura ya kwanta cike da haushi.
auta da wuri ta daura girki, ko ina a gd sai kamshi ke tashi, bata gama girkin rana ba sai 3:40 tashiga tayi wanka, ta dauko kayan da Ammar ya musu tsaraba tasa, gata fara ga kayan maroon da baki, bakaramin kyau ya mata ba, “(ko kai mai karatu katsara irin wan nan kaya a idonk ya kake ganin auta zata fito)”.
Munay manya bacci tasha, sai da ta tashi wanka tashiga, tana fitowa ta bude sif dinta tana zaban kaya can idonta ya kai kan wani green sai lokacin ta tuna Ammar ne ya sayo musu a dubai da yaje sari, da sauri ta dauko, nasan yau un yaganni da shi zaiyi farin ciki, tana sawa tayi make up kamar  zata bar kasan.
Misalin4:30 wayarta tayi kara, tana dagawa taga bsty ta ce, da sauri tace ya kun isone?, bsty tace eh, right!,….
gani zuwa da sauri ta nufi gate, tana zuwa ta hango su, oyoyo ta musu, kafin suka rankwafo zuwa falo.
bayan sun zauna ne munay tace kee auta!!, auta!! auta!! cikin isa da gadara take kiran, Ganin bata fito ba yasa tayi hanyan stairs, fuskanta dauke da kwandon bala’i.
  auta ko jin kira bana karau ba, yasa tafito da sauri sam bata lura ba saiji tayi garam!!….. Sunyi karo da mutum cikin tsoro ta ja da baya kee yar iska dan ubakin waya baki damar tafiya kwa2ra agidan nan?, ta sadakar da duka kwai, duk tsoro ya cikata amma jin ta zagi ubanta yasa taji wani bacin rai da karfin guwa yazomata.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts