AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
15
Wani kara tasaki, sai a lokacin suka kula da ita, take suka haskata da toci sai sukaga macece, wani daga cikinsu yace mai ya kawo wan nan guri, sai da yace tsaya in ga barawo nan tukun don wancan gajeren wando ne ajikinsa, yana haskawa ko ah… ah.. wan nan ba barawon bane to ina yayi, sai dayan yace wan can na da kirar gutun mutum, auta ko sai ihu take, ammar ko motsi ba yayi sanadin dukan da aka masa harda bora, wasu ice haka akayita kwana masa.
A kaduna kuwa sadiya Al’amari abban ta ya daure mata kai don yasaka dukiyar auta gaba sai ci sukeyi, a ko a jikinsu, wata ran kam ma intasoma masa zancen auta ya hauta da fada kenan, haka yasa ta soma zargin wani abu a tare da su,
Wani yammacin asabar sun fito gidansu futha suna tattaunawa akan batun auta da yanda zasu bi al’amarin kenan sai suka hango abban sady, tun daga nesa yasoma wurga mata wani kallon tuhuma, ganin haka yasa tayi sallama ma futha tashiga gd, aiko kamar jira yake yazo ya fara zazzaga mata bala’i akan tafita harkan futha ko ya saba mata, shi baya son kawancen su, ganin su tare ma baya so, sady tace kayi hakuri abba ina tarayya da ita ba dan komai ba sai tun auta ta nan muna tare mun kuma shaku, abban sady yace hungo nan uwaki da autan nace uwaki da auta kar ki kara kira min sunan wayan nan banza mutanen,
nan take idon sady ya kawo hawaye ita kam bazata manta auta ba aminiyarta jininta, anya baba na da imani kuwa ko tausayinsu babu a zuciyarshi ko ya manta dukiyar iyayenta yake wada kansa shi, ya Allah kasanya mana tausayi da imani a zukatan mu Ameen ranan tayi kuka haka ta yini sukuku, sai yamma tayi shirin issalamiyya ta tafi ko da taje nan ta saida wa malaman su akan sutayata adu’ah ta kuma musu bayani ko mai ake ciki, tun daga ranan ya zamana kulum a makaranta bayan an gama karatu sai anyi ma auta da iyayenta adu’ah.
Futha kuwa kwana 2 taji sady shiru nan tashirya ta shiga gdnsu aiko nan sukayi karo da abban sady, tun daga nesa yasoma hararanta, tana isowa kusa yace kee wajen wa kika zo cikin ladabi tace baba kawar Auta ce nazo gun sadiya ne, yace maza ki juya kar na kara ganin lafarki a gdn nan yata batayi kawance da ke ba don ban yarda da kee ba.
ran futha in yayi dubu ya baci haka ta juya gd jiki ba kwari kuma tana tunani akan al’amarin nan,
anya ba hannu baban sady a kisan su abban auta, to tabbas ko ma miye sai na binciko ko da hakan yana nufin rasa raina ne ya Allah ka bayya na gsky.
Muta ne da ke gun duk suka soma watsewa ganin baya motsi gashi sun dakesa ba akan wani laifi ba, gudun shiga Case, auta ko in banda kuka da ihu ba abinda take sai kiran sunan Allah ga idonta har ya kubura yayi ja ga ammar shi da matatce marabansu kadan ne, wayyo Allah na ka taimaka min ka min agaji in ammar ya tafi bani da wanda zan kalla inji dadi, rayuwata zata zama abar tausayi Allah kaine gata na ka tai make ni ammar dina ya tashi, cikin kuka take jijiga Ammar ga hawaye ga majina duk sauka sukeyi, Ammar dan Allah ka tashi kar ka barni ka manta Dad ya baka “AMANA TA” ka tashi ka kula da “YAR AMANA” ka kuka take sosai mai ban tausayi tana ta surutai amma shiri ganin haka yasa takara fasa wani kuka mai ban tausayi wanda ni kaina Rasheedah ban san lokacin da na fara zubar da hawaye ba, gsky Auta da Ammar kun ga jarabawar rayuwa ga wlh Allah sarki auta abun tausayi, Allah yasa ammar dinki ya tashi Ameen.
Jumma’at Mubarak 2 all my muslim sisters n brothers.
Saturday, 1 April 2017
Home »
» AMANA TA CE 15
AMANA TA CE 15
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment