AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
27
Washe gari Kausar ta dauko wasu katanta masu kyau ta ba ma auta san nan tace tayi wanka zasu shiga kasuwa hajiya ta bada kudi ayi mata sayya godiya tayi sosai daki tashiga tayi wanka wani dogon riga tasaka dark blue da gyalansa tayi rolling bakaramin kyau tayi ba nan ta fito dai2 lokacin munay tashigo hajiya da kausar suna ganinta suka fara tafawa kausar tace Zee kinyi kyau baka danba hajiya mamu tace Masha’allah gsky kinyi kyau yata wani bakin ciki ne ya daki zuciyar munay don ta tsani ace ga wanda ya fita kyau ita gani take tafi kowa kyau nan ta gode musu ta karaso suka shiga motar kausar suka nufi kasuwa sunyi sayya sosai kafin suka dawo gd suna shi gowa ta hango ammar a gate suna zaune da mai gadi nan tayi gunsa da fara a suka gaisa kausar ta karaso suka gaisa, ammar yaji dadi ganin auta cikin farin ciki sosai nan yayi godia ma kausar sosai don yaga tana da nutsuwa ba kamar Munay da rawan kai ya mata yawa ba nuna isa haka suka nufi gd bayan sun huta auta ta nufi kitchen ta taya hauwa aiki bayan sun gama ta je dakin Munay ta gyara san nan suka ci abinci rana.
* * * * * *
Hajiya Mamu ta bama ammar driver gd tana so sai taga yanayisa kafin ta daura sa akan dukiyarsa kafin Ahyan ya dawo daga turai tun da yakusa zuwa ganin gd kafin ya koma duk yanda sukayi to.
Haka rayuwa tayi ta tafiya auta na cikin kunci amma ta boye sai dai tayi fari sosai ga hutu amma fa ta rame sabida damuwa haka take bautawa munay ko tausayinta bata ji baran itaga ba mum da kausar a gd tana mata ba dadi kam.
Haka rayuwa yayita tafiya yau sun dauki shekara 2 a gidan yanzu hajiya tasa ammar akan karamin shagon kayan ta wanda yake cikin garin bauchi mall ne babba duk abun da mutum kenema zai samu hakan yasa ammar baya zaman gd sai shago yanzu hajiya tana jiran Ahyan in yazo zasu yi magan daga na Ammar sai ya fara harkokin kasar wajen kawai tunda taga yana da AMANA.
* * * * *
Yau gd an tashi da shiri don gobe bros dinsu Ahyan zai dawo daga turai kausar ne taja auta sukaje kasu nan suka suyo kayan vegetables nan kausar ta umurci auta da gobe zasu shiga kitchen tunda taga auta gwanar girki ce kuma ta iya sosai Munay wani haushin auta take ji don bataso ta kusanci Ahyan don tasan zai yi wuya yaga auta bai kyasa ba tunda tana da kyau dai2 gwargwado.
Washe gari duk inda kaleka agidan kamshi yakeyi Kausar da auta ne a kitchen sai sarrafa girki sukeyi abun sai wanda ya jiyo don ina daga nan yawuna har ya tsinke bayan sun gama suka jera komai a inda ya dace nan kausar tace auta ta shirya da ita za aje dauko Ahyan wanka tayi sosai kafi tayi kwalliya Munay ko tace duk yanda zatayi sai ta hanata zuwa don bazasu tafi da wan nan mai kodaden fuskan ba, sai da munay ta shirya kafin tazo dakinta ta shigo ko sallma babu ta kali Zee Auta tabbas kam tayi kyau amma sai tace ko tsari bakiyi ba ina zakije da kodaden fuskan ta ki mai kama da na biri wlh na kuskura na ga kin saka kafa kin bimu sai
Kinyi na dama da mata harara sama da kasa tace sannan kuma kisani daga yau bake ba kwaliya bake ba zaman falo kinji ko auta da idonta ya kawo hawaye ta daga kai da alamar eh kafin munay ta gita a dakin falo ta fito tasamu kausar ta fito nan tace ina Zee take Munay tace ai bazata ba ko mai yasa oho kema kya gayyaci wannan kofadiyar kausar kalon tambaya ta mata duk da haka bata daddara ta haura sama tasamu auta ta kifa kanta tana kuka kausar da sauri ta hau kan gado lfy zee auta tace kaina ke ciwo bazan samu zuwa ba ba yanda kausar ta iya dole ta hakura ta sauko ta ja mata kofar suka nufi AVUBAKAR TAFAWA/BALEWA AIRPORT BAUCHI, kausar ke jan motar suka nufi airport suna isa suka samu jirgin tasauka har fasinja sun soma saukowa tun da suka iso na zuba ma kofar sauka inga masu fita tun daga nesa na hango wani guy shidai ba fari bane amma ba laifi ya hadu sosai yana da tsayi da fadin kirji fuskansa dauke da murmushi hannu sa rike da wata jaka yana sanye da jar riga da yar bakar falmara yana sanye da bakar wando jeans da takalminsa baka da ratsin ja abun sai wanda ya ganin tun daga nesa na hango kausar fara ary ya karu da sauri ta mike tanufi wan nan guy din mai kice da kyau don kalo daya zaka masa kaga hutu da wayewa sun masa yawa ga boko kunnesa makale da yar manne kana gani kasan yana taba rayuwa sosai amma fa ya hadu ba laifi.
Saturday, 1 April 2017
Home »
» AMANA TA CE 27
AMANA TA CE 27
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment