YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-71~75.
Khadi kulum tana cikin k’unci, Gwaggo
ta sata a gaba, baran in taga, Malam ya
fita kasuwa. Gashi Dr Umar ya kwana
biyu bai zoba, d’inki ma, tabar zuwa
sabida bala’in Gwaggo, wai sai Malam ya
saka su duka, don su Beeba su samu
suma mai saya musu kaya. Malam ko
yace”bata isa ba, tayi k’ad’an ta gindaya
mishi sharad’i yabi. Tunda tun farko,
Khadi ne tafara cewa tana so, dan haka
ba zaisasu ba. Zaban tayar musu da
hankali yasa Khadi ta samu Malam tace”
Baba bana jin dad’i zan d’an huta da
zuwa aiki, kafin wata sati, Tukun ya
hak’ura.
Dr Umar ko, bai da tunani da yawuce na
Khadijat, so ya kemata, wanda shi
kanshi, bazai iya auna shi, a mizani ba.
Masu karatu zamu so musan,
WAYE DR UMAR?
Umar Adam Naira, shine cikaken
sunansa, d’a, d’aya tilo girin Adam
Naira. Adam naira haifafen d’an Kano
ne, nan yayi karatunsa, har ya girma, ya
Auri maransa Maryama, sun dade da
aure, Allah bai basu haihuwa ba, sai
daga baya Allah ya azurta su da
haihuwan Umar, wanda yaci sunan
Baban Mum d’insa, bayan shekaru da
yawa, ta haifi Ilham, wacce itace auta, a
yamzu haka. Alhaji Adam Naira yarike
muk’amai, na gwamnati da dama.
Wanda yanzu haka shine gwamnan
Kano State mai ci. Ya kasance mutum ne
mai kwatanta gaskiya da adalci, hakan
yasa al’uman garin Kano ta Dabo suke
sonsa. Tunda Umar ya taso, shi bamai
son yawan, hayaniya bane, sannan bai
kula yan’mata,sai wata yarinya, Sakina
da ta makalemasa, sam bata cikin
tsarinsa, don bata da kamun kai,
yar’gidan, matai makin governor ne,
gata da rashin kunya, shiyasa basa shiri.
Yanzuma saukin da yasamu, ya dawo
yasamu sun fita waje, ita da Mum d’inta.
Iyayensa burinsu shine, yayi aure amma
baya kula yan’mata. Tun randa ya had’u
da Khadi, tunda yasanar da Mum d’insa,
da murna ta, tasanar da His Excellency.
Yayi farinciki ba kad’an ba. Yace” yana
dawowa zasu samu iyayen yarinyan, ayi
magana a sanya rana.wanna shine
labarin Umar a takaice.
Dr Umar zaune yau, sai tunanin
Khadijat, da ya damesa.
Key mutarsa ya d’auka, yana fitowa
securitys, suka fara gaidasa, da gudu
suka bud’e masa, k’ofar motan yashiga,
gida ya nufa yayi wanka, dun zuwa gun
Khadi. Yayi kyau sosai, ya shiga mota shi
kad’ai batare da security’s ba, ya nufi
gidan.
Khadi ko tunda ta tashi, tashi tana son
yin wanka, kayan da Dr Umar ya kawo
mata. ta d’auko wani less, mai kyau
purple da duwatsu farare a jiki. Tayi
kwaliya sosai, ta kuma yi kyau.
Kasancewan yanayi gari, da sanyi, gun
sai yayi, bada yanayi mai kayatarwa.
Gwaggo ta shiga makwabta, sai zuba
take musu. Yaro ne yashigo”wai ana
salama, da Khadijat inji Umar.
Tace”kace ina zuwa. Yana fita ta d’auko
hijab d’inta fari tasa, bakaramin kyau
tayi ba. Cikin nutsuwa ta fito, tunda
Umar ya hangota, zuciyar sa sai
harbawa, ido ya k’ura mata.
Gwaggo da tafito daga, gidan su abula,
ganin Umar acikin k’atuwar mota, nan
zuciyarta ya fara tafarfasa. Yau mai
zanyi ma Khadi na huce?. Wata zuciya
tace”kawai ki d’auko wuka ki burma
mata. Mtss a’a za’a kamani, can shaidan
ya tuna mata, kawai ki shek’a mata
ruwan sanyi, tunda bata so. Da sauri ta
koma gidan Abula, tace”dan Allah samin
ruwan a fridge d’inki. Sam Abula bata
kawo komai ba, ta iba mata, a karami
roban plastic. Da sauri tayi gida, ta k’ara
dana randa, kamar wata mahauk’aciya
ta fito.
Dr Umar ya shagala, da kalon Khadi,
itako tana wasa, da yan’yatsun hannuta.
Sai jin shaaa… sukayi, take idon Khadi
ya kafe, numfashinta ya d’auke, ta tafi
luuuuu zata fad’i kasa. Da sauri Dr Umar
ya fito, yana kiran sunanta, tareta yayi
ta fad’i a hannusa yana jijigata, amma
sam bata ko motsi.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺗﻠﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» 'YA'YA DA DUKIYA.... 71-75
'YA'YA DA DUKIYA.... 71-75
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment